NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 323

ya taɓu. Muryarta so cool tace,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu". Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin dake hannunta ta ajiyewa Kaka. "gashi ai adu'a wa iyayenmu". Kaka dake ta zabga godiya ta koma jero adu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abinda zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine kaiwa iyayenta adu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan. Har ta fita bata lura da Fillo dake gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka me kauri saboda sanyin da ta ke ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi gaisheta kuma har haɗa ido sunyi, kuma tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shi yasa itama Kaka ɗin taita adu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna tura da ita balle ta bata kunya. Kaka da ta dawo daga rakiya tace da Fillo. "ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne". Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar. "Amir ne ya kira yace na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe". Kaka tace,"ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta". Fillo ta kalli wayar dake kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance tace,"kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta". Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin ɗaukewa tana faɗin,"yanda Yami ke ji da wayar nan kika fasa aini za ki jawa faɗa". *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *7* Acikin ɗan ƙaramin falon nasu, Fillo ce zaune ta takure daga jikin bango, jikinta gaba ɗaya a nannaɗe da babban mayafin da suke rufa da shi saboda sanyin da ta ke ji, kallo ɗaya za kai mata ta baka mugu mugun tausayi saboda yanda ta rame duk da cewar ita ɗin dama asali ba mai ƙiba ba bace, amma kana kallon ramarta a yanzu zaka san ta lalura ce. Fillo cikin tuƙewar wani kukan ta kifa kanta saman gwiwoyin ƙafarta, kukan daya kusa yin rugu-rugu da zuciyar Amir dake zaune yana fuskantarta daga ɗan nesa da ita, yana jin zuciyarsa na matsewa da wani irin zafi. Ya ɗauke ƙwayar idonsa daga kanta ya mayar kan magungunan daya ɓallo a hannunsa, sai kawai ya janyo ledar magungunan dake kusa da shi ya zuba su aciki ya ɗaure. Ya sauke numfashi very calmly yace da ita. "ba saboda na takura miki ba, saboda lafiyanki Halima...but kiyi shiru ki bar kukan na zubar kin fasa sha". zatonsa furucinsa zai yi tasirin da zai tsayar da kukan nata, amma sai yaji taci gaba da abunta kamar ba da ita yay maganar ba. Sai ya duƙar da kansa a cikin damuwar da shi kaɗai yasan me yake ji, Allah ma ya sani, da ace yana da iko da har abada Halimatunsa ba zata yi ciwo ba, haka kuma da ace da yanda zai yi ciwon nan ya bar kanta ya dawo kansa tabbas da yayi hakan ko da hakan zai zama ajalinsa, shi dai ya ganta cikin ƙoshin lafiya da walwala. ya ƙara ɗago kansa ya kai kallonsa gareta, ganin har yanzu kamar ba zata daina ba yace da ita,"Halima kin san kuwa irin zafin da nake ji a zuciyata?, ki yiwa girman Allah ki daina wannan kukan wallahi ko kaɗan bana sonsa, yana taɓa zuciyata...indai magani ne nace ba za ki sha inace shikenan ko?". Fillo ta ɗago da kanta, idon nan ya ƙara yin loko yayi jawur, jijiyoyin kanta sun fito raɗau kamar idan kasa hannu zaka kamosu waje. Amir ya tsareta da idanu ita kuma tana saka hannu ta goge hawayen, amma da ike ita ɗin me ruwan hawaye ce tana gogewa wani na kuma sakkowa. Ita ɗaya tasan irin azabar da ta ke ji a gaba ɗaya jikinta, ita ɗaya tasan me ta ke gani acikin barcinta tun daga waccan ranar zuwa yau. cikin muryarta da ta disashe da kuka tace,"ni nace maka waɗannan magungunan naku babu abunda zasu yi min. ka daina asarar kuɗinka Amir, kawai a kira Malami yayi min adu'a". Amir dai dubanta yake da mamaki, ita ba aljanu ba amma kusan sati biyu kenan da ta ke ciwon nan ta kafe akan ita dai a kira Malami yay mata karatu, ba maganin asibiti bane maganin ciwon da ke damunta. kuma anyi anyi ta faɗa me ta ke ji tace ita babu komai zazzaɓi ne kawai. Asibiti kuma a duka test ɗin da suka mata sunce ma babu maleria. Cikin kwantar da murya yace,"insha'Allahu kin daina shan maganin, amma ki bar kukan gaba ɗaya hakan kawai zai sa na kira Malam yay miki adu'a". Ta ɗan kafe shi da ido tana tunani cikin ranta, maganarsa da ta kutso cikin kanta ta katse abunda ta ke tunani. "amma tunda nima kusan Malamin ne nayi maki adu'an ko Halimatu na?". Kai ka
🏠