NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 190 of 323

sunanta yana girgiza fuskarta. shiru bata amsa ba kuma kamar bata numfashi balle ta motsa, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi ya tattaro ƙafafunsa ya haye kan kujerar gaba ɗaya yana ƙoƙarin janyota jikinsa, can ƙasa yaji muryarta ta fita a wahalce da cewa,"hannuna". ta faɗa tana kama gaban rigarsa ta riƙe. yace,"what?". ta ƙara cewa,"hannuna". ta faɗa tana fizgar numfashi. a burkice yace,"hannunki?, me ya sami hannun naki?". bata iya ce masa komai ba sai rufe ido da tayi ta ɓingilar da kai a jikinsa. sai ya kamo hannunta dake jikinsa ya duba yaga babu komai, ya kai hannu zai kamo ɗaya kawai sai ƙwayar idonsa ta sauka akan yatsunta dake jikin ƙofa ya ɓame da su, bai san lokacin da ya furta,"innalillahi wa'inna ilaihi waji'un". a matuƙar gigice ba ya saketa daga jikinsa. da sauri ya buɗe murfin motar, daidai lokacin ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ta wahala, gumi ya keto masa kamar yanda itama ta haɗa uwar zufa duk da ac ɗin dake cikin motar, ya kamo hannun yana duban yatsun, sunyi jazur jini ya tare a waje ɗaya, fatar da farcen sun haɗe sun laguɓe, siririn ƙashin wajen kamar ya karye, sai kawai ya rufe idanunsa yana kai yatsun ya saka su cikin bakinsa, ya cika bakin da iska ya hura musu iska, ɗumin iskar ya ratsa yatsun har ɓargon jikin Fillo. tayi wani zullo a jikinsa saboda tsananin azaba, ta saki sabon kuka tana cewa,"da zafiii". ta faɗa da ƙyar cikin mawuyacin hali. ya rugumeta sosai yana ɗora haɓarsa kan fuskarta yace,"am sorry Fulaniii, i didn't do it to you on purpose, please am very sorry". yaji yacca tai wata iriyar shaƙuwa, irin shaƙuwar dake fitowa ba saboda ƙishirwa ba sai dan tsananin azabar da mutum ke ji, ya rumtse idonsa sosai yana cije leɓensa na ƙasa, yana jin kamar duk duniya ya rasa jin daɗinsa har mutuwa. wucewar sakanni 30 ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa ya kira Zaytuna, tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba yace,"fito da sauri". Tsantsar damuwar data tsinta a muryarsa ita ta shaida mata babu lafiya, kuma ita tasa ta fitowa da gudu bada sauri ba, tana zuwa bakin motar ta leƙo tana cewa,"Hammah lafiya?". ta tambaya da fargaba ganin tashin hankali shimfiɗe a fuskarsa. bai amsa mata ba ya fito daga motar ya zaga ya ɗauki Fillo ya shiga baya da ita, sannan ya iya cewa da Zaytuna,"mu wuce asibiti". ya faɗa muryarsa a sama kamar ita ke da laifin. akan hanya tana tambayarsa me ya faru amma bai iya ko amsa mata ba, sai jijjiga Fillo yake a hankali kamar yanda ake lallashin jaririn da ake son yay bacci, kuma har suka isa asibitin yatsun Fillo na cikin bakinsa kamar yanda take rungume tsam ajikinsa tamkar zai sakata cikin ƙirjinsa. ba asibitin su Dr Yusuf suka je ba, dan gani yake idonsa idon Dr Yusuf ba za'a kwashe ta daɗi ba, wani abokinsa ya kira Allah ya taimaka yana asibitin, allurar lidocane aka yi mata don kashe zafin wajen, aka haɗa mata da drugs na pain reliver, duk tsoronta da allura amma ko kusa bata yi kuka ba saboda wahala ba zata barta yinsa ba, tanalafe jikin Turaki sai kallo da ido kawai, haka ma maganin da Zaytuna ta bata tasha sam bata iya musawa ba, ta zama kamar hoto sai kallon Turaki da duk ya hargitse take yi. ya sauketa daga jikinsa ya zauna da ita kan kujera ya fita cikin sauri, in few minutes sai gashi ya dawo da malt da madara peak kamar wanda likita yace masa tana da buƙatar jini. Zaytuna dai sai kallonsa take yi tana murmushi tana kuma tausayinsa, ganin yacca duk yake ta abu kamar ba Hammansu da ta sani ba, ko su suka ji ciwo ko rashin lafiya baya wannan rawar jikin akansu, akwai shi dai kulawa kamar me ba irin wacca take gani a yanzu ba. ta bisa da kallo har ya isa dispenser ya ciro cup ya haɗa malt ɗin da madara, ya durƙusa gaban Fillo ya kama hannunta ɗaya yana murzawa tare da kai cup ɗin bakinta, idonta ƙyam akansa da rashin makamar ma wanne irin tunani zata yi, ya kwantar da murya cikin sigar roƙo da lallashi yace,"please kisha kaɗan". ta girgiza masa kai idonta na tara ruwa, yay saurin saka handky ya matse hawayen yana cewa,"kukan ya tsaya haka please bana so, ciwon zai warke yanzu, aima ya kusa daina zafin ko?". sai kuma ya ƙara kai cup ɗin bakinta yana cewa,"please drink a little". yacca face ɗinsa tayi turning zuwa na ban tausayi da kuma magiyar da yake yi mata yasa ta buɗe bakin ta sha kaɗan. yana ganin ta kau da kai ya miƙawa Zaytuna cup ɗin ya ɗora hannayensa saman ƙafarta yace,"am sorry pleaae forgive me, ba da niyya nai ba ban san hakan zai faru ba". ya miƙe ya fita ya dawo, lokacin Dr Anwar ya gama shafa mata wani magani a wajen, Turaki ya kasa tsayuwa waje ɗaya sai durƙusawa da ya ƙarayi agabanta yana riƙe hannun a hankali yace,"zafin yana raguwa?". tana kallonsa kawai wasu sabbin hawayen suka sauko mata, wannan ya ƙara rikita shi ya miƙe yana ɗagata ya rungumeta a gaban mutane dake ta wucewa. "Fulanii bana sane, am sorry dan Allah". yanda taga duk ya gigice ɗin nan ya ruɗe ta tabbatar da baya sane ɗin, dan haka kawai sai tai masa knodding
🏠