NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 323

an haƙoransa a waje yake faɗa mata cewar,"da asubar nan fa ko lazimi bata gama ba take mitan Allah kaimu safiya ta bar gidan ita ba zata iya da gorin da akeyi mata ba". Hajiya Madina ma tai dariya sosai, lokacin kuma hankalinsu ya karkata kan yaransu dake shigowa parlon bakunansu ɗauke da sallama. Shigar jikinsu kaɗai zata shaida maka ƴaƴan wani ƙusan ne, ballanta azo ga kallon fatar jiki da zata tabbatar maka da hutu, jin daɗi da gata ya zauna. Baffa ne ke amsa sallamar tasu yana miƙewa zaune daga kishingiɗar da yay ajikin tumtum. Samha, Zaytuna da Nihal suka zube a gabansa, cike da tsantsar girmama da ladabi suka gaishe shi cikin taushin murya. ba sai an faɗa ba, irin zaman ma da sukai a gabansa shi zai baka tabbacin an gina tarbiyarsu bisa bigere na addini, duk da Judge Dikko ɗan boko ne hakan bai sa yay watsi da koyarwar addini da al'ada ta fulani ba ya ɗauki ɗabi'ar bature ya gina iyalinsa akai. Idanuwansa na bin kowacce da kallon so da ƙauna dake tsakanin uba da ɗansa yake amsa musu cikin farin ciki da annashuwa. Adu'a yake jero musu iya adu'a su kuma suna amsawa da amin, Zaytuna wadda ke da idon hawaye tuni idanuwanta suka ciko da ƙwalla, haka ma muryarta tayi rauni wajen amsa albarkar da mahaifinsu ke saka musu. Da yake shi mutum ne me barkwanci acikin iyalinsa ya kalla Nihal cike da zolaya yace,"Auta ya naga kinyi fari har kinfi Boɗejo, saura ƙiris ki koma Zabiya". Babu shiri Nihal tai dariyar da duka haƙoranta suka bayyana a waje tana rufe bakinta da hannu. Baffa ya ƙara cewa,"ki sammawa Mamanki abinda kike shafawa ko ta ƙara yin kyau ta koma ƴan mata". Yay maganar cike da barkwanci. bata bar dariya ba tace,"Baffa ni babu abinda nake shafawa tsabagen hutu ne kawai". Yay murmushi, Hajiya Madina tace,"yo Allah na tuba ni wa zai ganni ma yace na ajiye maka waɗannan yaran...ni jikina ma ai yafi na wata budurwar, man bature kuwa ai sai dai mu barwa wasu danmu da namu farin Allah ya halitto mu". acikin amon yanda tayi maganar zaka tsinci tsagoron kishi duk da cewar maganar anyita ne for raha becouse of ayi dariya. "Zaytuna naga hannun naki". Hajiya Madina tace tana duban inda Zaytuna ke zaune, gefen mahaifinta tamkar zata shige cikinsa. ta taso ta dawo kusa da ita tana nuna ma ta hannun. "ya fara sauƙi ai...da zafi har yanzu?". "ehh Maama yana zafi". "sannu, did you take your drugs?". Tace,"ehhh". "Allah ya sauƙe". Baffa yace,"to wai ba za'a nemo wata ƴar aikin bane?, kuma ke har kina shirmen me da kika bari ruwan zafi ya taɓa ki". Hajiya Madina tace,"tsautsayi dai da baya wuce ranarsa, ita kasan kamar inji ba son zama take yi ba tai aiki ba ko masu aikin suna nan...amma idan yau Jamilar bata dawo ba sai nayi magana da Yami ta samo wata, ai dama sati ɗaya Jamilar tace zata yi". Sahma tace,"ai Maama a nemi wata kawai, dan bana tunanin Jamila zata dawo, don naji Sha'awanatu na cewa kamar aurenta za'ai". "ai da hakanne zata faɗa, ko ta kira waya ta sanar". Baffa na riƙe da hannun Zaytuna yake cewa da ita,"please Babyn Baffa a daina shiga kitchen kinji, bana so wani abu ya dinga taɓa min lafiyarku". Sameer da suka shigo shi da Khalil yace,"to wai a yanke hannun mana". Zaytun tayi masa wani kallo tace,"sai kazo ka yanke ai". yace,"karki bari a barmu daga ni sai ke a gidan nan kiga aiki da cikawa". Baffa with full of smile on his face yace,"ƙyale shi haushi yake ji hannunki yafi na budurwarsa kyau, kuma nan gani nan bari...". tun bai ƙarasa ba Samha da Nihal da ita Zaytunan suka ƙarashe faɗin,"ɗumamen mayya ba". sukai maganar suna dariya. Sun ɗau tsawon lokaci suna hira kafin yaran su tashi su tafi, suna fita Baffa ya kamo hannun matarsa yana cewa,"haba ƴar shawalwalata ɓata fuskan kuma na menene?". Bai jira me zata ce ba yaci gaba,"kema dai ai kin san waɗannan idanun tsufan nawa kallon jaririya ma suke miki ba ma budurwa ba, me za'ai da wata ƴan mata ina dake ƴar shila, kin fa riga kin rufe ƙofar tuntuni, to mene kuma wani batu zai sa ki ɓata fuska ummm Babyn Baby, please saki ran karki ɓatan kwalliyan da akayi mani nake kallo ina jin daɗi". ya ƙarasa maganar yana shafo fuskarta ita kuma tana ƙoƙarin danne murmushin jin daɗin dake neman suɓuce mata, yanda yake yi mata kamar ƙaramar wata yarinya, har sai da yayi nasarar sakata yin murmushin daya haɗe da dariya. "yauwa ko ke fa gimbiyata, sarauniya a fadar zuciyata, ina sonki fa, ina sonki da yawa wallahi...kai Allah dai ya ƙara miki kyau". Ya faɗa yana kamo dogon hancinta. sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"wai yaushe zamu ƙara tafiya honey moon ne?". Hajiya Madina tace,"da gaske fa nai zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne". Yace,"waa nii rufani ki saya". Yana nuna idanuwansa yace,"ai wannan idanuwan babu abunda suke gani sai ke, ke ɗaya tallin tal Aina'u ta Habibullahi". "to yanzu tashi mu koma ɗaki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba...nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar ku
🏠