NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 173 of 323

a,"Beta Half". yace,"pick". tace,"my daughter inlaw right?". sai ya saketa ya karɓi wayan yana wani murmushin na daban, ya shafo kumatunta yace,"you will soon meet her". ya faɗa yana miƙewa tsaye still holding her hand ya juya yana kallon kowa dake kallonsu, idonsa ya sauka akan Inna Wuro da ta saki baki tana kallon film ɗin da zuciyarta ke raya mata shi take kallo. ya saki hannun Mum ya isa wurin da take bakinsa gaba ɗaya yaƙi rufuwa, yana zuwa da sigar tsokana yace,"tsohuwa aron ɗan kwalin kanki". da sauri kuwa Inna Wuro ta kunto Farha dake bayanta ta jefa masa zanin goyon tace,"komai ma ai sai a baku girmaku ne". ya karɓa ya juya bayan yace mata,"Thanku, zan baki tukwici after". ya isa wajen ya rufe fuskar Hajiya Ramla da zanin sannan ya zauna kusa da ita yace,"stay quite har inje in dawo kinji". tai masa knodding kanta kawai tana binsa da kallo da jin soyayyar nan ta ɗa na fizgarta. ya miƙe kenan sai ga Hajiya Madina ta iso wajen hankali a tashe, tana ganinsa ta yo kansa a rikice, za tai magana expression ɗin da take gani a fuskarsa yasa ta tsaya tana ƙare masa kallo. kafin ta ɗauke idonta daga kansa da mamaki tabi mutanen wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, sannan ta ƙara kallonsa tace,"mene haka a fuskarka?, Fillon ta farka lafiya ne?". ya kamo hannunta yace,"insha'Allahu lafiya zata farka, yanzu just close your eyes i want to show you something". tace,"in rufe idona?, ka nuna min me?". ya zagaya ta bayanta yace,"suprise". sannan ya ɗora haɓarsa kan kafaɗarta yana fuskantar da ita wurin da Mum ke zaune yace,"gidan da kika gina a Ausburg nake so a matsayin tikwici". tace,"na ma baka Me Babban suna, amma ni dai barni in buɗe idona inga halin da yarinyar mutane ke ciki, ni ce silar condition ɗin da take ciki, so this is not time for joke, kaima ɗin mamakinka nake". ya saketa yana faɗin,"indai kika buɗe ban ce ba isn't a suprise, kuma sai na doka miki yaji". Hajiya Madina tai shiru ƙirjinta sai duka yake, Turaki ya ƙarasa wurin Hajiya Ramla ya ɗauke zanin daga saman fuskarta, sannan ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ya kwantar da gefen fuskarsa a gefentata, Hajiya Ramla tabi Hajiya Madina da kallo tana jin wani irin shauƙi na kewar ahalinta da tayi, tana tuna irin rayuwar zaman lafiya, jin daɗi da kwanciyar hankalin da sukai da Madina. Hajiya Madina na yin kalar tausayi har sannan idonta a rufe tace,"Me babban suna kai ka taɓa saɓa umarnina, amma ni ba zan iya saɓa naka ba, but ai na san kana jin tausayina ko?, to mu jingine wasa gefe kaji ɗan albarka". muryarsa na fita da wani emotions yace,"gidan da ke Ausburg Maama". tace,"naji nace maka, muna komawa gida zan baka takardun". yay murmushi me kama da dariya ganin duk yanda ta ƙosa yace,"promise?". tace,"i do, har ma da key ɗin sabbin motocina guda biyu duk na baka". yace,"zanyi kyauta ne da su nima". tace,"tunda na riga na mallaka maka ikonka ne kai duk yanda kaso da su, can i open my eyes now?". yana dariyar jin daɗi ƙasa-ƙasa yace,"not now, untill i say". kawai sai yaga ta buɗe idon, Hajiya Madina ta buɗe idon da niyyar kai masa duka ganin yau yana neman mayar da ita wata yarinyarsa abinda basu taɓa yi ba, ƙwayar idonta ta sauka akansa sai kuma ta mayar da kallonta kan fuskar da take ganin kamar gizau a kusa da shi. in ace da abinda yafi mamaki tabbas ta shiga cikinsa, ta ƙara buɗe ido tana kallon Hajiya Ramla dake ta mata murmushi, ta ƙwala wata ƙara tace,"Your Excellency are you really the one?". ta faɗa bakinta na ƙin rufuwa tana ganin hakan kamar a mafarki. sai kawai tai sufa taje ta rungume Hajiya Ramla tana faɗin,"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah". ta faɗa tana ɗagowa daga jikinta ta shiga duddubuta wai ganin dai kamar ba dai-dai take gani ba. a lokacin ne kuma su Zaytuna suka ƙaraso wajen, abinda kowa ya gani yasa suka tsatstsaya da mamaki suna kallon Maama da tabi ta susuce saboda tsabagen murna. Maama ta waigo ta kalle su tace,"ubangiji yaji kukanmu ya amsa adu'armu ya dawo mana da Mum". ai kan kace me wannan asibiti ya karaɗe da ihun murna, duk suka tafi da gudu suka faɗa kan Hajiya Ramla suna ta ihu, wanda in ace a tsaye ta-ke sai sun kaita ƙasa. Zaytuna ce kawai ta tsaya taƙi zuwa wajen tana kaudar da fuskarta da gefe, dan ita bata ganin zata yi farinciki kamar yanda bata tunanin zata yafewa Mum. Ilham kuwa na tsaye daga gefen su tana ta kallon su cike da burgewa, musamman Turaki da ta kasa ɗauke idonta a kansa saboda yacca ta-ke ganin haƙoransa gaba ɗaya a waje, da irin tarin farin ciki da annurin da bata taɓa ganinsa ba aciki. a ɗazu hankalinta duk a tashe yake da bai dawo gida ba, haka da taji wurin kidnappers ya tafi hankalinta ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi, but a yanzu zata iya cewa kamar tana jin kanta ne a saman gajimare tana tafiya, ko ba komai tasan lokaci yayi da zata samu wannan gurbin da Turaki ke cewa ba zata same shi ba a zuciyarta, ta sani wuyarta mahaifiyarsa ta san ita matarsa ce, ita kanta bata san Mum ba dan ba'a hai
🏠