laifin komai ba Babana. ni ce nayi muku laifi wanda har ba zan yafewa kaina ba sai in kun yafe min, dan Allah, dan Annabi Babana kai da Zaytuna ina baku haƙuri, ina roƙonku ku yafe min da nisanta daga gareku da nayi, sharrin shaiɗan ne".
Zaytuna ta fashe da kuka tana shigewa jikin Mum ɗin sosai, cikin muryar kuka suka haɗe baki ita da Turaki suka ce,"Mum ke fa Uwa ce akan me za kike neman yafiyarmu bayan baki yi mana komai ba. to ma idan kinyi ɗin menene ai girmanki ne da cancantarki, balle ma har duniya ta naɗe ba za ki taɓa yi mana abinda zamu kallesa a matsayin kin mana laifi ba".
furucin nasu sai ya zama kamar haɗin baki ko kuma tun can dama sun tsara hakan. sukai shiru suna barin jikinta, Turaki yasa hannunsa na hagu a gefen fuskarta ta ɓarin da yake, itama Zaytuna haka.
suka ƙara haɗa baki da faɗin,"muna miki tsananin so, farin cikinki shi ne muce mun yafe ko?, to mun yafe miki Jarumar mata".
sukai kissing nata a goshi suna jin wani irin shauƙi na daban da basu taɓa jinsa ba mara misaltuwa na bin jinin jikinsu.
gaba ɗayansu kuma har Mum ɗin sai suka saki murmushi me faɗi, har haƙoransu duka na bayyana a waje. Hajiya Madina da su Neehal sai suka koma ƴan kallo, dukkansu sai murmushi suke yi, kuma har sannan Hajiya Madina bata bari Baffa ya sani ba saboda sanin irin fushin da yake da Hajiya Ramla, ta bari ne kawai sai dai ya gansu a gida.
Zaytuna taƙi sakin mahaifiyartata tace,"Mum yau a jikinki nake so na kwana, yau ba zanyi bacci ba Mum zan zauna inta kallonki".
suka riƙo hannunta ta miƙe ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ne ta kalli Hajiya Madina da zolaya tace,"Madam kisa ƴaƴanki su sakeni in tafi wurin sabuwar ƴar da nayi".
aiko karaf Neehal tace,"ki tafi ina Mum?". ta faɗa tana turo baki tai saurin zagayowa ta zauna kusa da ita tana kama hannunta da cewar,"ai mu daga yau kina manne wajenmu kuma".
bata bar murmushi ba tace,"to zanje in duba patients ɗina, a ban izini dan Allah". Kusan duk a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"patient kuma Mum?".
tana kallon Hajiya Madina tace,"wata yarinya ce da ta taimaka min muka fito daga cikin jeji mota ta bigeta, tun ɗazu munfi 1hour amma shiru, tace min ƴar aikin gidanmu ce, dan tunda ta ganni ma take cewa muna kama da Zaytun".
a lokacinne kuma sai ga Fillo nan tazo wajen kamar tasan zancenta akeyi, tana riƙe da hannun Ummi ta ƙaraso da kumburarriyar fuskarta da taƙi barin murmushi. ta saki hannun Ummi ta nufi wajen Hajiya Madina wacca ta buɗe mata hannu, ta shige jikin Hajiya Madina ita kuma tana rungumeta tare da faɗin,"hasken gidan Alƙali Dikko, haƙiƙa ke ɗin haske ce a tare damu Fillo".
Fillo tace,"Maama nima ga Ummina na gani, ashe bata mutu ba". ta saketa tana faɗin,"haba dai". tabi Ummi da kallo kafin ta isa wajenta da sauri tana gaisheta suna yiwa juna barka da farin cikin da suka tsinci kansu a ranar yau.
Turaki dai sai yabi Fillo da kallo, ba wai ya manta da ita bane, tun ɗazu hankalinsa na kanta, kawai dai ba zai iya barin Mum bane, amma Allah Allah yake yaga Dr Yusuf yazo wajen. ji yake kamar yaje ya sunkuceta ya ɗauketa ya kaita inda zai zama daga shi sai ita, silent place ɗin da ba za'aji sautin komai ba sai na dariyarta, dan tabbas zai ƙara yalwata wannan annurin da yake gani shimfiɗe a saman fuskarta. zai ajiyeta akan cinyarsa yayi mata godiya da irin salon da ba'a taɓa yiwa wani mahaluƙi shi ba duk girman matsayinsa da mulkinsa kuwa.
Mum ta dubeta tace,"zo nan ƴata". Fillo ta isa wurinta zata tsuguna tace,"a'a zo nan". ta faɗa tana yi mata nuni da kusa da ita, yayinda take kallon Turaki tana cewa,"Babana matsa".
Turaki ya matsa Fillo ta zauna, Mum na kama fuskarta tace,"how are you feeling now dear?, ina ke miki ciwo?". tace,"feeling much better Mum". ta faɗa da ƙyar saboda yacca take jin babban yatsan Turaki na ƙafarsa na yawo akan ƙafarta. ga shi yana matso da fuskarsa saitin kunnenta kamar baya ganin kowa da komai a wajen, ita al'amarunsa tukun before yay tafi sun fara bata tsoro, kuma kawai sai ji tayi ya ratso da hannunsa ta baya ya matsa cikinta, ta ɗanyi zillo tana jin kamar ta fashe da kuka.
a hankali ta yanda ko kaɗan Mum ba zata ji ba balle ta gane yace,"tanks immeasurably".
ta ɗan kallesa kaɗan ta ɗauke idonta. a sannanne suka jiyo guɗa ta karaɗe cikin asibitin, Boɗejo ce ta taho sai rawa takeyi, take kuma wuri ya ƙara kacemewa da murna.
Inna Wuro dai na gefe da sakakken baki cikin ranta tana faɗin ashe haka aljanu ma suke da haɗin kai. daga bige musu ƴa har sunyi cincirindo haka da wannan uban daren, sai dai babu hankali sam dan taga kamar murna suke yi.
ta ratsa ta gefen su Kaka da suke tsatstsaye da ƴan gidan su Yusuf, ta tafi da sauri zuwa reception, ta sami wasu nurses su huɗu a zaune suna hira, tayi musu sallama suka gaida ita.
tace,"ku ana can anata haska film kunan zaune da farin kaya kamar sabababbin gawa, a'a to ni dai da kuka ganni kujerar zama nazo ɗauka. wata ƴar arziƙin tazo ta kai min kujera dan Allah in sam