faɗawa kowa ba?".
tai ƙasa da idonta tana so ta ƙaryata zancen nasa sai taji hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta yana ɗagamata kai,"ehen am hearing you, ba kuma na son ƙarya dan nasan komai".
tayi narai-narai da idanu tace,"ni fa duk ban san me kake cewa ba, ni waye yace maka na ɗauke asiri akanka?".
yace,"bakinki". ta waro ido waje tace,"da yaushe?". yace,"ranar da kike bawa ƙawarki labari a asibiti, accident ɗinki na farko da na kaɗeki". tace,"da ma kaine ka kaɗe ni akace wani ne?". kan yay magana ta tari numfashinsa da faɗin,"shima kana sane ka kaɗeni?".
ya galla mata harara da cewar,"ehhh sai ki haɗa duka har marinki ki rama, yanzu amsa min tambayata".
ta tankaɗe shi daga gabanta ta bar wajen da sauri, tana zuwa bakin ƙofa ya isa ya fizgota ya haɗeta da bango yana faɗin,"Allah you are going no where sai kin amsa min tun yaushe kika sanni?, kuma me yasa kika min asiri?".
hakan yasa ta sakin kuka sosai, tana rantsuwar,"Allah ni ban taɓa saninka ba sai da na fara aiki a gidanku, sunanka kawai na sani ajikin takardar da akai maka asiri, amma wallahi bani nayi maka ba, banma san su waye ba jinsu nai kawai suna faɗa, kuma ma ai saboda idan na faɗa ba za'a yarda da ni ba shisa ban faɗawa kowa ba, ina tsoron kar ace ƙarya ne ni nayi maka, amma na rantse da zatin Allah bani ce nayi maka asiri ba".
tai maganar idanuwanta a rufe, dalilin ba zai iya jin kukan ba ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"na yarda daina kukan cry cry Baby, kanki zai ciwo za ki zazzaɓi".
tana fizgar numfashi da ƙarfi tace,"wallahi Allah bani bace kuma ban san su waye ba".
ya ƙara yin ƙasa da murya very calmly yace,"ohh nace na yarda, na yarda ba ke kika min ba shikenan daina kukan haka, ko ba kya so na barki ki tafi?".
da sauri ta girgiza kanta,"ina so".
yace,"to inji kinyi shiru sai in barki ki tafi".
ɗiff ta ɗauke wuta kamar ba ita ta cika ɗakin da kuka ba yanzu, ta lafe a chest ɗinsa tana jin yanda heart ɗinsa ke bugawa ba irin yanda ta san ainihin bugun zuciya ba, shima fuskarsa kwance akan gashinta ya lumshe ido, wayarsa na ta uban ringing bai ma san anai ba.
har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo daga shi har ita ba wanda yaji motsin buɗe ƙofar balle kuma motsin mutum.
Hajiya Ramla tai mutuwar tsaye daga inda take tana neman bango ta dafe, kafin dai tayi ƙarfin halin ɗaga ƙafarta da take jin kamar ta mutu ta dawo saitin inda zata ga fuskar wacce yake rungume da ita haka, bata san ba ko matar tasa ta dawo basu sani ba, sai dai tana zuwa ganin fuskar Fillo wacce idanuwanta ke lumshe yasa tai saurin ja da baya tana dafe bango da furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
wannan dogon salatin da taja cikin razani shi ya dawo da Turaki cikin duniyarsa, ya buɗe ido a tsoroce jin muryar Mum akansa, ya kalleta ya juya ya kalla ƙofa sannan ya juyo ya kuma kallonta, sai kawai ya saki Fillo yana ja da baya, lokaci ɗaya sai ya dawo kamar wanda ya kashe ɗan sarki aka gurfanar da shi a gaban sarki.
Mum ta bi ɗakin nasa da kallo sannan ta tsayar da kallonta akansa, ta tattaro yawun bakinta da ƙyar tace,"Babana, me nake gani haka?, kai ne da kanka tare da wadda ba matarka ba?".
sai kawai ta ɗaga hannu ta wanke shi da marin da ya kai fuskarsa ƙasa, da kanta ta ɗago da shi ta ƙara wanke shi da wani sabon marin da ya kaisa ƙasa gaba ɗaya gwiyoyinsa suka zube a gabanta.
Zaytuna tasa hannu ta rufe bakinta tana fashewa da kuka, tun ɗazu take kiransa a waya bai ɗaga ba, abinda take ta so ta faɗa masa kenan ga Mum nan. Fillo dai tuni ta durƙushe a wajen tana kuka sosai kamar ranta zai fita, cikin ƙunar rai da zafin zuciya ta rarumi lamp zata buga masa Zaytuna tai saurin riƙe hannunta tana faɗin,"Mum ki tsaya kiji".
tayi wancakali da ita gefe tai kansa tana kai masa ƙafa ta ko'ina. "mutumcin gidan namu zaka zubar mana?, dama abinda na haifarwa kaina kenan?, sheɗani na haifa dama ban sani ba?". ya saurin ɗagowa yana kallonta idonsa na hawaye yace,"Mum". bata barsa ya faɗi abinda zai faɗa ba tasa ƙafa ta daki gefen cikinsa.
"kaico, kaico da haihuwar irinka, nayi dana sanin haihuwarka, me ma yasa na saka maka sunan da ba zan iya kiranka da shi kai tsaye ba na zazzageka, me yasa nake jin ba zan iya tsine maka ba kai tsaye, wallahi na tsani ganinka, kai ba ɗana bane, yau sai dai ko ni ko kai a gidan nan".
ta ƙarashe maganar dai-dai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa a rikice, tayi fatali da kwalbar da taga Mum ta ɗauka zata rotsa masa, ta riƙeta da kyau tana cewa,"me idanunki suka gane miki your excellency da har ba zaki iya excusing ɗinsa ba".
Mum na huci sosai kuka na zuwar mata tace,"kin san i spent morethan 5minutes a bakin ƙofar nan ina jiyo kukan yarinyar nan tana roƙonsa akan ya rabu da ita, amma ɗan banzan yaron nan yaƙi barinta ƙarshe dana buɗe ɗakin ajikinsa na ganta rungume da ita tana sauke numfashin wahala, bai ma san na shigo ba tsabar ya riƙa a iskanci, ki barni kawai na kashe shi Madina ba zamu zauna da gurɓata