NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 174 of 323

feta ba lokacin, amma kallo ɗaya ta yiwa Mum ɗin tasan itace mahaifiyarsu da kowa ya taso a family yake jin labarin ɓatanta. a taƙaice dai Maama da iyalanta duk sai suka manta da batun wata Fillo saboda tsabagen farin cikin da suke a ciki. kuma haka suka zama ababen kallo a wajen dan tuni akai caa akansu ana kallon ikon Allah. gaba ɗaya sun cikwikwiye Hajiya Ramla sun kasa jin ma abinda ta-ke cewa na,"ina da patient kuyi a hankali". but inaa duk wannan batu da take yi babu wanda ya jita hatta Turaki dake manne a jikinta. kuma a lokacinne Kaka suka shigo ita da su Yami da Khalil waɗanda yaje ya ɗauko daga asibiti, sai dai me?, zuwan su wajen kawai suka ga Fillo a guje ta fito tana ƙwala kiran,"Kaka ga Ummina, Kaka Ummina ta dawo". _ayi haƙuri nayi late, azumi nai na kasa motsi after ansha ruwa._ *Vote, Comment, and Share.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _😂😂yau dai ina typing ina gyangyaɗi, so duk baragadar da ku ka ci karo da ita ku gyara da kanku kawai🤣🤣._ *37* gaba ɗaya Fillo sai ta rikice ta firgice ta nemi fita a hayyacinta, ba don komai ba sai dan tsananin murna da kuma mamakin ganin mahaifiyarta a lokacin da bata tsammata ba, tsabar farin ciki ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ganin komai ta ke yi tamkar mafarki ko kuma ba daidai take gani ba, lokacin da ta farka da matsanancin ciwon kai ta tashi, amma buɗe idon da zata yi ƙwayar idanunta suka sauka akan Ummi dake zaune a gefenta ta kama hannunta ta riƙe tana hawaye. da farko tai zaton gizau idonta yay mata, dan haka tai saurin maida murfin idonta ta rufe sannan ta ƙara buɗewa, kuma a wannan buɗewar ne ta tabbatar da abinda ta gani ɗin gaskiya ne, Umminta ce a gabanta, wannan macen da tafi gwal, tafi zinare, tafi lu'u lu'u girma da daraja, wannan macen ce da bata da tamkarta a duniyarta, tauraruwar da ke haska duniyarta, mahaifiyarta ce mafi soyuwa a ranta, jarumar da tai fama da rainon cikinta tsawon watanni tara, jarumar macen da ta tsaya tsayin daka akan ibadarta da iliminta da kuma tarbiyarta, jarumar macen da ke sadaukar da farincikinta domin ƴaƴanta, jarumar dake ɓoye zafin ciwon rashin lafiyarta gudun tashin hankalin ƴaƴanta, jarumar uwar da ta kan iya haƙura da loma ɗaya na abinci da zata sa a bakinta ta rabarwa ƴaƴanta, tabbas itace, ba zata mantata ba ko da ace tana cikin ciwon hauka ne, har a naɗe duniya ba zata kasa gane ɗumin jikinta ba, ba zata manta wannan farar fuskar da bata iya bacci ba har sai ita tayi, abu ɗaya da ta san yake dahir shine uwa dabance, daban take da kowacce irin halitta a duniya, soyayyarta dabance da ta kowa, ƙaunarta ma haka, mahaifiyarta itace ranta itace jininta itace duniyarta. hawaye ta dinƙa ji yana bi ta gefen fuskarta, dama tasha faɗawa Kaka cewar Ummi bata mutu ba tana raye, kuma da izinin Allah zamu gana da ita, sai ga shi yau ta ganta, sai ga shi ta ganta a ranar da wani macuci, azzalumi ya dasa baƙin ciki a zuciyarta wanda ba zai taɓa gogewa ba, to mai ma zai ci gaba da zamar da wannan baƙin cikin alhalin ga mahaifiyarta ta dawo a sanda take tunanin babu me iya share mata hawayen baƙin cikin da Amir ya haifar mata?, ai babu wani sauran baƙin cikinsa kuma, ta san in ace bata sami ganin mahaifiyarta ayau ba, to tabbas baƙin cikin abinda Amir yayi mata shi zai zama ajalinta. zata iya cewa bata san lokacin da ta yunƙura ta miƙe zaune ba daga kwancen da take, jinta tayi kawai ajikin Ummi tayi mata wata tsatstsaurar runguma, Ummin ma ta kewayeta da dukkan hannayenta tana daɗa matseta a jikinta, Fillo taji saukar wannan ɗumin na daban wanda ajikin uwa kawai aka halicci yana ɗumama jikinta, tana jin wannan soyayyar mahaifiya ta daban tana ratsa jini da sassan jikinta, sai kawai suka fashe da kukan farin ciki a tare, babu wanda ya lallashi wani acikinsu har sai da suka yi me isar su tukunna. cikin muryar kuka tace,"Ummina ina sonki sosai". kuma abinda taji Ummin ta fara ce mata shine,"Auta wa ya kawoki nan garin?, me ya sa me ki haka?". ta tambayeta ɗin tana janyeta daga jikinta tana dubanta, tana yi mata kallo me cike da tausayi da kuma fargabar abinda bata fatan ya kasance a rayuwar ƴarta, domin tasan rashin uwa a tare da ƴaƴanta babu halin da baya jefa su, balle kuma su da basu yi sa'ar uba ba, wanda ko kallonsu ba yayi balle ya kula da rayuwarsu. a lokacin sai kawai ta faɗa ƙirjin Ummi tace,"Ummi kullum sai nayi kukan rashinki, Ummi ko me nake yi tare dake nake yinsa a zuciyata, Ummi duk sanda naga ƴa da mahaifiyarta sai nayi ta kuka in kasa ko da cin abinci. Ummina me yasa kika tafi inda ba zamu ganki ba?, me yasa baki ci gaba da wannan haƙurin naki ba?, me yasa kika bari takaicin ɗa namiji da baƙin cikinsa yasa kika nesanta kanki da ƴaƴanki da kowa naki?, Ummi kin san kuwa tsananin son da nake miki?, muna fa yi miki so me zafi, Ummi kin san buƙatar rayuwar ƴaƴa shine mahaifiyarsu, amma mu sai kika ƙaurace mana na tsawon shekaru da yawa, Ummi ba kiyi tunanin in ta gayyara ba?, ba
🏠