waɗanda ta zalunta, shikenan ita kuma tayi biyu babu, babu nan duniyar babu can lahirar, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
sosai take kuka idonta guda ɗaya na hawaye, inama ace a dawo da baya, da tayi amfani da damarmakin da take da su ta gyara lahirarta, to sai dai hakan ba zai kasance ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, yanda kowa ke ganin saukar hawayen nata babu wanda ya fahimci me take buƙata, sai tausayinta da kowa yaji yana roƙo mata lafiya a wurin Allah.
Ilham ta ƙwace daga hannun Sauraniya Mabruka ta isa gadon ta faɗa jikinta ta fashewa da wani irin kuka, kukan da duk sai da ya saka kowa dake ɗakin hawaye babu shiri.
*Dubai Quarters, Gombe State, Nigeria.*
daga ɓangaren kudu, gida na tsakiya me lamba 20, flat house ne ɗan tsakiya me ɗauke da milk gate da abuja brown paint, sai flowers dake zagaye da ƙofar gidan, daga yanda wajensa yake da kyau zaka shaida cikinsa ma me kyau ne.
daga cikin gidan Fillo ce a ɗakinta kwance akan madaidaicin gadonta, ba bacci takeyi ba idanuwanta a rufe suka kawai hawaye na bin gefen fuskarta. ta tashi zaune tana saukowa akan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah, tana cikin sallar Ummi ta shigo, ganin tana sallar yasa ta ce mata,"idan kin idar ki fito muci abinci".
bayan Fillo ta idar ta kalli agogo taga har biyu saura, dan haka bata fita ba sai da ta saka uniform na islamiyarta tukunna, ta ajiye hijab ɗin da jakar akan gadonta ta fito cikin sauri.
Kaka da Ummi na zaune a ƙasa kan carpet suna kallon tashar arewa 24 ana maimaicin kwana casa'in, ta zauna gefen Ummi sannan su kai bismillah suka fara cin abincin, bai fi spoon biyar Fillo tayi ba ta miƙe, Kaka da Ummi suka bita da ido har ta shiga ɗakinta.
wucewar minti biyu sai gata ta dawo riƙe da jaka da hijab a hannu, ta zauna kan kujera tana kallo tv tana ji tana neman kasa riƙe hawayen dake yunƙurin zubo mata.
sai bayan da su Ummi suka kammala cin abincin sannan Kaka na dubanta tace,"kinga, kinga Fillo ki kiyaye ni, na faɗa miki ki cire batun cutarwar da Amir yay miki a ranki amma kinƙi ji ko, haka kawai kina ƴar ƙarama dake kisawa kanki damuwa salon kija mana masifa, ke bama abin farin cikinki bane tunda har aka sami bayin Allahn da suka tsaya miki hukuma tabi miki hakkinki".
take kuwa hawayen da take ta riƙewa suka zubo, ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, Ummi na kallon ƴartata da tausayawa tace,"Auta zo nan". ta taso ta dawo kan kujerar da Ummi take ta kwanta a jikinta.
Ummi na shafa kanta tace,"kina so na koma inda ba xaki ƙara ganina ba?". da sauri ta girgiza kanta da cewar,"a'a Ummina".
tace,"to ki daina kuka haka nan ya isa bana so, ki manta da duk abinda ya zama past ki focusing akan rayuwar gabanki, babu abinda zai fishsheki yanzu sama da ki mayar da hankali akan karatunki shine kawai gatanki har zuwa ranar da Allah zai kawo miki miji na gari kiyi aurenki".
bata daina kukan ba tace,"Ummi har yanzu abin yana yi min ciwo sosai".
Ummi tace,"sai ki godewa Allah da ya tona asirinsa tun bai aureki ya miki cuta me gaba ɗaya ba, ki kuma gode masa da ya kareki daga sharrinsa a iya zaman da ku kai da shi".
tayi shiru bata ce komai ba, idonta na haska mata hoton jiya sanda suka je kotu ita da su Maama akan case ɗin Amir da aka ƙarke a jiyan, tana tsaye a bayan Mum taji Turaki ya kama hannunta ba tare da sanin kowa ba suka bar wajen, kuma duk ta yanda taso ta raba hannunsa da nata ta kasa har suka shiga wani ɗaki inda aka kai Amir shi da tawagarsa, kallo ɗaya tayi masa ta saurin ɗauke kanta gefe dan a duniya idan da mutumin da bata ƙaunar gani bai wuce shi ba.
kuma tsabar rashin kunya irin da azzalumin bawa wai har yake zubewa a gaban ƙafafunta yana roƙonta Allah da Annabi akan ta yafe masa abinda yay mata, sannan ta roƙar masa alƙali ya sassauta masa hukuncin da aka yanke masa na zaman prison tsawon shekara goma sha biyar, har da wai in ya fito yayi mata alƙawari zai tuba ya koma mutumin arziƙi ya aureta.
wannan maganar kuma ita tayi mata zafi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta wanke shi da maruka har biyu ba, Turaki kuma ya karɓi kulki a hannun police ya bata, ta dinga buga masa a fuska har sai da taga jini yana zuba ta hancinsa tukunna ta ƙyale shi tayi saurin fita daga ɗakin, in ba haka ba tsab zuciya zata iya sata ta rarumi duk abinda zai kai Amir Lahira ta buga masa.
Kaka na kallon Ummi tace,"Halimatu kinga duk inda Hamid yake yana nan hankalinsa na kanki da tunanin halin da kike ciki, fushin fa da kike da mahaifinsa ba zai fa shafe shi ba tunda ba shi yay miki laifi ba".
fuskar Ummi ta juye zuwa ɓacin rai tace,"Dada zan nemi Hamid amma ba yanzu ba, akwai lokacin da nake jira, dama in ace ma zan ƙara waiwayar gidan Hayyo to ace Auta na hannunsa ne, yanzu kuwa da bata wurinsa banga dalilin da zaisa in taka ƙafata a ƙofar gidansa saboda ina da wata ajiyar a gidansa ba, Hamid namiji ne baya buƙatata kamar yanda Auta ke buƙatata".
Kaka tace,"bafa zance ake na ki dawo da shi hannunki ba, kije ya ganki y