.
ta kasa ɗauke idonta akansa saboda itama a shock take, and gani take kamar ya sha ƙwaya ne shisa yake wannan maganar da hankali ba zai ɗauka ba.
"shi auren film ne dama?". yana kallonta yace,"ba film ba ne, namu ɗin ne dai ya zama kamar a film".
ya faɗa yana matso da ita ta ƙwace daga riƙon da yay mata ta tankaɗa shi baya, cikin sheƙar sabon kuka tace,"leave me alone, Allah i hate you, ji a matsalar daka jefa ni alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe hannuna ma, shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni".
tai maganar tana wani kukan sosai.
da damuwa sosai yace da ita,"muje". taƙi tafiya, ransa a ɓace ya doka mata tsawa,"nace muje ko".
jikinta ya fara kyarma ya kama hannunta suka fito, tafiya suke kamar marasa lafiya, ji yake kamar babu komai acikin kansa, kamar babu yawun da zai yi musu bayani, taƙaimaimai ma bai san ta ina zai fara ba.
Bello dake daga gefensu yace da Fillo,"ki ɗaga ƙafa dan Allah, acikin matsala fa muke".
suka haɗa ido da Turaki yace masa,"kaita innalillahi ni inata yin hasbunallahu".
sai da Bello yay adu'a sosai tukunna ya iya saka ƙafarsa cikin parlon, ƙafafun Fillo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa dake riƙe da nata wanda da alama forcing nata yay ta ƙasa ƙwacewa, lallai me babban suna ya riƙa da yawa.
bai yi gigin nufar inda Mum da Maama suke ba, still hannunsa na riƙe dana Fillo ya wuce ta bayan kujerar da suke suka zagayo ta ɗaya side ɗin, Fillo tayi-tayi ta ƙwace hannunta ya hana hakan har suka zo tsakiya ya zauna sannan itama ta zauna, duk akan idon Baffa dake jinjina ƙarfin hali irin nasa, sai da suka zauna ya saki hannun nata tayi saurin matsawa ta bar kusa da shi.
Baffa ya ajiye wayar dake hannunsa yana girgiza ƙafa, sai da yaywa Turaki kallon tsab ya tabbatar ba ƙwaya ce ke aiki a jikinsa ba sannan yace da shi,"maimaita abinda kace ɗazu".
Turaki yace,"Baffa...". ganin zai masa dogon jawabi ya dakatar da shi wajen ɗaga masa hannu. "ce nayi ka maimaita abinda kace ba dogon turanci nace ka min ba".
Turaki ya sauke numfashi ya sunkuyar da kansa yace,"na aureta tun 5months da suka wuce".
yana yin shiru Baffa ya maida kallonsa kan Bello yace,"ehen?". yay saurin ɗaga masa kansa,"ehh Baffa da gaske ne ya aureta". Baffa ya sake cewa,"kai ka zama waliyin right?".
da sauri ya girgiza kansa ganin irin kallon da Baffa ke watsa masa yace,"a'a wallahi Baffa, ban ma san yay auren ba sai after yake faɗa min, wallahi ban san yanda auren...".
tsawar da Baffa ya sakar masa ta dakatar da shi,"shutup, waye marainin wayonka anan da zaka faɗa masa ba da kai akayi komai ba, marasa mutunci banza ƴan iska marasa hankali, waɗanda baku ɗauka iyayenku a bakin komai ba, wato har kuna da bakin ma da kuke maimaita min ko?, gaku kun balaga bari kuyi gaban kanku, to tunda ka aureta sai ka saketa yanzu dan ni ba zan yarda da wannan auren iskar ba, ba'a gidana ba, ba'a zuri'armu ba, ka saketa yanzu nace sannan ka min bayanin uban da yasa ka kai ƴar mutane cikin ɗakinka".
furucin Baffan na ƙarshe ya doka wata tsayawa acikin kan Turaki, bai san lokacin da ya ɗago yana kallon Baffa da wani bala'in tsoro ba, muryarsa na breaking yace,"saki kuma Baffa, dan Allah karka yanke min wannan tsatstsauran hukuncin ba zan iya ba".
Baffa dai ya riƙe haɓa couldn't stop looking at him, dama saboda ya ƙara tabbatar da abinda yace shisa yace ya saketa ɗin, kenan da gaske yake ya aureta ɗin tunda ga tashin hankali nan ɓaro-ɓaro akan fuskarsa saboda yace ya saketa, ya dinga kallonsa da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, yayi aure kuma har 5months duk ba wanda ya sa ni, to waye ya ɗaura masa auren?, kuma when hakan ta kasance?.
"kayi aure Muhammad?, wa yay maka auren?".
Turaki ya ƙara yin ƙasa da kansa yace,"Baffa ni ɗaya naje, dama ina da niyyar zan faɗa muku".
ran Baffa ya ƙara ɓaci yana jijjiga kansa yace,"kana da niyyar faɗa mana bayan kayi gaban kanka?, ka ɗaurama kanka aure ba tare da saninmu ba Muhammad?, kayi aure babu ni ubanka da nake raye, babu ƴan uwana, ka shiryama kanka aure kai ɗaya, yaushe ka zama ɗan iska har haka?, yaushe ka mayar da ni mutumin banza ban sani ba?".
sai kuma yay shiru ya mayar da kallonsa kan Hajiya Madina yace,"dama har haka ku ka mayar da ni mutumin banza da wofi?".
kan ya ƙara magana ta tari nunfashinsa,"ya dai mayar da mu ƴan banza da wofi, ko idan da haɗin bakina akayi kaga na bari anyi wannan zaman?, to ni wiwin ma da ya fara sha ban sani ba balle sanda yaje ya ɗaura ma kansa aure, saboda haka kayi jan idonka akansa shi ɗaya, inma ɗauresa zaka yi duk kayi ba damuwata ba ce".
sai kuma ta kalli Fillo tace,"kema ashe tantiriya ce ban sa ni ba...".
kuma bata ƙarasa ba Turaki yay saurin katseta da cewa,"Maama bata san komai ba itama".
da mamakin da yafi na da Maama ta saki baki tana kallonsa, sai ya juya yay facing Baffa yay kneeling murya a hankali yace "Kayi haƙuri Baffa, na san nayi kuskure amma ka yafe min dan Allah, wallahi ba zan