da taci, ƙari da kuma da kyan halinta, dan duk cikin yaransa mata tafi kowa haƙuri da biyayya da nuna ita ɗin ba ƴar kowa bace.
yana riƙe da hannunta ya nunfasa yace,"ya kamata ki koma gida haka Ilham, ba zai yiwu ki baro mijinki kizo ki tare anan ba, karki damu ko every weekend ne sai kizo kike ganinta kina komawa".
tai saurin cewa,"Dad ni ba zan koma ba sai Mami taji sauƙi".
yace,"a'a Ilham".
cikin kuka sosai tace,"to Dad ai shima yayi min uzuri tunda yasan wacce bata da lafiya, ni dai ba zan koma ba, Allah Dad ba zan iya zama a ko'ina ba yanzu in ba kusa da Mami ba".
Mai Martaba yay shiru bai ce komai ba, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗauko waya ya kira Turaki, yana ɗagawa daga ɓangaren Turaki cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya gaida shi. bayan sun gama gaisawa Mai Martaba yace da shi,"Muhammad babu damuwa dai ko idan Ilham ta zauna nan?".
Turaki yace,"ba damuwa Dad".
"ka tabbata Muhammad?, karka ce zaka yi kara ko kuma alkunya".
yace,"ko ɗaya Dad, ai abinda ya zama dole shi ake dubawa".
Mai Martaba yace,"to shikenan, Allah yayi muku albarka".
daga haka suka yi sallama. su kai shiru daga Ilham har Mai martaba kowa yana jin ransa ba daɗi, in ace suna da iko kwana ɗaya tal ba za'a ƙara ba Fulani Azima zata warke, to amma lamarin ba nasu bane na ubangiji ne, sai dai su roƙe shi ya warkar da ita ba tare da tayi doguwar jinya ba.
suna zaune kusan minti goma sai ga Sarauniya Mabruka wato matar Mai Martaba ta farko, ita da ƴaƴanta uku suna biye da ita tare da masu kula da su mutum uku. tun a washegarin ranar da Fulani Azima tai accident aka taho da ita Philippines domin ƙwararrun likitoci su dubata, dan Mai Martaba yana ganin kamar likitocin nigeria ba zasu iya ba, duk da cewar asibitin fada ma ba ƙanan likitoci bane acikinsa, kusan duk ɗinsu a ƙasar waje suka yi karatu, amma shi yafi ganin su taho nan ɗin.
kuma families da dama sun so su biyo bayansu Mai Martaba yace a'a su ɗan dakata tukunna, ita kanta Ilham sai da aka kwana biyar sannan suka taho ita da su Hajiya Shema'u da Turaki, kuma shi ranar da yazo ranar ya koma bai zauna ba.
kuma sai a yau da suka kwan 21days sannan mai martaba ya bar iyalinsa suka taho, don farko duk bai zaton za'aja haka ba, da zarar an mata aiki a ido shikenan zata dawo normal, to kuma likita sai yazo musu da bayanin duk da ya girgiza su. Sarauniya Mabruka ce ta fara sauka sauran biyun duk suna baya suma tare da nasu ƴaƴan. ta zauna kusa da Mai Martaba tana ɗago da Ilham daga jikinsa ta kwantar da ita a nata jikin, hadiman dake tare da ita suka watse suka tsaitsaya daga can gefe, Yarima Abbas da Yarima Lateef da Yarima Bilal suka zauna kusa da mahaifinsu ta ɗayan ɓarin.
Sarauniya Mabruka tace da Mai Martaba,"ya jikin nata?".
idonsa na tsaye ƙyam akan wata ƙofa cike da nazari a bisa faruwar accident ɗin ya bata amsa da cewar,"da sauƙi irin na malam bahaushe, zuwa anjima zasu ƙara shiga da ita theater za'aiwa ɗaya idon aiki, shima tana kukan bata gani da shi sosai, sai maƙogaronta da akai hoto akaga still akwai glasses na mota da suka farfashe mata aciki".
"Allah ya sauƙe ya bata lafiya don nabiyyurrahmati". ta faɗa tana saka hannu ta goge hawayen da ya sauko mata. lamarin duk yasa jikinsu mutuwa, sosai suke tausayin Fulani Azima domin ita ɗin mutum ce a garesu, duk wanda zai buɗi baki ya faɗi aibutunta to sai dai idan maƙiyinta ko kuma wanda basa shiri.
duk cikin su huɗun ita ɗaya ce babu ruwanta a yanda take nuna musu, ko irin kishin nan ma na rashin haihuwar ɗa namiji ita bata yi sam bata ɗaga hankalinta ba, hasalima kama nasu ƴaƴan take kamar nata, nan kuwa duk basu san tana bi musu ta ƙarƙashin ƙasa ba ne, fir'auna ce a zuciya Allah a fili.
suka miƙe gaba ɗayansu suka wuce zuwa room ɗin da take, duk me cikakken imani kallo ɗaya zai yiwa Fulani Azima yaji saukar hawaye a fuskarsa, kwance take kan gadon kana kallon idonta na dama zaka san bata gani da shi kwatakwata, sai kallon kowa take yi da ɗayan shima kuma dusudusu take gani, ga karaya a hannayenta duka biyun banda ta ƙafarta guda ɗaya, kallon kowa kawai take tana hawaye masu zafi.
ita so take ma tayi magana amma ta kasa, tun washegarin ranar da abun ya faru taso ta buɗi baki ta nemi yafiyar Hajiya Ramla a sanda suka je dubata, amma tayi tayi tai magana sam ta kasa, ga shi duk ta yanda taso tayi wata alama da zaisa a fahimci tana so tayi magana da Hajiya Ramla ta kasa, kuma daga yanda taga fuskokin familyn Dikko tasan ko kusa Hajiya Ramla bata tona mata asiri ba, akwai tabbas ɗin bata faɗawa kowa komai ba, wanda hakan ya ƙara haifar da danasani da kuma dama nadama a tare da ita, tana ji tana gani ko da bata mutu ba tata rayuwar dai ta ƙare, ita da matacce marabarsu numfashi kawai, babu abinda take biɗa a yanzu sama da ta kalli Hajiya Ramla a gabanta ta nemi yafiyarta, sannan taga Jakadiyya da Drivern da ta kashe suma tace su yafe mata, to amma ba zata samu duka wannan damar ba, haka zata tafi lahira da tarin zunubi da kuma hakkin