NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 197 of 323

ƙara maimaita makamancin haka ba, ba zan ƙara aiwatar da abu ba da saninku ba, dan darajan Allah kayi haƙuri ka bani damar da zan maka bayanin da zaka fahimce ni". Baffa yace da shi,"ai na kawo ƙarshen komai, sakinta kawai zaka yi dan wannan gantalallan auren ba'a zuri'armu ba". Turaki ya rumtse idonsa yana jin kamar ya kurma ihu, ya dinga roƙon Baffa akan yayi haƙuri ba zai iya sakinta ba,"dan Allah Baffa kuyi min duk abinda zaku yi min amma karku ce in saketa ba zan iya ba, dan Allah ku bani damar da zan muku bayani ku fahimta". Baffa ya jinjina kai yace,"zo nan Muhammad". bai iya miƙewa ba ya dinga jan gwiwoyinsa har ya kai gaban Baffan, Baffa ya miƙa masa waya yace,"ka kirasa kayi masa bayani, ƙila shi ya fahimceka, dan ni ban da ta cewa dan lamarinka yafi ƙarfin tunanina". Turaki ya karɓi wayar hannunsa na rawa, tun bai kai ƙwayar idonsa kan screen ɗin ba ya san wa Baffa yake nufi da ya kira, yana kallo kuma yaga sunan Hakimi ne akai calling kawai zai yi, sai yaji kamar ya fashe da kuka sanin cewa in har Hakimi ya san wannan maganar tasa kuma ƙare, ina shi ina kiran wannan azababben mutumin ya faɗa masa laifin da yayi da bakinsa, he can't even imagine yanda Hakimin ma zai yi fata-fata da shi, abu mafi sauƙi ne a wurinsa yasa a ɗaure shi bayan ya raba auren, saboda haka sai yay switching wayar off ya riƙeta a hannunsa, ko giyar wake ya sha babu abinda zai sa yay ma Hakimi bayani da kansa, ba ma ya fatan maganar taje kunnensa, inma zata je gwara ace taje masa a sabon aure zai yi, ƙaramin laifi ma yana ɗaure mutum na tsawon shekaru balle wannan da shi kansa ya san bai kyauta ba, dan lamarin aure ba abinda wasa ba ne. Baffa ya ɗaga masa murya yace,"kana ɓata min lokaci Malami, ka kirasa kayi masa bayani da kanka nace, idan kuma ka bari na ɗau mataki da kaina zaka sha mugun mamakina, sai kayi zaton bani na haifeka ba Muhammad". Turaki ya kallesa hankalinsa a mugun tashe, ya marairaice yana haɗa hannayensa yace,"don girman Allah Baffa ba sai an faɗawa Hakimi ba dan Allah Baffa, i beg you kayi min hukuncin duk da zaka yi min amma karka faɗa masa". sai kuma ya juya wurin da Maama take yace,"dan Allah dan Annabi Maama kuyi haƙuri, idan nayi muku bayani Allah zaku fahimce ni, nima ban san nayi kuskure ba sai daga baya, kuma na rasa ta yanda zan maku bayani ne shisa aka ɗauka tsawon wannan lokacin". Maama ta kawar da kanta gefe ɗaya bata ko kallesa ba, ita aurar Fillo fa ba shi yay mata ciwo ba, ofcourse yayi ba daidai ba, but da auren ya ƙare akan Fillo abin yayi mata daɗi, takaicinta ɗaya da aurensa zai ƙare a unprepared marriage, shikenan mafarkinta akan aurensa duk sai ya tashi a banza?, bacin irin ƙwallafa rai da cin burin da tayi da aurensa mussaman da ta gama saka Fillo acikin lissafin ƙarin auren nasa?, wancan an yisa ba shiri wannan ma kuma sai azo mata da wani zance na daban da hankali ya kasa ɗauka. "Maama please". ya ƙara kiran sunanta dan ya san ita ɗaya yake da ita a wurin nan, roƙon Mum won't favour him shisa ma yake tsoron kallonta. tausayinsa ya kama Maama sosai amma sai ta kawar ta dake ta kalli Baffa tace,"ka yiwa tufkar hanci kawai, ka kira Hakimin da kanka ka faɗa masa komai, mu ba iyayen banza ba ne da zai ja mana magana a bakin duniya, inma sallamarsa zaka yi ka sallame shi ya tattara komatsansa ya wuce ya bar mana gida, dan ni ba zan ci gaba da zama da ɗan wiwi ba, rashin sanin darajar iyaye har ina haka?, ai cin mutumci da rashin sanin darajar tamu yayi yawa". ya miƙe daga gaban Baffa ya nufi Mum, tana kallon ya taho ta dakatar da shi,"karka sake kazo inda nake, banda hurumi da kai. su ma ɗin da suka gaza ɗaukar mataki akanka har yanzu lokacinka suke da, ni kuwa ka iso gabana banga abinda zai hanani shaƙeka ba". sai kuma ta mayar da kallonta kan Baffa cikin ƙunar rai tace,"kai har yarda kake da shi akan ya auri yarinya?, ta ina zai soma ɗaurama kansa aure babu iyaye, shege ne shi?, ko kuma shi uban yarinyar ba ƙwaƙwalwa akansa?, ai kawai ka zartar masa da hukuncin haikewa ƴar mutane da ya nemi yayi, ka bugasa a jarida ka yaɗawa duniya, ba wai ka tsaya sauraron zantukan kare kai daga bakinsa ba, mu zai rainama wayo saboda a rabu da shi shine zai ce ya aureta, ko ya taɓa ganin anyi haka a film da zai ce zai kwatanta?, to ka zartar masa da hukuncin da ake ma ƴan iska kawai, ka mance ɗanka ne kayi alƙalanci dai-dai da yanda kuke ma masu ɓata ƴaƴan mutane, batun ya aureta ma bai taso ba ƙarya yake yi kare kansa zai yi". hankalin Turaki ya ƙara tashi matuƙa, ya zube yana dafe kansa sosai yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi tallahi na aureta, na rantse da Allah na aureta, idan ban mallaketa ba babu abinda zai sa ki samemu a yanda kika ganmu Mum, mahaifinta ma shaida ne shi ya karɓi sadakinta...kuma wallahi ni banyi auren nan domin rashin sanin darajanku ba ko kuma ci muku mutumci ba, wallahi na amince an ɗaura auren ne saboda tausayinta". ya ɗaga kai ya kalli Baffa yace,"Baffa tayi min
🏠