taimakon da ba kowa zai iya yi min ba shisa na aureta saboda ina ganin hakan shine mafi cancantar sakayyar da zanyi mata".
"Taimako?". Baffa ya tambayesa. ya ɗaga kansa,"ehh Baffa, kuma ka tambayeta kaji".
Baffa ya kalli inda Fillo take kamar yanda Hajiya Madina ta buɗe ido tana kallonta, kar dai ta faɗa masa duk shirin da su Samha suke yi akansa, kuma tunaninta bai kai ga nisa ba taji Fillo na cewa Baffa,"ni bai aureni ba Baffa, bai ma san a inda Abbana yake ba, kuma banyi masa taimakon komai ba".
Turaki ya saki baki yana kallonta da mamaki, sai kuma yace,"ehh Baffa bata san na aureta ba amma ƙarya take yi wallahi tace bata taimakan ba, taimakon da tayi min ko wanda muka fito ciki ɗaya ba lallai ya iya yi min ba, ku a bata ƙur'ani ta rantse da shi bata saka kanta a haɗari ba saboda ceto ni daga hallaka ni da aka nemi yi, wallahi Baffa asirin da akayi min ta dinga bi tana ɗaukewa".
Mum ta riga Maama da Baffa furta kalmar asiri, Fillo ta ɗago kanta a rikice tana kallon Baffa tana girgiza masa kai,"Baffa ba haka bane, ni ban san abinda yake faɗa ba".
kwarjin dake tare da Baffa yasa bata san sanda ta fashe da kuka ba tace,"wallahi Allah bani nayi masa ba, waɗanda ma suka binne asirin ban sansu ba, jinsu nayi kawai suna faɗa, ni kuma nasan bai yi musu komai ba shisa na dinga lalata musu aiki".
Baffa ya kalli Hajiya Madina yace,"kira min Kakar yarinyar nan". abinda take shirin yi kenan dama, dan ta fara tunanin anya ba aljanu a jikin Fillo, ta ɗauka waya ta kira Kaka wadda taji ta ruɗe jin tace suzo yanzu cikin gaggawa.
Mum ta dinƙa kallon Fillo cike da nazari, muryarta kaɗai ta isa ta shaida maka abinda ta faɗa gaskiya ne balle kuma ka kalli fuskarta da gaskiyar ta fito ɓaro ɓaro, to waye zai ma Babanta asiri?, akan wanne dalili?, lokaci ɗaya kuma cikin kanta da zuciyarta suka haska mata sunan Fulani Azima, take ta furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wanda yaja idon kowa kanta.
kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani zafi da tashin hankali, me sukai ma Azima haka a rayuwa?, cutarwar da tayi mata bai isheta ba sai da ta biyo ta kan ɗanta?.
kukan nata kuma shi yasa Fillo hargitsewa ta fashe da kuka sosai tana girgiza kanta tana cewa,"wallahi Allah Mum bani nayi masa ba na rantse da Allah".
Baffa yace da ita,"in har ba ke bace me yasa baki sanar ba?".
tace,"Baffa ai nasan idan na faɗa ba lallai a yarda dani ba, kuma wataƙila ma ace ni nayi masa kuma wallahi bani bace".
Hajiya Madina ta sauke numfashi, calmly tace da ita,"nutsu Fillo ki juyo ki fuskance ni". tana fizgar numfashi ta juyo ta fuskanceta kanta a ƙasa tana cewa,"wallahi Maama bani bace, wasu ne su uku, kuma ban sansu ba".
Hajiya Madina tace,"kuma kin tabbatar asirin ne?".
tai saurin ɗaga kanta,"ehh Maama haka suka ce, Allah ne shaidata".
"amma me yasa baki taɓa faɗa min ba?".
tace,"Maama ban san ta yanda za'a yarda da ni ba, kuma da naga duk na kwashe waɗanda naji sun faɗa shisa ban faɗa miki ba, kuma bana so ku shiga damuwa ma".
Mum ta fashe da kuka sosai tace,"idan na yafe na wa ba zan yafe na Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji da ko waye yake da hannu akan lamarin nan, me yarona yayi mata tsakani da Allah?".
Maama na kallon Baffa tace,"kai kam har wanne kalar zunubi ka aikata da ake bibiyarmu da asiri?".
zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"wait Baffa, ya kamata mu fara sauraran maganar da yarinyar nan tayi, ni na san wacece ita fiye da tunaninka, tunda ta faɗi hakan tabbas haka ɗinne, beside ka duba ƙarancin shekarunta ta ina zata iya haɗa ƙarya irin haka farat ɗaya?, kai fa alƙali ne kayi nazari akan furucin nata mana".
ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"yi min bayanin komai kinji, karki ji tsoro".
Fillo ta shiga basu labari tiryan-tiryan tun daga ranar farko har zuwa rana ta ƙarshe da tayi wannan accident ɗin da Turaki ya bugeta, al'amarin yay matuƙar girgiza su, suka dinga salati suna maimaitawa, Mum dai kuka kawai take yi magana ma ta kasa, banda Hajiya Madina dake ta aikin tsinuwa tana jan muguwar adu'a akan duk wanda ma ya san da zancen za'ai asirin ba iya wanda yay ba.
Ummi dai kallon ƴarta kawai take yi da mamakin da yaƙi barinta da kuma tsoron kar ace aljanu ke aiki a jikinta, dan jefa kai a irin wannan haɗarin sai mutanen ɓoyen.
Mum ta sauko daga kan kujera ta rungumeta tana yi mata godiya da saka mata albarka, haka ma Maama, sun ma rasa kalar godiyar da zasu yi mata, kamar zasu haɗiyeta saboda son yarinyar da suka ji ya shigesu, matsayin da take da shi a zuciyar Hajiya Madina ya nunku a sa'i guda.
Baffa dai yay shiru saboda abin ya ɗimauta shi sosai, abinda yaji yana faruwa a film da kuma wata nahiyar yau shi ne akan ɗansa har ma da matarsa.
Turaki ganin yacca idon Baffa ke kansa yace,"kayi haƙuri Baffa, da na zauna nayi nazari shine naga babu da abinda ya dace na saka mata da shi sama dana aureta, kuma ni banje wurin mahaifinta da niyyar aurenta ba a lokacin, tausayi ne yasa na amince aka ɗaura auren babu shiri, kuma Baffa ina tsoro