NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 187 of 323

l, kawai dan dai bani da yanda zanyi ne, bana son fitina sannan bana so yarona ya rasa kwanciyar hankalinsa, amma wallahi da sai Babana ya saki yarinyar nan, bana gudun maganar mutane, girgizar al'arshin ubangiji ne bana so". "wait your excellency, me Madina ta kimtsa miki a dawowarki?". ya faɗa yana dafa shoulders ɗinta. tai guntun murmushi tace,"ai ko Madina bata kimtsan komai ba, ba zan taɓa son auren nan ba, balle ma bata kimtsan ba, let me tell you this; i hate Fulani Azima with passion, hakama duk wani abu da ya shafeta, kamar yanda ƴarta ma ƙaunar ganinta bana yi balle kuma aurenta da ɗana, kawai dan banda yanda zanyi da abinda ku ka ƙadarta masa ne. but you keep in mind duk ranar da Babana sees his life choice no one will stop him from getting another marriage, ya zama dole a barsa ya auri zaɓinsa kamar yanda aka tilasta masa auren zaɓin wasu, yana da damar da zaiyi mata huɗu addini ya halatta masa hakan, so banga dalilin kuma da zai sa ace ita da ubanta ya zauna da mata huɗu ace ba zata zauna da kishiya ba, there is no such thing at all, Babana ba ƙaramin yaro ba ne". da tsananin mamaki Baffa ke kallonta, tunda yake da ita bata taɓa rufe ido irin haka tana faɗa masa magana ba dake fitowa daga can ƙasan ranta, tafi Madina haƙuri nesa ba kusa ba, ta kan haƙura da duk kalar zaluncin da akayi mata ta barwa Allah, ansha cutarta ba sau ɗaya ba sau biyu ba tace ta haƙura ta yafe, sometimes ma sai dai Madina ta tayar da jijiyoyin wuya a madadinta. amma yau duk abinda yake jin tana faɗa daga can ƙasan ranta yake fitowa, and she means duk abinda ta faɗa ɗin. ya buɗe baki yana so ya kawar da ɓacin ransa yace,"kin san kuwa Boɗejo ce ta shirya wannan auren?, kuma kin san ita tace bai isa ya ƙara wani auren ba sai in mutuwa Ilham tayi?". ta kama maɓallin rigarsa tana saka masa tace,"idan har kai zaka bi umarnin mahaifiyarka to shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar". ta faɗa sanda take gama ɓallewar, sannan ta nufi saman mirror ta ɗauko glasses ɗinsa ta saka masa. "yau dai ƙila gwamnati taci tararka dan ka makara da yawa". ta faɗa tana basa peck a goshi. shima yay mata peck a kumatun yana cewa,"yau ɗin rana ce ta musamman a wurina, dan haka office dole suyi min uzuri". ya faɗa yana kama hannunta su fito daga ɗakin, suka nufa downstairs, suna sauka daga steps Baffa yasa hannu ya rufe mata ido. tace,"ah Your Highness so kake in faɗi ne?". yace,"ta ina za ki faɗi bayan ina tare da ke, i want to suprise you with something shisa". tai murmushi bata ce komai ba har suka sakko gaba ɗaga daga benen, Hajiya Madina da iyalanta na ƙasan sunja line kowannensu fuskarsa na bayyana farin cikin dake tare da shi, Hajiya Madina ta saka irin shaddar dake jikinsu da akai musu ɗinki iri ɗaya. Turaki dake gaban layi ya matso ya rungume Hajiya Ramla, ƙamshin turarensa kawai taji itama tayi hugging nasa tana cewa,"Babana ya dai?, tunda na dawo kaƙi barina na huta, ko sai na mayar da kai ciki?, ko kuma sabon feeding zan fara ne?". daga kunnenta Turaki ya raɗa mata,"If all mothers were like you, planet earth would be filled with such great families. I pray that you find happiness in every second of your wonderful life. Happy Birthday to the best Mother in the world, i so much loves you Mum". ya faɗi hakan yana matseta sosai da jin wani irin shauƙi na ƙaunar mahaifiyarsa a tare da shi, nan da nan kuma duk sauran yaran suka yo kanta suna wishing ɗinta, sai da suka saketa sannan ta sami damar kallon Baffa da Hajiya Madina, sukai hugging each other suma suna mata prayers daga nan kuma ta ɗaga idonta ta kalla yanda sukai decorating parlon Baffa ya dawo kamar ba shi ba. wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta tana jin wata iriyar soyayya ta daban akan families ɗin nata na bin dukkan sassa na jikinta. suka kama hannunta zuwa ƙaton center table ɗin da aka saka, an aje cakes kusan guda shida, kowanne an rubuta happy birthday to the special Mum, kallonta na ƙarshe ya sauka akan wanda akasa Happy Birthday your Excellency, tana kallo tasa hannu zata ɗauko suka tayata ɗaukowa suka kawo mata shi gabanta, da murmushin da ya kasa barin fuskarta tayi cutting cake ɗin tana cirowa ta kai bakin Hajiya Madina dake kusa da ita ta ɓarin hagu, Maama ta karɓa suna hugging each other da hawayen da ke sakko masu wanda basu san na menene shi ba. daga nan kuma kowa sai ya shiga bata gift ɗinsa, Turaki ne na ƙarshe a wanda ya ajiye mata passport har guda biyu, ɗaya na zuwa saudiyya ɗaya kuma na zuwa agentina inda zata je ta huta taji daɗinta. Hajiya Ramla ta dinƙa saka masa albarka da sambaɗa masa adu'a. suna cikin yin breakfast ne Hajiya Ramla ke sanarwa da Hajiya Madina saƙon Boɗejo akan ɗanta, Maama bata san lokacin da bakinta ya suɓuce ba tace da Mum,"kinga manta da wannan tsohuwar da Allah, fitinarta tayi yawa wallahi, duk tsufa ya rikitar da ita, ta barsa da abinda har yanzu bai gama isarsa ba mana, idan yaje shi zai bata lafiya ne ko menene ake so k
🏠