NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 178 of 323

u wajen zama tunda naga abin bana tsayuwa ba ne". Nurse ɗaya ta taso tana cewa,"Hajiya kawo Babyn". ɗayar kuma da mamaki tace,"film kuma Hajiya! a asibitin?". Inna Wuro ta gyara zaman mayafi tana riƙe Farha da kyau tace,"a'a babu zancen wani in kawo Baby, sunanta Farha ba Baby ba, kuma yanzu ina ni ina baki jaririya alhalin ban sanki ba?, inje ki cuceta in shiga uku, to wallah uwarta a kotu take yin aiki tsab sai ta iya sawa a ɗaure ni ba mutunci ne da ita ba, a hannuna ta san ƴarta haka kawai in baki ki yiwa ƴar allurar tetanus ki jamin jafa'i, yo banda ma tana can tana kallon Film ina zata bar min ita, ai basa bani ita nima kuma bana karɓa saboda sunan Zainabu Yusuf ya saka mata, ummm wai ko dai sunan uwarsa yasa bacin yasan Uwar ba mutumiyar ƙwarai bace, Allah yasa ma dai kar ƴar ta yo gadon hali, dan naga irin goshinta iri ɗaya dana Zainabun". Nurse ɗin tai murmushi kawai. Inna Wuro tace,"yanzu dai ɗaukar min kujerar muje, ko kuma sai an biya kuɗin ɗaukar ne?". Nurse ɗin tai ƴar dariya tace,"a'a Mama, kula daku ai aikinmu ne, muje". ta faɗa tana ɗaukar kujerar. Inna Wuro tace,"a'a in ma kince sai an biyaki ai sai a biyaki, albashin da ake baku dudu nawa yake, kuɗin fa abincin rana ɗaya ne da Amadu yake kashe mana, muje wallahi sai in sa ya baki wani abin ai ɗana yana da kuɗi, shisa ma kaf nabi Malaman duniya nace suke masa adu'a kar a sawa kuɗin ido su ƙare da wuri mu shiga uku mu gantale acikin ɗumamen safe, shayi kuma ba madara balle isassan sikari". Nurse ɗin tayi gaba tana ƙunshe dariyarta, Inna Wuro na lura da hakan tace,"a'a wallahi dawo ki ajiye in ɗauka da kaina, sam bana haɗa hanya da ƴan banza irinku, shisa kaf ƴaƴan Amadu da Kursum ce bama shiri saboda irin wannan munafukar dariyar, sai inyi magana a wani ƙunshe dariya saboda ga taɓaɓɓa na magana ko?, to Allah ya isar min dan ba yafe miki zan ba, yanzu tsakani da Allah wani yazo wucewa ya gani ai sai yace min sannu, to sannu ina lafiya ƙalau ai zagi ne da cin mutumci, gaskiya ajiye kujerarki bana so na ɗauka da kaina, dama ku yaran asibitin nan duk ƴan banza ne sam baku da mutumci wallahi, kullum sai mutane sun kai ƙararku radiyo tsabar ba kwa so ku gama da duniya lafiya, to wallahi ni babu ruwana a lahira kuna kallo zan yi gaba in shige aljannah salin alin ku kam kuna baya ana ramawa talakawa abinda ku kayi musu". Nurse ɗin tace,"yi haƙuri Mama bada ke nake ba". Inna Wuro ta haɗe rai tayi mata wani kallo tace,"wato ke harda halin ƙarya irin na Aliyu kina da shi kenan, ina ganinki da idona kina ce min bada ni kike ba, to kawai na barwa Allah abar zancen bana son sabuwar fitina bacin wadda nake ciki". tasa ƙafa tayi fatali da kujerar, ta nemi wata ta ɗauka tayi gaba sai masifa take yi. sai da zata bar wajen kuma sai ta dawo murya ƙasa-ƙasa tace,"ba zaku zo kallon ba ne?, ai ko dai zaku yiwa kanku dan zaku rasa na ɗorarwa, kunga yanda jama'a suka cika wajen akayi maƙil da ƙyar ake numfashi, to dai za'ai babu ku wallahi indai baku zo ba dan faɗan aljanu da mutane ne, ɗana Aliyu ne ya kashe musu ƴarsu suka zo cin Uwassa Zainabu, ni dai du Allah kuzo ina gayyatarku kallo, ku taho da kujeru kuma ku sami na takawa dan anyiwa wajen rumfa nima sai na taka zan hango abinda ke faruwa, dan baku ga yacce suka zo da makamai suka yiwa wajen ƙawayen ba, ni yanzu so nake ma suce ba akan Aliyu zasu ɗau fansar ba akan Zainabu zasu ɗauka, ni dai da nayi sati ban bacci ba saboda tsabagen murna". jiyo tashin hayaniya ta tafi da sauri,"kai kai kai na tafi kar ayi babu ni, kar a shanye ƙafar Aliyu banga ta yanda akayi ba in kasa bada labari". Nurses ɗin na dariya suka biyo bayanta da sauri suma, ita dai sai jan kujera take tana ɗaga ƙafarta me ciwo da ƙyar, ɗayar nurse ɗin ta dage sai da Inna Wuro ta tsaya ta bata Farha, ta bata ita tana cewa,"ni da ace da jakar goyo ma sai ku ara min in sakata aciki kar inje tashin hankali yay tashin hankali nayi ta kaina in yasar musu da ƴa a wajen ban sani ba". suka gimtse dariyarsu Nurse Raliya tace,"zan riƙe miki ita Mama". tace,"aiko dai Allah rabaki da sharrin zaurawa ya haɗaki da saurayi me irin zuciyar ɗana Amadu, ya rabaki da sharrin samarin zamani masu munin hali irin na Aliyu". ta amsa da amin. tana tafe sai faman sauri take tana cewa nurses ɗin,"amma fa kuyi shiri ku riƙe takalmanku a hannu dan da zarar an fara sare-sare ta kaina zanyi in barku, dan ba zan tuna ma ni na gayyatoku ba, ku taho da sauri dai kar ayi a gama babu mu". kuma duk bakin room ɗin da Inna Wuro tazo wucewa sai ta leƙa tace,"jama'a ku fito ana faɗan aljanu da mutane ana can ana faman shanye ƙafafu, dan Allah ku fito jama'a ku taimaka mana kar a kashe jikana Aliyu, wayyo na Annabi ku taimaka jikana yana cikin masifa ya kashe ƴar aljanu, ku kawo mana ɗauki dan Allah, jama'a da yawa sun taru an rasa yanda za'ai da su kowa yabi su da kallo ana zazzare ido". jin wannan yasa mutane aka dinƙa fitowa ana ta faɗin subhanallah da innalillahi, dama
🏠