NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 184 of 323

ace,"ke kuma sai da angon naki ya kashe wayar sannan za ki fito, wannan kiran dai ai nasan ba namu bane, naki ne ake wani wayance da Ummi ake nema". Fillo ta turo baki tace,"angon wata dai amma bani ba, me zanyi da wannan". ta faɗa da duk gaskiyarta. Ummi ta waro ido waje tace,"iye! Auta ɗan nawa kike cewa me zaki yi da shi?, ban da shi Auta kin isa yanzu ki sani ki ƙara saka ni a idonki?, ah lallai, wato babu ko kunya a gabana kike faɗin me zaki da ɗana, ba ki san nafi sonsa ba akanki". cike da shagwaɓa kamar zata yi kuka tace,"Ummi ni to ba zan auri me mata ba, dan Allah ku daina haɗa ni da shi". Ummi na ƴar dariya tace,"idan kin kwantar da hankalinki ma nima ba zan yarda ayiwa ƴata Nuratu kishiya ba, ah tou can ki yanka kije ki samo daidai dake ɗin, nima ɗana yafi ƙarfinki dan ba abinda zai yi da ƙwaila irinki". ta miƙe cike kunya tana barin kusa da Ummi tace,"ni bama yanzu ba ai, sai na zama barrister tukunna in zaɓa in dirje, by then Abba nah ya shiryu ya gane gaskiya sai yazo ya ɗaukemu, mu koma can inda muka fito sai mu bar tsohon ɗan naki anan da shi da gwalagwajin matar tasa". ta faɗa tana ƴar dariya, Ummi ta ɗau hula ta jefa mata. "kin ci ƙaniyarki naji kin ƙara kiran Nuratu da wannan sunan, ki kiyayeni wallahi". tana dariya sosai saboda yanda Ummin tayi tace,"nima to a faɗawa mijinta ya kiyayeni ya fita a sabgata, ya bar ganin ya taimakawa Ummina hakan ba zai sa ya kafa gwamnatinsa a zuciyata ba". sai kuma ta harari Maijidda tace,"ke kuma baƙar munafuka kici gaba da min abinda kike, Allah idan baki wasa ba naje na faɗawa Hamisu me gadi kince kin amince ya turo iyayen nasa. kuma wallah ki faɗawa Dr'n da yake wahalar dake kan yi masa campeign, Fillo ba zata auri me mata saboda haka ya kama gabansa". Maijidda tace,"wallah ba zan faɗa ba, insha'Allahu sai kin zama amaryar Dr". Fillo bata ce mata komai ba taiwa su Kaka sallama ta fita tana sai ta dawo. tun satin da suka dawo wannan sabon gidan da Hajiya Madina ta basu kyautarsa ta fara zuwa islamiyya wacca ƴaƴan maƙotansu suke zuwa, makaranta ce me kyau da tsada acan wajen gidan sarki, itama Hajiya Madina ce ta sakata dan har gida tazo ta sameta tana ƙara tambayarta,"Fillo ina sonki, ina tsananin sonki Fillo, gani nake har yanzu ban kyautata miki da rabin alkhairin da kika min ba, dan haka ki faɗa min me kike so na kuma yi miki yanzu?". Fillon na kukan farin ciki tace mata,"Maama ni makarantar Islamiyya nake so in koma, ina so na haddace alƙur'ani". kuma take a wurin Hajiya Madina ta kira Khalil ya gama yi mata komai a washegari kuma ta fara zuwa. yanzu haka kuma ana ma ta processing na zana private wa'ec ne, dan Hajiya Madina na gab da tafiya wani course kuma tana so idan zata tafi su tafi tare da ita kamar yanda tayi mata alƙawari. tana tsaye bakin titi tana jiran abin hawa wata jar mota tayi parking a gabanta, gabanta ya faɗi sanda aka zuge glass ɗin motar, ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace,"Adda Samha ina yini". tace,"lafiya lau Fillo, makaranta zaki wuce?". tace,"ehh". "to shigo sai in ajeki a hanya". Fillo kamar ba zata shiga ba, saboda ita har ga Allah tana tsoron mutumin da ko da sau ɗaya ne ya taɓa cutar da wani a rayuwa, balle kuma wanda ya jima yana haddasa abubuwan za zai sa yaga bayan wani duk da Allah ba ya ba shi nasara, gani take tamkar su Samha ba akan Turaki bane kawai suke da wannan mugun hali, wataƙila sun cutar da mutane da yawa ma ba tun yanzu ba. ɗayan ɓari na zuciyarta yace mata,"ki kyautata musu zato a yanzu, ki ɗauki komai da ya faru a matsayin abinda ya jima da wucewa". Fillo ta sauke numfashi ta buɗe motar ta shiga, daga yanda ta kalla Samha na driving ɗin ta san tana cikin nishaɗi sosai. dan kamar ba wannan azababbiyar Samhan da ta sani ba a baya ba, kamar ba wannan Samhan da taji suna haɗa plan ɗin yanda zasu kashe ɗan'uwansu ba, ta saki baki sai labari take yi mata, hirar da ita dai bata cewa komai. Samha tai picking call ɗin Maama da ya shigo wayarta, daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"ina kika tafi kuma?". fuskar Samha na bayyana wani irin farin ciki da jin daɗin da bata taɓa jinta ba a ciki tace,"Maama yanzu zan dawo, naje siyo special gift ɗin da zan bawa Mum ne". ta jiyo fitar sautin murmushi a tare da Hajiya Madina wacce tace,"good, but ki dawo da wuri". tace,"tom Maama". sai kuma tace,"muna tare da Fillo ma yanzu haka, na ganta hanya zata wuce school na ɗauketa". da sauri Maama tace,"bani ita". Samha ta miƙawa Fillo wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina tace,"Fillo ƴata, Allah yayi miki albarka kinji, ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya yarinyar nan, wallahi shigowarki rayuwarmu alkhairi ne. Fillo nayi amfani da shawarar da kika bani akan su Samha kuma naga nasara, domin kuwa Samha da kanta ma tazo tana faɗa min duk abinda suka aikata ita da Sameer, Allah yay miki albarka Fillo yanzu hankalina ya kwanta banda damuwar komai, ƴaƴana sun shiryu". Fillo dai murmushi take bata ce komai ba, daidai sanda suka zo gate
🏠