kan mata ne".
Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"ai nai zaton idan munje ɗakin soyayya zamu sha". tai murmushi ta kama hannunsa. "to kai dai muje mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs.
****
"ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fillo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba".
Kaka ce ke maganar tana daga cikin ɗaki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fillo asibiti, dalilin ma daya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kaisu, acan asibiti suka tarar da shi dan da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta.
tun wancan ranar da Fillo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yay ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi.
A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fillo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini.
ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da akai bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. dai-dai da ruwan sha wannan sai daya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba.
Fillo dai kukanta ta ke rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abinda take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da akayi mata. allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba.
"kinga yau burabusko akayi...Allah sarki su Yami sun sha aiki". Maganar Kaka keyi tana ɗiban burabuskon dake cikin kwano ta saka a baki. ta kalli Fillo tace,"tunda kina sonsa daure ki tashi kici".
Fillo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da takeyi tace,"miyar mene?".
Kaka tace,"miyar ganye ce, kuma yayi daɗi sosai".
Fillo ta koma ta kwanta,"ki aje min zanci anjima". ta faɗa sannan taci gaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya.
"Allah ya shirya min ke...ni banga wani hankali a tare dake ba da Amir ya gani ya nace miki".
"ni daga yau ai babu ni babu shi, can yaje ya nemi wata ba dai ni Haliman Dada ba, dan ba zanje gidan da za'a kassara rayuwata ba".
Kaka ta taɓe baki,"to dama Fillo waya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki".
Kaka na sauraron radio akai sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin daya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama.
"jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a sanda ta ke bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan tace,"ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo".
Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka tace,"sai dai ban gane wacece ba wallahi". Tai maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin dake fuskar.
"ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake".
Kaka ta washe baki tace,"ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan...sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace...bari na kawo miki ruwa".
Ta miƙe Zaytuna tace,"a'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce". Kaka tace,"ai ko ba za ki sha ba saina kawo". Ta faɗa tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta ɗauko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu ɗazu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna suna daɗa gaisawa.
Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe ta ke, amma gudun kar Kaka taji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon daya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane.
Ɓangaren masu aikin a haɗe yake, amma kuma kowa da gefen da yake.
kan Kaka a ƙasa tace,"ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace". Zaytun tace,"a'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku". "Allah sarki aikuwa mun gode".
Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store tace,"ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne...akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, banma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min...da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu".
Kaka tace,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo...itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na ɗaukota".
Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tai saurin danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon dake manne a zuciyarta