kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min".
Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa.
"kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba".
Hajiya Ramla ta tari numfashinta da cewa,"a'a Boɗejo Maamansa ai ba zata hanasa zuwa ba, ita kanta ina mai tabbatar miki da bata san da wannan rashin tunanin nasa ba da tuni ta tsawatar masa, amma zan faɗa mata insha'Allahu".
Boɗejo tace,"to ai dama Madina ta gama hanadameki ke da ƴaƴan, sai yanda tayi da ku. ke yanzu Ramla baki da ikon sawa da hanawa ga ƴaƴanki dake kanki sai dai Madina?, ni ko a tarihi ina na taɓa jin wannan yardar dake tsakanin kiahiyoyi, ai tun a auren nan na san Madina ba haka ta bar mutane ba, to ni dai wallahi tallahi zan baɗawa idona toka, in mance da cewar Turaki jikana ne in maka shi a kotu, Allah sai nayi ƙararsa akan zaluntar Ilham da yake dan ubansa, ina na taɓa jin kalar wannan auren me cike tsantsar zalunci da rashin adalci, wato yana nufin ma bai damu da ita ba ya huta da ƙaya kenanan tunda yanzu bata kusa da shi".
Hajiya Ramla ta kwantar da murya tace,"kiyi haƙuri Boɗejo zai zo insha'Allahu".
"ke ni rufe min baki sokuwar uwa kawai wacce wata ta fita iko da abinda ta haifa".
tai maganar a fusace tana kashe wayar cikin ɓacin rai, daga can ɓangarenta sai masifa take yi a asibitin muryarta ta karaɗe ko'ina, faɗawa me martaba take cewar yazo ya kaita kotu na ƙasar nan wallahi sai ta kai ƙarar Turaki akan wofuntar da matarsa da yay, sai taga ubansa Alƙali d ya tsaya masa.
Baffa ya dubi Hajiya Ramla dake riƙe da waya tai shiru fuskarta na bayyana rashin jin daɗi, ya karɓi wayar daga hannunta wannan yasa tayi firgigita ta dawo daga gajeran tunanin da ta lula, ta sakar masa murmushin da bai fito daga can ƙasar zuciyarta ba, Allah ma ya sani ko kaɗan bata farin ciki da wannan auren tun a ranar da ta san Ilham ƴar Fulani Azima ce, kuma in ace taso a ranar ko minti ɗaya Turaki ba zai ƙara ba da auren Ilham akansa, sai ta sa ya saketa, to amma babu yanda zata yi tunda har ubangiji ya riga ya shirya faruwar hakan, tsoronta ɗaya kar Ilham ta cutar mata da ɗanta tunda shi hali ana tsotsarsa a nono.
muryar Baffa na bayyana ɓacin rai yace,"a zatona tunda har an riga anyi auren kuma yayi haƙuri shikenan komai ya wuce, ashe ƴan banza ya mayar damu, to wannan yaron sai na saɓa masa, naga alamun sai mun saka ƙafar wando ɗaya da shi, sai nayi fatali da wannan son da nake masa in har bai riƙi matarsa da kyau ba, shikenan sai ace ni ne ban isa da yarana ba, ita yarinyar ba biyayya tayi ba ta haƙura da zama da shi har take kyautata masa, ko dan ubansa an faɗa masa ita so takeyi, zai gamu da fushina tabbas, zai haɗu da ni".
Hajiya Ramla ta sauke numfashi a sanyaye tace,"ai duk da kun aura masa wacce yake yaso da hakan bata faru ba, haka itama da kun bata wanda take so da hankalin ƴarku ya kwanta, da mijinta ya girmama halin da mahaifiyarta ke ciki. to amma ya zamu yi tunda me faruwa ta riga ta faru, wata matsalar dai muke ƙirƙirarta da kanmu yayinda ta zamar mana damuwa sai mu kirata da ƙaddara, kuma ma dai banda rashin adalci har ba'a ga biyayyar da Babana yayi ba ace za'asa ƙafar wando ɗaya da shi"...
Baffa ya katseta da cewar,"wait! mu kenan bamu isa da ƴaƴanmu ba sai mu bari suke juyamu?, wato bamu isa muyi musu zaɓi su karɓe shi ba kenan?".
tace,"a'a ai ƙarshen isa ai kun isa tunda har ya yarda aka ɗaura auren, ya kuma halarci ɗaurin aure har ya iya zama da matar, amma ko a musulunce ma auren dole dai bai halatta ba, ya kamata kuyi duba akan wannan, kun san irin cutuwar da zucoyiyin zasu yi kuwa?, ko baku taɓa cin karo da labarin auren dole yasa mata ta kashe miji ko kuma miji ya kashe mata?, duk abinda za'ai ake duba da yanda zamani ke tafiya ba yacca zamanin baya yake ba. kaga your Highness to tell you the truth, I personally do not like this marriage at al