NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 185 of 323

na makarantar tasu, tace. "Maama mun kawo makaranta zan sauka". Hajiya Madina tace,"to shikenan, sai kin dawo Allah ya bada ilimi me albarka. a dage sosai kinji, gobe da safe ki shigo ina son ganinki, ko da yake ma zan aiko driver yazo ya ɗaukar min ke". daga haka sukai sallama, Fillo ta fita a motar, har ta bar wajen Samha ta kirata ta bata wani biro me kyau. ta karɓa tayi mata godiya sannan ta wuce, ta tafi tana me jin tausayin Samha a ranta, lallai rashin nunawa ɗa soyayya daga wurin uwa ba ƙaramin ƙalubale bane a rayuwarsa. banda hakan dama me zai kai su Samha ƙudurtar cewa sai sun kashe ɗan uwansu alhalin su babansu ba wata kujerar mulki garesa ba. ta tuna sanda ta zauna ta bawa Umminta labarin duk abinda ya faru ga me da taimakon da Hajiya Madina tace zata yi mata akan ta shiga jikin Samha ta dinga yawan bibiyar al'amuranta dan ta dinƙa jiyo mata plans ɗinsu akan Turaki. wannan dalilin yasa tace ta dage ta iya turanci saboda Samha bata fiya magana da hausa ba ko fulatanci sai dai english. kuma ba tare da dogon nazari ba kai tsaye abinda Ummi tace mata shine,"duk abinda yaranta suka aikata laifinta ne, domin babbar illar da zaka yiwa kanka shine ka nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka, ka nuna soyayyar wancan tafi ta wannan a gareka, ka kasa ɓoye musu yanda kake jin matsayin kowannensu a zuciyarka, tabbas idan zuciyar wani ta ɗauka ta wani ba zata ɗauka ba, nuna banbanci tsakanin ƴaƴa kan haifar da matsala sosai, domin zuciyar wasu zata yi ƙoƙarin ganin yanda za ai su kauda wanda ake so ko kuma su illata shi". Ummin tace mata,"dan haka yanzu shawara ɗaya da zaki bata tunda suma Allah yasa mahaifiyarsu ta dawo, to ta maida hankalinta kan waɗannan yaran masu raunin zuciya, karta ce zata fasa yiwa su Turakin abinda take musu dan hakan zai iya kawo gurɓataccen tunani a zuciyar mutane, ta mayar da son yaranta equal to yanda take son su Turakin, shine kawai samun kwanciyar hankalinta". *Vote, Comment, and share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *39* *08:30am.* acikin bedroom ɗin na Baffa, Hajiya Ramla ce tsaye gaban mirror ita da shi, sanye take da shadda golden colour tasha azababben aiki ajiki, anyi mata ɗinki bubun sai ƙyallin stones take yi, tayi masifar kyau kamar balarabiyar usuli, ita da Baffan iri ɗaya sak. daren jiya tailor ya kawo musu ɗinkin su uku iri ɗaya, ita take taimakawa Baffa wajen shirin da yake yi, tana shirya shi ɗin suna hira cikin annashuwa da jin daɗi tare da alfaharin ƙara kasancewa da junansu. turare ta ɗauka ta fesshe shi da shi tuni kuwa ɗakin ya ɗauka da wani daddaɗan ƙamshi, Baffa ya rungumeta jikinsa yana faɗa mata irin son da yake mata da kuma kewarta da yay a sanda bata tare da su, albarka kawai yake zunduma mata kamar yawun bakinsa zai ƙare. wayarsa tayi ƙara ta zame daga jikinsa tai saurin isa kan gado ta ɗauko wayar, sai da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne. daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba. cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya". ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai. Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar. Boɗejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita". "tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah". tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba
🏠