maka ciwo".
ana idar da sallah ko cikakken azkar bai yi ba ya baro masallacin, kuma tun bai shigo gida ba ya kira Zaytuna yace ta kira Ummi ta faɗa mata Fillo zata kwana a wurinta.
Zaytuna da ɗan tsoro tace,"but Hammah kasan at any time Mum zata zo ɗakinka ko".
yace,"zance mata zan kwana office saboda wani aiki".
yana faɗar hakan ya kashe wayarsa yaci gaba da tafiya a gaggauce, a parking lot ya sami Bello ya fito zai tafi, bai ko tsaya ba ya wuce shi fuskar nan babu ko annuri kamar bai taɓa sanin Bello ba, Bello ya bisa da kallo yana dariya sosai.
sai da yay me isarsa sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Turaki, yana picking yace masa,"in tafi?". yace,"ehh tafiyarka". daga yanda yake maganar a daƙile yasan haushinsa yake ji. yace,"baka buƙatar shawarar tawa kenan?". yace,"ehh bana buƙata". ya faɗi hakan yana kashe wayar.
tun a masallaci hankalinsa ke kan Fullo, yana tafiya yana haɗa hanya saboda rashin ganin hanyar da kyau, hoton fuskarta kawai ke haska masa, a yanzu ma da zai buɗe ɗakin hannunsa duk rawa yake yi. yana buɗewa ya ganta tsaye a bakin ƙofar kamar dama jira take yi a buɗe, ganin tana neman saka kai ta fice yay saurin tura ƙofar ya saka key ya kama hannunta ya kaita bakin toilet yace,"shiga ki alwala".
ya faɗa yana tamke fuskarsa dan yaga kamar sai yayi hakan tukunna zasu dai-dai da ita.
kuma bata musa ba ta shiga toilet ɗin jikinta sai kyarma yake, ba jimawa ta fito tana kyaɓe fuska kamar zata yi kuka tana yarfe hannun me ciwo, ya kamo hannun ya dinga hura mata iskar bakinsa me ɗumi har sai da ruwan wajen ya tsane tukunna ya ƙyaleta. ya riƙe hannunta yaje ya shimfiɗa mata darduma ya buɗe closet ɗinsa ya ciro sabon hijab da Granny taje saudiyya ta taho dasu ta raba musu tace suyi kyautarsa, shi kuma baida wanda zai bawa hakan yasa ta ajiyarsu suna nan kusan guda biyar.
Fillo taƙi karɓar hijab ɗin har hannunsa ya ƙage, ya ƙara ɗago da hannun ya miƙa mata taƙi karɓa, shi dai ya san mayafinta na mota balle tace da shi zata yi.
ita ko ta bisa da kallo da mamakin zuwan hijab cikin kayansa, zuciyarta taji tana neman dasa mata wani banzan tunani tayi saurin kawarwa, itama ta haɗe rai daidai da yanda ya haɗe nasa ta turo baki ta bar kusa da shi ta tafi kan dardumar tana kunce ɗankwalin kanta ta yafa.
kawai sai ya tsaya yana kallonta da mamaki baki a buɗe yace,"a hakan za ki sallar?". ta ɗaga masa kai kawai, abinma sai ya kusa basa dariya, ya tafi yaje ya tsaya ta gabanta yana ƙare mata kallon mamaki da kyau, bilhaqqi da wannan guntun mayafin zata yi sallar tunda gashi har kabbara tayi, mamakinsa bai ƙare ba kawai yaji ta fashe da kuka tana cewa,"to ni ba zanyi da wannan hijab ɗin ba".
ya kalli hijab ɗin ya kalleta sannan yace,"ba'a sallah da irinsa ne?". ya tambaya da gaskiyarsa saboda irin me kwalliyar nan ne na saudiya.
taja majinar hancinta tace,"ni kawai ba zanyi da shi ba". ya ƙara gyara zaman hannunsa a ƙirji yace,"saboda?". tace,"to ai ban san na waye ba". yace,"aina kika ga na ɗauko?". ta ɗan kallesa tace,"to me zai kawo kayan mata cikin kayanka?". yace,"sawa nake idan zan fita".
bata kulasa ba kawai ta tsuguna ta ɗauki dardumar ta bar wajen ta sauya wuri, zata tayar kawai taji ya saka mata hijab ɗin yana gargaɗinta akan,"Allah kika yi gigin cirewa sai na ji miki ciwon da yafi na ɗazu". ta kallesa tace,"da ma kana sane?". ya bar wajen yana faɗin,"ehh ina sane sai ki rama".
tai masa shiru ta tayar da sallar, saboda bata son lokaci ya ƙure mata shisa ma bata sa masa darun sai ya buɗe mata ƙofar ta fita ba. tana idarwa ta yasar da hijab ɗin a wajen ko adu'a bata tsaya yi ba ta nufi ƙofa, ta dinga murɗa handle taji ta kasa buɗewa, sai tayi ƙasa da murya ta shiga roƙonsa tana cewa,"dan darajan Allah kazo ka buɗe min, Maama ce fa ta kirani kuma ko wurinta banje ba, kaje ka ɓallo min yatsuna, kuma ni Allah bana so kake min irin haka, na faɗa maka bana so babu kyau kana kawo ni ɗakinka ka kulle, babu kyau kana taɓani, kuma ai yanzu kai ba yaro bane tunda ka yi aure ka daina irin haka".
ya ɗaga ido yana kallon yanda ta rufe ido tana ta maganar kamar me shirin sa masa duka, yaci gaba da buɗe ledar kazar da ya ɗauko yace,"zan buɗe miki amma sai in kiyi duk abinda nace".
tace,"ai nasan halinka". yace,"wane hali gare ni?". tace,"ai ko nayi ba zaka buɗe ba". yace,"ki ci gaba da saka ni magana kici gaba da zama anan, tunda nace miki zan buɗe ai zan buɗe, but in kinyi abinda nace".
tana hararsa tace,"to rantse da Allah". kamar ƙaramin yaro yace,"Allah da gaske". tace,"to me zan maka?". ta faɗa still tana tsaye bakin ƙofan, ya kalleta yana ɗan ƙunshe dariyarsa yace,"to anan zan saki aikin?". ta turo baki gaba ta taho kamar mara laka, har ta ƙaraso inda yake bai ɗauke idonsa akanta ba. ta tsaya ƙeƙam akansa yace,"hau saman kan nawa sai ki tsaya da kyau".
ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"wai mene hakan?". ya jawo ledan fruite ɗin yana yanka abarba yace,"abinda yay hakan shi yay hakan, sa