NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 193 of 323

i an tambayeki tare aka haife ku da Kuka kice ba haka ba". yaci gaba da yankan lemonsa yana kallonta ta gefen ido, ganin zata bar wajen yace,"dawo". ta tsaya ya ɗago yana mata nuni da gefen gadon yace,"zauna". kamar zatai masa musu sai kuma ta zauna tana aikin kumbure-kumbure. zai kama hannunta ta janye tana neman fashewa da kuka tace,"nace maka babu kyau, Allah zan faɗawa Mum". ya ɗaga gira ɗaya yace,"i will escourt you". ta langaɓar da kai cikin wata iriyar shagaɓar da bata san sanda tai ba tace,"Allah to sai in faɗawa Baffa". da sauri ya zaro ido waje yace,"kice masa me?". tace,"ince masa Turaki yana taɓani kuma har kulleni yake a ɗakinsa". ganin da gaske take maganar yay saurin cewa,"Allah ya baki haƙuri". ya faɗa yana dawowa gabanta ya gutsuro kaza ya kai bakinta,"wannan za ki cinye sai in barki ki tafi". ta kallesa ta kalli gudar kazar sannan tace,"duka?". ya girgiza kansa,"a'a iyaka yanda likita yace kici". ya faɗa yana kama hannun ciwon da ƙara cewa,"wai sai kinci iyakar yanda fatar nan da ta loma zata ciko". ta kalli yatsunta da fatarsu ta shafe sannan ta kai hannun hagunta zata karɓa ya janye yace,"kafirai ke cin abinci da hannun hagu, kawai ki yarda in taimaka in baki tunda dai baki da hannun musulmai". ba yanda ta iya haka ta dinga amsar naman da ya gutsuro yana bata, tun tana kawar da kai tana ƙin karɓa har ta gaji ta dinƙa karɓa a dole tana ci, bai ƙyaleta ba sai da yaga taci da yawa sannan ya ɗauko madarar kwali ya bata itama sai da tasha rabi sannan ya yarda ya barta, ya bata ayaba da kankana suma tasha tana jin kamar zata yi amai saboda ƙoshi, ita dai kallonsa kawai take yi tana jin wani irin abu tare da ita. ya tattare komai ya kaisu gefe sannan ya ɗauko jakar uban choculates ɗin ya ɗauko ɗaya ya buɗe ya kai bakinta, ta kauda fuska tana yamutsa fuska tace,"na ƙoshi fa, zanyi amai". ya ɗauke yana faɗin,"ashe ba ki shirya fita a ɗakin nan ba". da sauri ta janyo hannunsa ta kai choculate ɗin bakinta ta gutsura sai ɓata fuska take yi, a haka sai da ta shanye guda ɗaya tass tukunna ya kafeta da ido yana kallonta da wani sihirtaccen murmushi. bata hanasa kamo hannunta me ciwon ba, ya tmbayeta,"yana zafin ko ya daina?". tace,"yana zafi sosai dauriya kawai nake yi, kaine ina ta maka alama ka datse min hannu amma baka gani ba kaci gaba da masifarka, dan Allah ka mayar dani wajen likitan ya yanke min su na huta, kuma dan Allah ka rage masifa in ba haka ba wataran zaka iya ɓallani gaba ɗaya". ya shafo wuyansa yana wani irin murmushi da yake jin yana motsa ilahirin jikinsa da wani feelings na daban. sai taga ya sauke daga kan stool da yake zaune ya zauna gaban ƙafafunta, sannan ya ɗora kansa da hannunsa ɗaya kan ƙafafunta yace,"idan aka yanke kuma da wanne za kike wa mijinki ƙunshi yana kallo yana jin daɗi?, a barsu dai insha'Allahu zuwa safiya zasu daina zafin". ta ture kansa da ɗayan hannun tace,"ka ɗagani ba kyau". ya riƙe hannun ya mayar da kansa yana cewa,"naji, Allah kuma kika ƙara ce min ba kyau sai kin kwana a dakin nan yau". tai shiru tana sakin kukanta mara sauti, ya ɗago kansa haɓarsa kan gwiwarta yana kallonta sosai yace,"ai dama ranar nan kince min ni ke saki kuka, dan haka yi me isarki tunda yau Allah ya haɗa mu". da mamakinsa sai yaga ta saki kukan sosai, sai turesa daga jikinta take yi, tana so ta tashi, shi kuma har ga Allah yau karo na farko kenan da yaji kukan nata na masa daɗi saɓanin da sai ya dinga kukan na haifar masa da jin zafi a zuciyarsa. har tsawon minti uku bai daina kallon yanda take da bakin kukan ba kamar yarinyar ƴar 3years, yasa wayarsa yana ta mata vedio, dan kansa dai yaji kukan ya fara taɓasa tukunna ya tashi ya kamota ya miƙar da ita. jikinsa ya janyota ya rungumeta yana lallashinta yana bata haƙuri, ita dai bata daina kukan ba kuma ba tai ƙoƙarin fita daga jikinsa ba. a ranta kuwa rayawa take yau babu abinda zai hanata faɗawa Maama irin wannan abinda yake mata. ya kai bakinsa saitin kunnenta ya kira sunanta, tana shagwaɓe murya tace,"ni Fillo sunana ba Fulani ba". yace,"ba haka naga damar faɗa ba". ya faɗa yana kai hannunsa saman sumar kanta. tasa ƙarfi tana ture shi tana faɗin,"dan darajan Allah ka ƙyaleni in fita, wallahi hakan da kake yi babu kyau, ni fa ba muharramarka bace, kuma idan wani ya shigo ɗakin fa?". yace,"zan barki ki wuce yanzu i promise, but you answer me first me yasa kika dinƙa taimakona?". ya faɗa yana janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ƙwayar idonta, ta ƙanƙance ido tace,"taimako kuma?, wane irin taimako na maka ni kam?, ni ban taɓa maka taimakon komai ba, kaine ma ka taimaka min aka kulle Amir". ya matse tsintsiyar hannunta yana cewa,"kar na ƙara jin kin ambaci sunansa ko ba'a gabana ba". ya faɗa da sautin ɓacin rai da kuma kashedi me kyau. tace,"to ka sakeni in tafi". yace,"fara ban amsata tukunna, asirikan da kika dinga ɗaukewa akaina me yasa kika ɗauke su?, me yasa baki bari sun same ni ba?, kuma me yasa baki taɓa
🏠