asan kina raye kuma kina cikin ƙoshin lafiya shine maganar da nake yi miki".
Ummi tace,"ba yanzu ba Dada".
Kaka ta gyaɗa kai tace,"ai shikenan ban san lissafin da kike yi ba. ni Allah yasa ma ta hanyar arziƙi Hayyo yayi kuɗin da aka ce yayi".
Ummi tace,"ni banma yarda da yaron da ya faɗa ba".
Fillo tace,"Ummi da gaske ne fa, ai sanda ku ka tafi gidan Inna Azimi munje ni da su Badariyya, da muka shiga matan gidan suka ce ai kusan wata huɗu kenan da suka sayi gidan, masu gidan sunyi kuɗi sun tashi, to ni naso ma na tambayi inda suka koma kawai na fasa".
Ummi dai bata ce komai ba tayi shiru, ita ai banda ma dai bata son musawa maganar mahaifiyarta ai bata ga me zai sa su ƙara komawa Taraba ba a rayuwarsu, tunda Allah baisa sunyi dacen dangi ba, ita bata yi dacen miji ba, ƴan'uwan Kaka kaf ba wani kula suke da ita ba, kamar ma ba ciki ɗaya suka fito ba ayanda suke nuna mata, kansu da matansu kawai suka sani, dalilin da ya dawo da Kaka nan gombe kenan ta samarwa kanta mafita na neman aiki a gidan sarki, daga nan kuma ta koma gidan Dikko ga kuma matsayin da Allah ya kawo su ayau.
Maijidda ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama, su Kaka suka amsa mata ta nemi wuri ta zauna tana kallon Fillo dake jikin Ummi tana hararta da cewa,"Ummi dan Allah ki daina ɗora wannan ƙatuwar abar a jikinki".
Ummi na murmushi tace,"autar guda?".
Maijidda ta taso ta taho tazo itama ta ɗora kanta a kafaɗar Ummi tana cewa,"Ummi to nima ai autar ce".
Fillo tasa hannu ta tureta tana faɗin,"dilla ɗaga min uwa, da wani ƙaton kanki anan zaki ce zaki kwanta jikinta salon kija kafaɗarta tayi ciwo".
Maijidda ta harareta tana mayar da kanta wurin Kaka tace,"Kaka Yami tana gaisheki, wai ki bada wannan saƙon da za'a kawai Baba Huraira zata je gidan gobe".
Kaka tace,"aiko gwara da Allah yasa ta tuna min, jeki ɗakina ɗauko wannan baƙar jakar tawa ta gado ki kawo min".
Maijidda ta shiga ta ɗauko jakar ta dawo, Kaka ta ɗauko saƙon ta bata tana yi mata bayani. sannan ta ɗora da ce mata,"yauwa kuma ki faɗa mata jiya fa an karɓo kuɗaɗenmu na wajen matsiyacin yaron can, an karɓo miliyan shidan duka wallahi".
Maijidda tace,"shege ai ni naso jefe ɗan iska akayi kowa ya huta da annoba". sai kuma cikin tsokana tace,"umm in iya bakina kar Fillo ta ƙullace ni".
Fillo ta miƙe a jikin Ummi tana hararta tace,"banza kawai". ta faɗa tana tashi ta wuce ɗaki.
Ummi tace da Maijidda,"kin fara zuwa yiwa su Hajiya Madina aikin?".
tace,"ehh Ummi tun washe garin ma da ku ka taho ai".
Kaka tace,"to Maijidda sai ki kula da Allah, na san ki kema hankali da natsuwa ba daga nan ba, dan haka ki iya zamanki da mutanen nan, ki zama me gaskiya da amana da kula da aikinki, kina ganin dai ta dalilin iya zama da su da Fillo tayi alkhairin da suka yi mana, bacin haka wa zai ɗauki gida sukutun guda ya bamu kyauta?, waye zai tsaya tsayin daka akan a karɓar mana hakkinmu wajen wancan azzalumin bawan?, aini babu abinda zance da Hajiya Madina sai dai ubangiji yayi mata sakayya da gidan aljannah, mutuncin matar nan ya wuce duk mutum yake zato wallahi".
ƙarar wayar Kaka ta katse maganartata, ta ɗaga tasa a kunne ba tare da ta san waye me kiran ba dan bata iya karanta sunan ba. sai bayan kuma ta ɗaga ɗin ta ɗau muryar Dr Yusuf daga can ɓangarensa da yay sallama, bayan gama gaisawa ta tambayesa iyalin da mutanen gidan sannan yace ta bawa Ummi.
Ummi na murmushi ta amsa sallamarsa tace,"Shikenan kuma sai ɗana ya manta da ni".
Dr Yusuf ya sosa ƙeyarsa yace,"na isa na manta dake Mommi, wallahi kullum sai munyi kewarki, Mommi ban san me yasa kika ƙi yarda kici gaba da zama a wurinmu ba, ko mun miki laifi ne Mommi?".
Ummi tace,"kul Yusuf naji ka ƙara ambatar kun min laifi, ni dai kawai abinda nake so ku sani shine har duniya ta naɗe ba zan manta daku ba da alkhairin da ku kai min, ina nan zan ƙara zuwa na musamman in ƙara godiya, ina jikata Farha?".
Dr Yusuf yace,"tana lafiya Mommi, jiya ma Nuratu ke cewa tana so tazo ta gaida ke, to kuma sai naji kamar Maijidda tace kun bar can gidan Alƙali".
Ummi tace,"ehh wallahi, ai sun sallami Kaka daga aikin da sha tara ta arziƙi, sunce taje ta huta haka, wallah kam sun bamu gida anan Dubai Quaters, baka gida ba Yusuf so masha'Allah, dama nace sai munyi waya tukunna sai in sanar muku insha'Allahu, to ashe ma Maijidda ta rigani".
yace,"masha'Allahu, Allah ya saka musu da alkhairi".
"ameen Yusuf, dan Allah ka gaidar min da su Nuratu da Ammi da Umma, kai da kowa ma musamman Inna Wuro, gaisuwarta tafi ta kowa yawa".
yace,"insha'Allah Ummi duk zasu ji, sai munzo gaisuwa".
"to Allah ya kawo ku, ina nan ina zuba ido".
daga haka suka yi sallama, Maijidda na murmushi tayi tafi tace,"mu dai abinmu sharr".
ta faɗa tana kallon Fillo data fito cikin complete shirinta na tafiya makaranta, ta gimtse dariyarta Fillo ƙuma ta galla mata harara tana cewa da Ummi,"na fito Ummi". ta zauna Ummi ta dafa kanta tayi mata adu'a sosai, tana ƙara ce mata ta kula.
Kaka da zolaya itama t