NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 199 of 323

n kar da kuce min baku amince ba shisa ban faɗa muku ba nayi gaban kan nawa, amma dan Allah dan Annabi kayi haƙuri ka yafe min". Baffa yace,"to wa yay maka waliccin auren?". yace,"ba kowa Baffa, ni da naje wurin Baban nata izinin auren naje nema shine yace sai dai na aureta a lokacin in ba haka ba zai bawa wani ita". Baffa yace,"kai kuma ba zaka iya rayuwa babu ita ba?". ya girgiza kansa da sauri yace,"a'a Baffa, kawai naji ina da son ta zama mallakina a sanda na san waye mahaifinta". Baffa ya girgiza kansa,"har yanzu labarin film kake ban Muhammad, waye zai ɗau ƴarsa ya aura maka babu waliyi kamar dai wani mahaukaci irinka?". yace,"idan baka yarda ba zan iya kai ka wurin limamin masallacin da ya ɗaura so you can believe me". Baffa yace,"why not wajen mahaifinta daka ce ka damƙawa sadakin?, ko kuma da limamin ku ka haɗa bakin ƙarya?". Turaki ya kalla Fillo da yake jin kukanta na taɓa zuciyarsa yay ƙasa da murya sannan yace,"saboda yana da son zuciya ba lallai ya faɗi gaskiya ba idan akaje wurinsa, mugu ne zai iya cewa ma bai san da maganar ba". Baffa yace,"kamar yanda kaima baka da gaskiya ba, becoux i cant believe cewan kaje kaima kanka aure ba tare da saninmu ba kawai saboda zuciyarka na ganin abinda ya dace kayi kenan, da ta taimaka maka kana so ka saka mata ba akwai hanyoyin kyautatawa da yawa ba? dole lallai sai ka aureta sannan zaka biyata da abinda tayi maka?". Turaki yay girgiza kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, gani nayi ko duka dukiyarmu aka bata ba'a biyata ba". sannan yay saurin ɗauko wayarsa ya shiga file manager ya lalubo record ɗin da yayi yace,"kuma Baffa zaka yarda da ni in kaji wannan". su Maama sukai shiru suna sauraron Hayyo dake cewa,"ni idan har ka tafi ba zan yarda da cewa iyayenka zaka je ka kawo ba, ka ajiye sadakinta kawai shine nasan da gaske aurenta kazo nema, duk da ba ƴata bace amma zanyi abinda uba na gari ya dace yayi a matsayina na wanda yaga an haifeta a titi na taimaka musu ita da uwarta, in kuma ba sadakinta a yanzu ina mai tabbatar maka kana barin wurin nan zan aurawa Malam Mudi ita tunda nasan inda take, sai muje da hukuma aje wurin tsohuwar da ta saceta mu karɓota". haka suka dinƙa sauraron maganganun Hayyo har zuwa sanda Liman yace da Turaki ya ajiye sadaki, ya jiye maƙullin motarsa bayan ya shaida musu cewa shi maraya ne baida iyaye, Hayyo kuma yace ya ba shi ita sai su haɗu can su zama shege da shegiya su haifi ƴaƴan sunnah. Baffa ya dinƙa kallon wayar Turakin kamar Hayyo yake gani acikin wayar, Kaka ta zabga salati tana faɗin,"wallahi tallahi wannan muryar Hayyo ce gata nan tarrr, yanzu lalacewar tasa har ta kai ya sheganta yarsa?, kai jama'a wannan duniya ina zaki damu?, ina azzalumai suke so suje da ɗumbin alhaki?, me ya sami Hayyo ni ƴar nan?, ni da nake uwar matarsa ma yana cewa bai sanni ba?, to wallahi tallahi Fillo ƴarsa ce ta sunnah ma kuwa, mutuwar zuciya ce kawai irin tasa da yake cewa a titi ya tsinto su, amma ai Allah yana ji yana gani". Ummi na kuka sosai tace,"akwai Allah, akwai ranar hisabi, ko da na yafe zaluncin da Hayyo yayi min a zaman aurenmu ba zan yafe sheganta min ƴa da yayi ba, ba zan yafe masa ba sai Allah ya saka min". Fillo tai jikin Ummi tana kuka sosai da jin maganganun Hayyo da suke yi mata zafi, kukan da duk ya taɓa zuƙatan wajen. Kaka na kuka tace,"waye kuwa zai so haɗa jini da Hayyo banda ƙaddara". Baffa yace,"shi waye shi ɗin ne?". Kaka tace,"Hayyo ai sheɗani ne, ba zaka tabbatar da hakan ba sai ka aura masa ƴarka, matansa sunfi goma kuma duka babu wacca ya saka, kowacce gajiya take tayi da muguntarsa ta bar masa gidansa, da zarar ya sami abinda yake so a wajen mace shikenan kuma ta zama abar banza a wurinsa tun balle ki sami ciki saboda baya son ƴaƴa, ba ya aje abinci a gidansa kuma baya bari a fita a nema kuma baya yarda masu taimakawa su kawo masa". ta numfasa ta ƙara cewa,"kaga wannan". ta faɗa tana nuna masa Ummi, tace,"maraicin uba ne yasa tayi zaman gidan Hayyo, har ta haifi wannan ƴa bai daina dukanta ba, saboda kawai ta haihu har sau biyu kuma taƙi tayi zuciya ta bar masa gida, ita kuma ƴaƴanta kawai take tausayi duk da tana da ɗan banzan haƙuri, akan dalilin barinta gidan ma abinci aka aika mata daga gidan wata ƙawata yana zuwa ya haɗa da ita da wadda ta kawo abinci da wannan ƴa yay musu duka, sannan yay mata zagi na ƙare dangi irin zagin da ko dabba ba aiwa shi ba, mahaifinta dake ƙasa kansa na san sai yayi baƙin cikin wannan aure saboda kiran sunansa da yay yana zaga, kuma wallah banda wannan yaro yay jihadi ya aureta ina me maka rantsuwa da Allah siyar da ita zai yi, dan manyan ƴaƴansa mata 3 wallahi tallahi duk siyar da su yay, bafa siya irin ta abayar da sadaki ba, a'a! a taya ɗan mutum a ɗau kuɗi a bashi ya ɗauko yarinyar ya bayar a tafi da ita, kuma da bakinsa zai faɗa yace ya siyar da wance shi baida hurumin rayuwa da ƴaƴa". kowa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zuciyar Baffa na tafarfasa yace,"siyar da ƴa
🏠