NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 195 of 323

cce ba wallahi". Hajiya Madina taja da baya tana neman faɗuwa, tai saurin dafe bango saboda daina gani da ta fara yi, ta shiga tashin hankali na farat ɗaya da take jin kamar zuciyarta na neman bugawa, batun hawan jini kuwa tasan tuni ya hau, tabi Fillo dake kuka sosai da ido, sannan ta dawo da kallonta kan Turaki bata san lokacin da ta zube ba a gabansa, nan da nan hawaye ya shiga sauko mata. tana magana da ƙyar tace,"this is not the background i gave you, ba foundation ɗina bane wannan, dan Allah na roƙeka ka ƙaryata abinda idanuwa da kunnuwa suka ji, me babban suna me ya sameka?, me kaje ka sha da har ka nemi ka aikata abinda baka taɓa aikatawa ba tsawon shekaru talatin da uku?, ina kaje aka baka wani abu kasha?, me yasa ɗazu baka ce min in barka kaje wurin matarka ba kana buƙatarta?, me ƙaramar yarinya kamila kamar Fillo tayi maka da zaka lalata mata rayuwa?, me babban suna me nai maka da zaka saka min da hakan?, so kake ka kashemu ko so kake kace mu mutu mu bar maka duniyar?, ashe da rabon kaine silar yanke farin cikin rayuwata?, ban yafe maka ba me babban suna, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, da ƙarin cewa,"ba tarbiyyata bace wannan me babban suna, ba haka na raineka ba, wannan sabon halin me muni daga ina?". Mum tace,"ki matsa daga gabansa kar na fallatso miki jini, ki matsa nace miki". ganin abinda take ƙoƙarin aikatawa Samha tai saurin doka tsalle ta dire a bayanta tana rirriƙeta. Zaytuna ta duƙe a wajen tana cewa,"Maama duk fa ba yanda kuke zato ba ne, dan Allah ku barsa yay muku bayani". a fusace Maama ta dunƙule hannu ta kai mata naushi ta baya tai mata wani mugun duka a hanci, tsananin zafi yasa tai shiru tana dafe hancin da take jin kamar ya cire. Turaki ya dinga kallon Maama dake ta kuka a gabansa, kuma irin mugun kallon da take masa in har ya bari ta miƙe akansa sai ta kaisa har lahira, ya ɗaga kai ya kalli Mum dake faman kokawa da Samha da Khaleel tana so ta ƙwace daga riƙon da sukai mata ta rotsa masa kwalbar hannunsa. ya rumtse ido sosai ya daki kansa da bango sannan ya buɗe baki yace,"Maama she is my wife, na bayar da sadakinta 5months da suka wuce, na damƙa sadakinta a hannun mahaifinta". "what?!!!". abinda Maama da Mum da Baffa dake shigowa yanzu suka faɗa tare. Bello ma dake zuwa yace,"ehh Maama ya aureta tunda daɗewa". *Vote, Comment and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Avoid error mistakes._ na kwana 3 ne🤐, ataimaka kar inji ana nemana🙏🏃‍♀ *41* with confusion Baffa ke kallon Turaki, kuma tashin hankali da damuwar dake tattare da Mum da Maama sai suka juye zuwa tsantsar mamaki. Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifta ido, so take ta tabbatar da idan a hayyacinsa yay wannan maganar, kamar dai ba ɗanta ba an sauya mata wani, kuma kamar dai yasha wani abu da ya juyar da tunaninsa. Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta mayar da ƙwayar idonta kan Bello wanda ganin zata kallesa ɗin yay saurin sauke idonsa ƙasa. Baffa yay ajiyar zuciya wadda babu wanda bai jita ba, muryarsa ta fito da amon da babu wanda bai sha jinin jikinsa ba acikinsu, ya juya zai bar ɗakin yace,"ku sameni a parlo". wannan sautin muryar tasa da kuma yacca ya juya ya fice ɗin Turaki ya tabbatar da ya gama shiga uku, Bello ma ya ɗora hannu aka ya furzar da wata iska daga bakinsa, ya san Baffa ya san ya faɗansa idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, yana da masifar son ƴaƴa shisa ma ba ya iya musu faɗa, but baya tolerating shits, ya san ba zai taɓa ɗaukar wannan kwaɓar da Turaki yajawa kansa ba, bayan wannan ɗan guntun jawabin da yay bai kuma san ta inda zai fara yin wani ba in aka tsaresu. Mum tazo ta wuce ta kusa da shi fuuu kamar zata tashi sama, kallo ɗaya zaka mata ka san a fusace take. Turaki yabi bayanta da ido kafin ya maida kallonsa kan Maama ya buɗe baki zai yi magana, tayi saurin ɗaga masa hannu,"dakata, kar ɗan ƙwaya ya sake yace zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba". sai kuma ta miƙe tai bakin ƙofa tana ƙara faɗa masa,"kar in jini a cikin lamarinka". ta fice tana jin ita bama tasan actual tunanin da zatai akan maganar tasa ba, dan magana ce yay ba irin ta waɗanda ke cikin hankalinsu ba. kowa ya fita a ɗakin aka bar Turaki da Fillo kawai, ya miƙe yana jin kansa na sara masa, Bello ya dawo yay tsaya jikin ƙofar yana kallon abokin nasa da tausayi yace,"ka taso muje tun wutar da sanyi sanyinta before ta balbala ta ƙona mu". Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fillo da har yanzu take a wajen a duƙe kowa ma ya manta da ita, kukanta take tayi bata daina ba, ya tafi yana jin jikinsa kamar mara lafiya ya isa inda take, ya ɗagota tsaye yana faɗin,"please stop this crying its hurts me alot, from today ba zan ƙara saka ki hawaye ba, i promise". ya faɗa yana ƙoƙarin ɗora kanta a ƙirjinsa, sai ta hana hakan tana ɗago da kanta ta kallesa tace,"me kace musu?". ya rufe ido ya buɗe yace,"ce musu nayi ke matata ce"
🏠