ni da fuskar mutanen ƙwarai?, Allah ya tawarwatsa rayuwar mutane irinsa a duk inda suke, adu'ata ɗaya Allah yasa bai lalata miki rayuwa ba".
Fillo ta zame daga jikinta, tasa hannu ta goge hawayenta tace,"bai ida mugun nufinsa ba Allah yaɓullo min da hanyar guduwa, Kaka bana son kukanki dan Allah ki daina, ki manta da zaluncin da Amir yay mana ki barsa da Allah, indai duniya ce ga shi gata nan, yau ba ranar kukan baƙin ciki ba ce ranar kukan farin ciki ne, irin wannan hawayen nawa nake so kiyi ba irin wanda nayi a sanda na san cewar Amir Birin da ya lulluɓe kansa da mayafin da ba mai iya ɓata shi bane. Ummi ta dawo Kaka, Allah ya bayyana mana ita, dan haka ki kalla gabas ki yiwa jalla wa'azza godiya".
Kaka bata bar kukan ba tace,"ke wai kina hauka ne, a ina kika ga wata Ummi?".
Ummi dake riƙe da Kaka ta gefe ta kwanto a kafaɗarta tace,"gani Dada".
"Halimatu". Kakan ta kira Ummi da mamaki matuƙa. "na'am Dada". sai Kaka ta rungumeta tana hawayen farin ciki itama,"Halimatu ina kika je?, dama kina raye Halimatu?, ƴata na yafe miki domin nasan ba komai ya saki barin gida ba sai baƙin cikin mugun miji, amma tsayin wannan lokaci ina kika shiga Halimatu har na ganki haka lafiya ƙalau?, kai Allah maji roƙon bayinsa".
Ummi tace,"tashin farko Kawu Nasir ne ya bani goyon baya harma ya ɓoye ni a gidansa, daga nan labarin da yawa, amma waɗan can mutanen da kike gani ɗansu ne ya tsince a sanda na faɗa cikin wani hali, kusan shekara yanzu suke bani duk wata kalar kulawa".
nan da nan kuma duka Families biyu sai suka manta da damuwar da ake ciki, a shiga babin farin ciki. dan kamar yanda su Hajiya Madina suka mance da lamarin su Fillo haka suma su Kaka suka manta da lamarinsu, dan suma waje suka samu suka zauna, Kaka sai kwarara adu'a take yi da godiya ga su Yusuf, tunda Ummi ta shiga faɗa mata irin alkhairan da suka yi mata.
da ƙyar iyalan Dikko suka safafawa Hajiya Ramla suka bar jikinta, ta bisu da kallo tana cewa Hajiya Madina,"ranki ya daɗe yanzu duka waɗannan yaranmu ne?, har waɗannan samarin?". ta faɗa tana nuna Khalil da Sameer.
Hajiya Madina tace,"ƙwarai kuwa". nan da nan ta shiga nuna mata su Nihal tana faɗa mata sunayensu, tai mata nuni da Ilham dake gefe ɗaya ta rakuɓe sai kallonsu take tana murmushi.
tace,"ga inlaw ɗinmu can". Mum tace,"really?". Maama tace,"ga zahiri na kunya nan kina gani". ai nan da ko Mum ta buɗe mata hannu tace ta taho gareta, ta rungumeta da tsananin farinciki sai saka mata albarka take yi.
kuma sai a lokacin Mama ta lura da rashin Zaytuna, sai ta miƙe tana dube dube dan dama tuni ta san da ƙullatar da Zaytuna tayi da Mum.
ta ganta tsaye can gefe ta haɗe rai fuskarta a gefe ɗaya, ranta ya ɓaci sosai taji tama kasa magana, hakan ne yasa Hajiya Ramla fahimtar komai musamman da ta ɗaga ido ta kalli photocopy ɗinta, ba sai an faɗa mata ba ai tana kallonta tasan itace jaririyarta da ta tafi ta bari.
Turaki ma ya dinƙa kallon Zaytuna yana tuna lokuta da dama da take ce masa,"ka daina damuwa da ita Hammah tunda ai itama bata damu da mu, ni fa Hammah Allah ko ace ta dawo inda take ba zan kalla ba balle na raɓeta".
sai kawai ya miƙe ya nufi wajenta, yana jin Maama cikin muryar ɓacin rai tana cewa,"wannan ba itace tarbiyar dana baki ba Zaytuna, kuma ko ki ɗago ƙafa kizo mahaifiyarki tasa miki albarka ko kuma wallahi in ƙaraso nan inyi miki duk abinda zuciyata ta sani, dan ba ki isa ki lalata mana farin cikin da muke ciki ba".
Tayi shiru a sanda Turaki yaje gaban Zaytuna ɗin ya kamo hannunta, har ta cije tana neman ƙwacewa, ban san me ya faɗa mata a kunne ba yasa ta biyo shi.
suna zuwa gaban Mum Turaki ya zube duka gwiwoyinsa a ƙasa, yaja hannun Zaytuna da ta tsaya ƙiƙam itama ta zube nata gwiwoyin, dama wannan ranar ya daɗe yana jira, dama wannan lokacin yake ta jira, dan haka kawai sai ya haɗe hannayensa duka biyu alamun neman yafiya cikin amon sauti me mugun ban tausayi yace,"Mum dan Allah dan Annabi ki yafe mana, ki yafe min dan girman Allah, wallahi tallahi ban san ta yacca akayi wutar ta kama ba, da sanina ba zan haddasa gobara ba Mum kema kin san banda fitina, amma ina neman yafiyarka dan Allah Mum".
yay maganar hawaye na sakko masa hoton komai na wancan lokacin na haska masa musamman a sanda yabi Mum ta hankaɗo shi ta rufe ƙofa ta tafi ta barsu.
Hajiya Ramla ta fashe da kuka, kukan da ya tafi ya shiga kunnuwansu ya daki zuciyar Turaki da Zaytuna, suka yi saurin ɗago ido suna kallonta, a ɗazu zai faɗi duk wani saukar hawayenta da sunan hawayen farin ciki, amma wannan kukan da ta kasa riƙe ƙarfin sautinsa na shaida masa so take ta yishi iyakar gwargwado, ta yanda zata samu ta rage raɗaɗi da baƙin cikin wani abu dake ranta. to me ya kawo hakan?, shi da yayi mata laifi.
kuma kafin ya gama karantar dattin baƙin cikin dake saman fuskarta sai yaga ta sauko daga kan kujerar, itama ta zube nata gwiwon a ƙasa ta rungumo su jikinta tsam. tana kukan sosai tana faɗin,"Babana babu abinda ka yi min, baka min