NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 179 of 323

tun ɗazu suna ɗan jiyo hayaniyar, kan kace me wannan wuri ya ƙara ɗinkewa da mutane kamar cinema, Inna Wuro ta rasa wajen ratsawa ta wuce sai ta tsaya daga gefe ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da tasa a lokaci ɗaya akayo kanta. kamin a rufeta tayi saurin jan kujerarta tabi ta gefe ta wuce ta samu wurin da zata bawa idonta hakkinsa, ta zauna tana ɗaga kai sai kalle-kalle take tana kiran,"ƙawayena masu farin kaya dana gayyato kuna ina?, gani anan tsakiya idan kun jini ku ɗaga hannu in zo in shigo da ku, ga sarauniyar aljanun nan duk an rungumeta ku hasko waya ku ɗaukarwa duniya". wani takaici ya turnuƙe Dr Yusuf, ya dinga kallonta yana jin kamar ya kai mata duka, Aliyu da ya dawo hayyacinsa ya ɓata rai yazo yana ce mata,"wai ke dan Allah mene haka?, jifa yanda kika tarowa mutane jama'a, ke ko ina akaje sai kin yarfa mutane, kinga tashi kawai mu tafi gida kamin ki gama ɓararwa da Daddy mutunci". ko kallonsa bata yi ba tasa hannu tana turesa gefe. "yo Aliyu tunda dai ba naka mutuncin zan ɓarar ba me kuma ya shafeka". ganin yaƙi matsawa ta zabga salati tana nuna masa can gefe da cewar,"mun shiga uku ga Zainabu can ta yanke jiki zata faɗi". Aliyu yay hanzarin matsawa yana wurga idanuwa, ta kallesa tai dariya tace,"ɗan ƙwal uba addababbe". ta buɗe idanuwa duka tana ƙara kallon su Hajiya Madina da su Kaka waɗanda a yanzu suka haɗe wuri ɗaya, waje ya zama kamar gidan biki, Hajiya Madina na rungume da Fillo tana cewa,"tabbas ke ɗin alkhairi ce, kin zama haske a cikin rayuwarmu tunda kika kusance mu, insha'Allahu nayi ɗamarar faranta miki Fillo har ƙarshen rayuwata". Daddy ya ƙaraso inda Inna Wuro take zaune tayi ƙyam da ido a waje ɗaya tana ta aikin kallon bidirin da har yanzu bata fahimci kansa ba ma. in zaka yanka wuyanta ba zata ce ga abu ɗaya da taji an faɗa ba tun ɗazu, balle tace maka ga akan ainihin abinda yasa ake wannan murna, ita dai abu ɗaya ta barwa kanta dukansu aljanu ne kuma uban Aliyu suka zo ci. Daddy ya rissina yace,"mu tafi gida Inna dare yayi sosai, ƙarfe uku har da rabi, alhamdulillah yarinyar ta samu sauƙi dan Yusuf ma yace gida zasu wuce". ta kallesa tace,"to su kuma waɗancan da suka cunkushe waje ɗaya tafiya zamu yi mu barsu bamu gama kallonsu ba?". Daddy yace,"ai yanzu su ma zasu tafi". tace,"kai Amadu bana son halin Aliyu a tare da kai, ni kawai kayi tafiyarka ku ƙyaleni anan idan an gama na biyo motar haya, haka kawai yaran can da basu sami zuwa ba su rasa me basu labarin irin aratabun faɗan da aka sha, kai kasan halin ƴarka Yusra da gulma bata ƙi ta zageni tass ba akan ban kai musu rahota ba, ta dinƙa ɗaga min murya tana me amfanin zuwana wajen, to gwara ka barni in samu na kai musu, ni ƙafar Aliyun ma banga ta yanda aka shanyeta ba, yanzu dai ɗau wayarka kawai ka kayi musu hoton vedio me motsi sai akaiwa sauran ƴan gidan da basu ga tashin hankalin da akai ba". Daddy yace,"wayata na barta can gida kinga a halin da aka taho ai". tayi shiru dai bata ce masa komai ba, dai-dai da ƙarasowar Nuratu wajen tace,"Inna Wuro ashe matar da muka riƙe a wajenmu babar yarinyar da Aliyu ya buge ce, shekaru da yawa basu haɗu ba sai yau Allah ya haɗa fuskokinsu". Inna Wuro ta daki ƙirji ta dafe, babu shiri ta miƙe da sauri tana cewa Daddy,"tarkata yanamu yanamu mu wuce Amadu, daga nan kai tsaye Kano zamu wuce wuce ko gida ba zamu koma ba, gwara muje wurin Malam Ahmad Sulaiman ya haɗo mana turaruka azo ake bankawa juna, ina dalili haka irin wannan ibtila'i na rainon Aljanu, to Allah yasa dai bata shiga jikin wannan ƴa Farha ba". Daddy dai yay shiru, tashin hankalinsa ɗaya ta botsare tace sai anyi kano a tsakiyar daren nan, dan aka ƙi zuwa shi abin zai zamewa tashin hankali ta dinga kuka kenan tana ita ya biyata nononta da yasha kawai sai ta san nayi. Inna Wuro ta dinƙa bi tana cewa mutane ahalin Amadu Alfindiki kuna ina, mutane kuzo mu tafi gida ƙarfe uku ta dare tayi. Ammi tace mata,"Inna kiyi musu sallama, ki ɗan ƙara basu haƙuri sai mu wuce". ta daki cinya ta riƙe baki tace,"niiii, ba dani ba wallahi, akan me in bada haƙuri bani na kashe musu ƴa ba, ke dai da ya zamar miki dole da fitinannan ɗanki yaja miki masifa". har sai da suka je bakin mota sannan aka kula da babu wanda ke riƙe da Farha, Nuratu tace,"Inna wa kika bawa ita?". Inna Wuro ta fashe da kuka tana faɗin,"na shiga ukuna, wallahi ban san wanda ya amsheta ba, a hannuna fa take ƴar nan ban san garin ya ta bar hannun nawa ba, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, to aini sai yanzu ma na kula babu abu a hannuna, to dama abu ka ɗauka kamar baka ɗauka ba, Amadu kira Malam Ahmad ya buga mana istikara ko aga hannun wanda ta faɗa". tana yin shiru sai ga Yusuf nan ya fito ɗauke da Farha, ya wuce ta gabanta ko kallonta baiyi ba ya miƙawa Nuratu ita yace,"karki ƙara bawa tsohuwar can ƴata tunda ba'a kasuwa naje na siyota ba, ke ma kuma ba buɗe ido kika yi kika ga an ajiye miki ita kusa dake ba, sai da kika sha baƙar wuya kafin samunta". yay
🏠