NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 172 of 323

a banji ba ban gani ba". Umma ta dafa kafaɗar Mum dake bin bayan Nuratu da kallo tana jin shigar wani al'amari me girma a tare da ita. a hankali Umma tace,"am sorry to say, amma ɗanki bai da lafiyar ƙwaƙwalwa ko?". Mum ta juyo da kallonta gareta tace,"ɗana kuma?". ta tambaya da mamaki. Umma tace,"ehh fa, wanda ke zaune anan kusa da ke". kan Mum ya ƙara ƙullewa tace,"me kike son cewa ne?". ta tambaya tana jin ƙirjinta na bugawa. jin ƙarar saukar mari ya tattara hankalinsu kan su Turaki gaba ɗaya, Nuratu ce a gabansa tana huci tana faɗin,"baka da hankali ne?, ya daga ganin mahaifiyata zaka kama hannunta, ko an faɗa maka mu kafirai ne kamarka?, shashashan banza da wofi, to wallahi in baka bar asibitin nan cikin gaggawa ba sai nasa ƴan sanda sun zo sun tafi da kai yanzu". Turaki ya ɗago da fuskarsa yana dafe da kuncinsa, hoton fuskar tasa ya shiga cikin ƙwayar idon Hajiya Ramla da suka ƙaraso wajen da sassarfa. cikin zafin nama Turaki ya ɗaga hannu zai saukewa Nuratu zazzafan mari Hajiya Ramla ta zaro ido waje tana faɗin,"Babana". ta faɗa da ƙarfin sautin da yay amsa kuwa a wajen. Turaki yaji saukar muryar a cikin kunnensa, yaji shigar sunan acikin kansa da cikin zuciyarsa, daga jin muryar kasan muryar babbar macece, amma hakan ba shi zai hana shi gane mamallakiyar muryar ba, ba shi zai hana shi gane muryar kowa ce ba a duk inda ya jita, tsawon shekaru da yawa ba tare da suna tare ba, hakan ba zai hana shi gane muryar wadda ta kawo shi duniya ba, da wayonsa ta tafi dan haka a ko'ina kuma a kowanne hali yaji voice enta zai shaida. sai dai kafin komai dake cikin kansa ya gama wanzuwa sai ganin Hajiya Ramla yay a gabansa, ganin nata kuma ya firgita shi sau ɗaya yaja da baya, sai kuma ya dakata yana binta da kallo ƙwayar idonsa duk a waje. an ɗauki tsayin shekaru da yawa, sai dai duk tsayin shekaru da dogon zamanin da zata ɗauka ba tare da ƴaƴanta ba, hakan ba zai hana tana kallonsu ta shaidacewar su ɗin jininta ba ne, kamar yanda shima ba zai taɓa manta mahaifiyarsa ba, babu tantama wannan ɗanta ne, haka shima yake jin babu tantama wannan wadda ta kawosa duniya ce, ɗanta ne wanda ta tafi ta barsa a lokacin da yake shakaru shida a duniya, kamar yanda shima yake ganin uwassa wacce ta tafi ta barsa lokacin da yake da shekaru shaida a duniya. sai kawai ta fashe da kuka, Turaki ma da yay mutuwar tsaye ya fashe da kukan farin ciki, ya taho da sauri ya rungumeta yana faɗin,"Mum, Mum are really the one?, da gaske idona ba gizo suke yi min ba?, Mum ina kika tafi?, ina kika je Mum?, me yasa kika tafi kika barmu?, laifin me muka yi miki Mum?". maganarsa ta katse, kukan tsananin murna da farin cikinsa ya ƙaru. ya janye daga jikinta yana daɗa kallonta, daga shi har ita babu wanda zai iya kwatanta irin abinda yake ji a tare da shi. kallonta yake sosai da irin wannan tsananin so da tausayin da Allah ya halicce shi na daban a tsakanin uwa da ɗanta. Hajiya Ramla na hawaye ta kai hannunta ta kama fuskarsa, ɗayan kuma ta dungure masa kai fuskarta ɗauke da tarin murmushi, tace,"babu Alhamdulillah sai wannan tarin tambayoyin Babana". bai iya cewa komai ba, haƙoransa duka suka bayyana a waje kamar yanda nata ma suka bayyana, ya kuma rumgumeta sannan yace,"to Mum na faɗa Alhamdulillah...then you too should answer my questions". Hajiya Ramla ta ture shi daga jikinta tana cewa,"to ba zan amsa ba ɗin, in kuma ka zama Me girma Turakin Taraba sai in ji". ta faɗa da irin salo na wasa dake tsakanin uwa da ɗanta. ta kamo hannunsa tace,"where is Zaytun?". ya kasa ce mata komai, kawai sai ya ƙara rungumota yace,"to Mum aina kika ɓuya?, there are alot of questions but ki fara amsa min wannan". tace,"Babana muna gaban mutanene fa". ya zare jikinsa anata ya kama hannunta yaja ta zuwa wajen kujeru dake wajen ya zaunar da ita. shi kuma ya zube gwiwoyinsa a ƙasa tare da kwantar da kansa saman cinyarta yana kamo hannunta duk biyun ya riƙe su da kyau kamar wanda za'a ƙwaceta. daga ita har shi babu wanda ya iya cewa komai, hannunta a sumar kansa tana shafawa, shi murmushi ita murmushi, haƙoranta a waje nasa ma a waje. jinsa yake kamar ya buɗe cikinta ya koma ciki, haka itama ji take kamar ta tsaga ƙirjinta ta sanya shi a ciki, kowanne da maganar da yake son yi amma tsananin farin ciki da murnar da suke ciki ya ha rufe bakinsu. idon kowa dai tuni ya dawo kansu, aka bar batun Fillo da halin da take ciki, basu san tuni ta farka a lokacin su Dr Yusuf su kai kanta, kuma lokacin da zai shiga ɗin ne ya kama hannun Mommi ba tare da sanin kowa ba da hankalisu yay can kan su Turaki ba ya shiga da ita ciki ya tsayar da ita dai-dai saitin da idanuwan Fillo na buɗewa zasu sauka akanta. Hajiya Ramla tace,"Babana am asking you where is Zaytun?". ya ɗago da kansa ya kalleta kawai sai ya ƙara rungumeta. a lokacinne kuma wayarsa dake aljihu tayi ƙara, yace,"Mum ɗauko ki min picking ba zan iya sakinki ba". ta zaro wayar daga aljihunsa tana bin sunan dake yawo a jiki, kamin tace mas
🏠