NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 175 of 323

ki yi tunanin...". bata ƙarasa ba Ummi tasa hannu ta rufe mata baki, hawaye na zubar mata tace,"tambayar da nayi miki daban, zancen da kike min daban". Fillo ta ƙara matseta tace,"kiyi haƙuri Ummina". tace,"ban san amsar tambayata". Fillo ta rumtse ido tace,"ai tun sanda kika tafi na dawo wurin Kaka. wannan halin da kika ganni a ciki kuma wanda zan aura ne sila". lokaci ɗaya jikin Ummin ya hau kyarma ta ɗago Fillo ajikinta tana bin ta da kallo tace,"ya zamo silar me?, me yay miki?, ina Kakan?". tace,"garkuwa yayi dani Ummi after all na basa dukkan yarda". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, muryar Ummin ta fita a hankali da cewar,"ina fatan bai cuce ki ba?". bata iya amsawa da baki ba sai Kai da ta ɗaga kawai. anan taji Ummin ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, kafin ta furta,"Allah ya daɗa kare min ke, ya kareki daga sharrin duk wani abin ƙi. dan Allah kiyi haƙuri ƴata da abinda nayi muku, ban da bakin ce muku komai domin nasan ni ɗin me laifi ce, amma yanzu na dawo gareku sai mutuwa ce zata raba mu, ina roƙonku dan Allah ku yafe min, ki yafe min Autata". Fillo tace,"ni ba kiyi min komai ba Ummina". sai ta ɗago kai tana kallon Ummin tace,"Ummi to ya akai...". kuma karantar fuskarta kawai Ummin tayi ta bata amsa ba tare da ta ƙarasa ba. "Dr Yusuf, shi ya shigo da ni nan yay min nuni da ke, shine sabon ɗan da Allah ya bani wanda ya kula da ni shi da matarsa kusan shekara guda, ba ƙyama, ba hantara, sun ɗaukeni kamar mahaifiyarsu, duk da ni nayi musu laifi na ɓoye musu cewar ina magana tsawon lokacin da muka ɗauka, haka nayi ta wahalar da su da aikin rubutu a takarɗa kuma basu taɓa ƙosawa ba". maimakon kallon Ummi sai Fillo ta koma kallon Dr Yusuf, babu ko ƙyafta ido, kenan shisa watarana da yazo hira wajenta yace mata yana ganin me kama da ita sak, in ace zata yarda da ya kaita ta ganta, tave masa ba wani nan wasa yake yi, ashe Umminta ce ma, Umminta ya taimakawa har yake kyautata mata da irin halin karamcinsa. _"sun ɗauke ni kamar mahaifiyarsu"._ haka Ummin ta faɗa, ƙwarai yau ta ƙara tabbatar da cewa Dr Yusuf na musamman ne, kuma ya zama dole ta saka masa da taimakon mahaifiyarta da yayi, kamar yanda ta san cewa yafi ƙarfin duk wani abu da zata basa, haka bata san irin kyautar da zata yi masa ba domin nuna masa godiyarta, but zata tambaye shi kyautar da yake so tayi masa ko da ace za'a kai ga matakin da sai ta ɗaga zoben azurfarta ta siyar. Dr Yusuf ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa tana sauke idonta ƙasa tace,"Ubangiji Allah yay maka sakayya da gidan aljannah akan taimakawa Mahaifiyata da kayi, Allah ya rabaka da iyaye lafiya"...haka ta dinƙa jera masa adu'a kafin tace masa,"dan Allah Dr a wurin da ku ka tsinto ni ba kuga wata mata ba?". Dr Yusuf yace,"ai ba tsinto ki mukai ba, kawo ki akayi". ta ɗan dube shi da mamaki tace,"bai gudu ba?". yay murmushi kafin yace,"ƙanina ne yanzu haka yana waje tare da su Daddy nah, itama matar da kike magana tana waje, ƙila zuwa yanzu ma su Kaka sun iso dan anyi musu waya tuni". ai rufe bakinsa kenan t a saki hannun Ummi ta diro akan gadon tana ce da Ummi,"ba inwa Kaka albishir". bata jira cewarta ba ta fito da gudu daga ɗakin tana ƙwala wannan kiran sunan na,"Kaka ga Ummina". ba tare da ta lura da jama'ar da suke cike a wajen ba balle tabi ta kan dalilin da yasa akayi wannan dandazon. kuma cikin sa'a tana fitowar tayi karo da su Kaka na shigowa, idonta a rufe ta doka wani uban tsalle ta ɗafe Kaka tana ihun murna tana faɗa mata Ummi ce. Kaka lamarin sai ya nemi ya bata tsoro dan sai take ganin kamar ko Fillo ta samu matsala ne, ta tafi zata faɗi dalilin ɗafe jikinta da Fillo tayi sai taji an saurin riƙota ta gefe. Kaka ta fashe da kuka tana cewa da Fillo,"Fillo ashe dama Amir ne ya ɗauke ki, ashe yaron nan ba mutumin arziƙi ba ne, ashe Amir azzalumin bawa ne, ashe duk wannan kyawun halayyar tasa yardararmu yayi saboda cimma wata manufa tasa, ashe baƙin *BIRI* ne shi ya *LULLUƁE* kansa ta yanda ba zamu shaida mugun ƙudurinsa ba, Allah ya isa tsakaninmu da shi, ko yafiyarmu kaɗai ta ragewa Amir shiga aljannah ba zan yafe masa ba, sai Allah yay mana hisabi da shi, kuma insha'Allah sai yaga sakayya, sai ubangiji ya bi mana hakkin cutarmu da yayi tun anan duniya. yanzu muna kan hanya Khalil ya ɗauko mu ance an kawoki asibiti rai hannun Allah muka ji sanarwar an kama waɗanda sukai garkuwa da ke, wallahi tallahi ban shaida muryar matsiyacin ba sai Yami ce ta shaida, sai kuma da naji an ambaci sunansa, yanzu haka ance gobe za'a kai su kotu Hajiya Madina tace sai yayi zaman gidan yari". sai ta fashe da kuka sosai tana ƙara cewa,"yasa na siyar duk da wani abu da ku ka mallaka a wajen mahaifiyarku, sai da ya tsiyatamu tass Fillo, biyar ɗin kanmu bamu da ita a yanzu, yasa muka ɗauki dukkan yarda da amana muka ba shi?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba ɗaya tsoron kowa nake yi Fillo, ta ya yanzu zaka iya tantance fuskar mugun mutum da ta mutumin kirki bayan mugwayen na amfa
🏠