NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 191 of 323

kanta dake ƙirjinsa, tausayin kanta take matuƙa amma ji take kamar tafi tausayinsa saboda ganin kamar ma kuka yake so yayi koma yayi bata sa ni ba, so take ta zame daga jikinsa amma ya hana hakan, har sai da Zaytuna ta dawo daga pharmacy tukunna ya saketa ya duƙa ya sunkuceta kamar wata ƴar baby, tana ta kai masa duka kan ita ya sauketa amma yaƙi har suka zo mota. sai da suka shiga mota ta kallesa suka haɗa ido ta hararesa tana murguɗa masa baki tace,"ni nace maka bana son irin haka ba kyau". tun ɗazu sai yanzu ya ɗan sami relief jin muryarta da yay, murmushi ya sauka a leɓensa ya kai hannu zai shafo fuskarta ta ture hannun tana cewa,"nace ma ba kyau". a wannan karon kawai sai ya saki murmushi me gaba ɗaya yace,"to naji". cikin allurar da akayi mata dama har da ta bacci, so ko doguwan tafiya basu yi ba bacci ya ɗauketa, ya kwantar da ita sanda yake nunawa Zaytuna wani suya spot yana cewa ta tsaya a wajen. haka ya dinƙa tsayar da Zaytuna yana siyan kalolin nama a duk suya spot ɗin da ya gani, Fillo dai nata bacci bata san me ake ba, fruites ɗin ma da ya siya kamar me kafa tebur, a ƙarshe ya shiga wani store ya kwaso uban choculates kamar zai buɗe sabon kanti da su, gaban motar nan dai sai da ya cika maƙil da uban kaya kace mara lafiyan da ya shekara a asibiti za'a kaima. akan cinyarsa taita baccinta har suka iso gida, yace da Zaytuna ta zagaya ta can bayan part ɗinsu tayi parking acan, lokacin yamma tayi ana gab da magriba garin yayi duhu, ya fito ɗauke da Fillo ya shiga ta ƙofar da babu me ganinsa ya shiga part ɗinsu, Bello ya tarar zaune a parlonsu ya ɗauke kansa kamar bai gansa ba yay bedroom ɗinsa, akan gadon ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta da shi yana yi mata peck a kumatu. Zaytuna kuma ta dinƙa shigo da uban kayan da ya siya tana ajiyewa, ta tsaya tana kallonsa yanda ya zube a gaban gadon gwiwoyinsa duk a ƙasa ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta kamar zai haɗiyeta, ko me neman gafara ko wanda akace in ya tashi za'a saceta, ta sauke numfashi tana tunanin ta yanda za'a faɗi wannan aure dai, da kuma yacca za'a karɓe shi, sannan ta ankarar da shi cewa an fara kiran sallah a masallaci. kansa kawai ya gyaɗa mata alamar yaji, ita kuma tasa kai ta fita daga ɗakin haka kawai tana jin faɗuwar gaba da kuma tausayinsa. da ƙyar ya iya miƙewa yaje yayi alwala ya fito shap shap, ya ƙara zubewa a gaban gadon yana shafa fuskarta, ji yake kamar ya bari kawai yay sallarsa a gida ba sai yaje masallaci ba. ya kamo hannunta me ciwon wanda hakan yasa ta ɗan motsa amma bata tashi ba, sai ya dakata da motsin da yake yi, ya dinƙa kallon yatsun yanda suka koma, ta ƙara basa tausayi sosai yana jin kamar ya ciro zafin ya dawo da shi jikinsa, yana jiyo sautin ƙarar da ta ƙwala tana kiran sunan Ummi. jin ƙarar buɗe ƙofa yasa shi waigawa, ganin Bello yasa ya miƙe da sauri yana haɗe rai tare da ɗaukan keys ɗin room ɗin yace da shi,"lafiya?". Bello ya kalli Fillo sannan ya kallesa yace,"uban me ka yiwa ƴar mutane?". Turaki yace da shi,"ina ruwan munafuki da abinda ya shafeni ni da matata". Bello yay dariya yace,"you find the solution right?". yace,"you don't have any access to worry about that, its my personal issue, so get out". ya faɗa yana nuna masa ƙofa. Bello na kallonsa ido waje yace,"in fita daga ina?". Turaki ya kuma ɗaure fuska yace,"i don't want to waste my time masallaci zanje, dan Allah fita". ya faɗa yana tura Bello. a ƙufule Bello yace,"dilla Malami alwala zanyi ko baka ji ana kiran sallah ba ne". yace,"ba anan kaɗai ne akwai famfo ba, in ba zaka iya shiga other toilets ba sai ka bari kayi a masallacin, ko in kaje gidanku kayi". Bello na ƙunshe dariyarsa yace,"ban key ɗin zan rufe idan na gama". Turaki yay masa wani kallo yace,"ka rufe ina in ka gama?". yace,"to ai naga kamar saurin da kake yi ne yasa ba zaka iya barina nai alwalar ba". Turaki ya juya ya kalla Fillo dake baccinta peacefully, yay ƙasa da muryarsa yana cewa da Bello,"kayi a hankali mana karta tashi, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri kaje toilet ɗin Khaleel ko na Sameer kayi". da rainin hankali Bello yace,"to ni anan naga damar yi dan haka ba inda zanje, mene za'a ɓoyen da za'a hanani alwala, shigowarka ai bai isa har ka aikata wani abu ba". Turaki ya rumtse ido yana jin kamar ya saka masa ƙafa yace,"kaiwa Allah ka bar ɗakin nan Bello, baka san zafin da nake ji a zuciyata ba kana kalle min matata kwance akan gadona, kai baka san haramun bane hakan?, Allah banda bana so ta tashi tuni nasa maka ƙarfi ka fita". Sai da Bello yaga ransa ya ɓaci sosai sannan ya juya ya fita, yana faɗin,"sannu me mata". Turaki ma yabi bayansa da sauri yasa key ya rufe ƙofar. yana kallon Bello dake tsaye ta ƙasan ido yace,"maye kawai". Bello yay ƙwafa yace,"ka buɗe ɗakin sai in nuna maka ƙarshen maita a gaban idonka". Turaki yaja tsaki yay gaba bayan yace masa,"mahaukaci, kuma ka bar min ƙofar ɗaki in ba haka ba na dawo na sameka Allah sai na ji
🏠