NOVEL SHARES -
maganar ransa a ɓace.
Inna Wuro na jinsa tace,"nima halina yaja min na shegen shishshigi da ƙwala kai a faranti, in ban damu da ɗaukar ƴarka ba ai baka zagar min iyaye har haka ba Yusuhu, iyayen da sun jima a ƙasa, tunda suka mutu babu uban da ya taɓa buɗe ƙazamin bakinsa yay musu irin wannan ƙazamin zagin sai kai Yusuhu, kamar bani na haifi ubanka ba?, amma babu komai Allah yana ji kuma yana gani, ranar gobe ya bi min hakkina. ƴarka kuma ni da ɗaukarta har abada, kai kallonta ma ba zan ƙarayi ba indai na cika ƴar halas, shegen banza kawai da yayo kama da dangin uwassa duk munana".
tai gaba tana goge hawaye da gefen zani. "Amadu zo mu tafi kafin jinina ya hau".
tafiyarsu ba jimawa su Hajiya Madina ma suka fito, da su da su Kaka aka kwashesu duka a sienna har biyu. cikin dare ne amma kace tsakar rana saboda yanda suke ta hanyaniya a mota. dan lokacin har an kira Granny a waya vedio call, itama duk wannan fushin da take yi sai ta manta da shi, tana ganin Mum ta fashe da kukan farin ciki, tana faɗin gobe-gobe zata taho, yanzu Adil zai je ya yanko mata ticket.
taraddadin Hajiya Madina ɗaya ne su kuma Baffa ya lanƙwashe.
kuma suna gab da isa gida Baffa ya kira wayar Hajiya Madina yake shaida mata cewar,"Fulani Azima tayi mummunan accident, su wuce masarauta kawai ba sai sun koma gida ba".
*Vote, Comment and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*38*
*Massachusetts General Hospital, Philippines.*
acikin silent ward ɗin babu abinda kake ji yana tashi sai sautin kuka me ban tausayi. wata tsohuwa baƙa na sanye cikin les me tsada milk colour, ta baro inda take tsaye ta dawo kusa da Ilham ta zauna. ta janyota zuwa jikinta cikin sigar lallashi da ban haƙuri tace da ita,"Ilham wannan kukan naki da kika shafe kusan awa guda kina yinsa ba shine zai bawa Mahaifiyarki lafiya ba, saboda haka ki sha re hawayenki ki mata adu'a dan ita tafi buƙata a halin yanzu".
maimakon Ilham ta daina kukan sai sabo ya ƙaru fiye da wanda take yi, kuma Kakar tata Hajiya Shema'u wacce take mahaifiya wurin Azima bata ƙara ce mata komai ba, sai bubbuga bayanta da take cike da matsanancin tausayin Ilham ɗin.
a lokacinne kuma Ahlan ya iso wajen, ƙani ne a wurin Azima daga ita sai shi. ya zauna akan kujerar kusa da mahaifiyarsa, shima da ka kalla fuskarsa zaka hangi damuwa acikinta.
yace da ita,"Umma me likitan ya ƙara cewa?".
ta sauke numfashi ruwa na kawowa cikin idonta tace,"tou Me Martaba dai ya tafi wajensa tun bayan da suka fito da ita daga theater room ɗin, ban san yanzu kuma ya ake ciki ba".
Ahlan ya sauke numfashi sannan yace,"nima jiya muna tare da jami'an tsaron da suke ta bincike akan accident ɗin nata, kuma har yanzu fa Umma babu labarin driver'n da suka fita tare. anje wurin iyalinsa su kansu sunce satin biyun nan cif ba su saka shi a idonsu ba nemansa suke, itama kuma jakadiyar tata fa har yau ba labarinta".
da damuwa sosai Hajiya Shema'u tace,"to Allah masanin abinda ya faru, kuma ni gani nake idan lamari ne na ƴan garkuwa ai ita zasu ɗauke ba drivern ko Jakadiyar ba, kuma idan kidnappers ɗinne da tuni sun kira waya, amma koma mene dai mun barwa Allah, fatanmu Allah ya tashi kafaɗunta".
sai kuma ta fashe da kuka sosai tana cewa,"da banyi niyyar faɗa muku ba saboda kar hankalinku ya tashi, sai dai faɗar ya zama dole ko don a tayata da adu'a. likita yace ta kamu da paralyse, ɓarin damanta ya mutu ya gama aiki Ahlan, idonta guda ɗaya ma shima ya mutu wai ruwan ciki ya tsiyaye gaba ɗaya, ƙafar hagun ma yanzu suna bayanin yanketa za'ai, Azima dai na cikin wani hali Ahlan, wannan yarinya sai dai Allah yay mata sakayya da wanda ya zama silar shigarta wannan hali".
sosai take kuka sanda take maganar, wanda hakan ya ƙara tsawaita kukan Ilham.
Ahlan a razane yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, paralyse Umma?, yanke ƙafa?, rasa ido ɗaya?, kai rayuwa kenan kowanne bawa da kalar ƙaddararsa, ita kuma Yaya ga ta yanda tata tazo mata. hasbunallahu wani'imal wakil".
shima bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, tausayin ƴar'uwar tasa yay matuƙar kama shi.
Mai Martaba ya ƙaraso wajen jikinsa a mace, yana zuwa Ilham ta taso a jikin Hajiya Shema'u ta tafi ta faɗa jikinsa. ya rumtse idonsa sosai saboda tsananin tausayinta, ya kalli su Hajiya yace,"Dr yace kuna iya shiga wajenta". da sauri kuwa suka miƙe suka nufi wani dogon corridor hanyar da zai sadaka da room ɗin da aka kwantar da Fulani Azima.
Mai Martaba ya zauna akan kujerar da suka tashi, ya kwantar da kan Ilham a cinyarsa, yay dauriya da dakiyar maganar da yake jin kamar da kuka a cikinta. yace,"kina so Maminki ta sami lafiya?".
tai saurin ɗaga masa kai, yace,"to adu'a za ki mata ba kuka ba, indai kina kuka ba zata sami lafiya ba, kinga dai a halin da take ciki, halin da ko maƙiyinka ba zaka yi masa fatan ya shiga ba".
ta ɗago daga cinyar tasa, yasa hannu yana goge mata hawaye, wani na kuma bin wanda yake gogewar.
duk cikinsa ƴaƴa mata yafi son Ilham saboda sunan mahaifiyarsa