NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 171 of 323

hannayensa sarƙe a bayansa, idonsa ya kai bayan Mum da har yanzu ke zaune bata tashi daga wurin da tayi sallah ba, adu'a kawai take akan Allah ya tashi kafaɗun Fillo, har ga Allah tana so ta nemi ahalinta a wannan lokacin to amma ba zata iya ba har sai Fillo ta farka, yarinyar ta taimaka mata a lokacin da take neman taimako. duk da bayanta yake kallo haka yayi tsaye sai kallonta yake ya kasa ko da motsi, ya kuma kasa ɗauke idonsa akanta, yana jin wani irin abu na shigarsa, yana jin kamar yana so yaga ko wace, gaba ɗaya bai san dai taƙamemen abinda yake ji a tare da shi ba. yay ajiyar zuciya ya juya ya koma bakin ƙofar, yaci gaba da kallon Fillo yana ta adu'a cikin ransa, bini-bini sai ya kalli agogo ya duba time, cikar lokacin da likita ya ɗiba kawai yake jira, da dukkan fatansa na in lokaci ya cika ta farka lafiya lau. sai dai haka ɗaya kuma yaji totally ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na masa wani irin zillo, tunaninsa da hankalinsa ya rabu waje biyu, so yake yaci gaba da tsayuwa anan har sanda Fillo zata farka, haka kuma so yake ya bar wajen yaje wajen waccan matar da bai san wacece ba. ba tare da sani ba ya bar wajen ya nufa wurin da Mum ke zaune har yanzu, ya tsuguna ta gefenta daga ɗan bayanta, ba tare da sanin taƙaimemen abinda zai yi ba, idan ma magana zai mata shi bai san me zaice mata ba, zuciyarsa ce kawai ta kawo shi. ya buɗe bakinsa zai furta abinda bai san zaice ba sai ga Ammi ta ƙaraso wajen, bai iya ce mata komai ba ya bita da kallo har ta zagaya ta gaban Mum ta tsuguna agabanta. Ammi tace,"kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, Ɗana ya tabbatar min da cewar ƴarki zata farka cikin amincewar ubangiji, kuma zata farka lafiya lau insha'Allah". a sannan Mum ta ɗago da kanta tace,"Allah ya amsa, amma Hajiya lokaci yaja da yawa, har yanzu fa shiru". tai maganar muryarta ɗauke da sautin damuwa. Ammi ta ƙara cewa,"adu'a zamu ci gaba da yi". Mum bata iya magana ba illa gyaɗa kanta kawai da tayi. bata san me take ji a tare da ita ba, amma dai tana jin zuciyarta na ƙara matsuwa da zullumin son kasancewa acikin ahalinta, ba abinda idanuwanta ke da muradi yanzu sama da su ga Babanta, taga ƴaƴanta tukunna ta sami kwanciyar hankali. Umma ta ƙaraso wajen, Ammi ta ɗauke kanta daga kallonta, Umma bata kula hakan ba tace,"Ammin Yara wannan itace mahaifiyar yarinyar da Aliyu ya buge ɗin?". Ammi ta kauda fuska gefe tace,"umm ita ce". ta faɗa tana miƙewa ta bar wajen, Umma ta zagaya ta ɗaya ɓarin ta zauna kusa da Mum, suka gaisa tana yi mata adua da sanar mata cewar itama mahaifiya ce wurin yaron da ya bigesu ɗin. Mum tace,"Allah sarki, mun gode sosai. kun tsaya mana baku bari mun wahala ba". Umma tace,"to ai hakan ya zama dole akan wanda yasan hakkin bawa". ta faɗa idonta na kan Turaki da har sannan yake tsugune daga can gefe, kamar wani mutum mutumi sai bin kowa yake da ido, shi abinda ya ɗaure masa kai tun zuwan Ammi wajen yaji tana batun mahaifiyar Fillo, shi yasa yaji kamar ƙafafunsa ma ba zasu iya ɗagawa ba dan haka kawai yaji jikinsa duk yay sanyi, kuma Allah Allah yake yaga fuskar matar. ganin tsananin kamar dake tsakanin Turaki da Mum wanda Ammi bata lura da hakan ba yasa Umma ce masa,"sannu fa, ya mai jiki?". Turaki yaji kamar ba da shi take ba, lura da hakan yasa Umma cewa,"da kai nake". ta faɗa tana murmushi. yana sauke idonsa a ƙasa yace,"Alhamdulillah". tace,"to Allah ya bada lafiya, dan Allah ina daɗa bayar da haƙuri a madadin yarona". shi dai bai iya cewa komai ba, ya zama kamar wani soko ko me neman gafara. kuma Umman na yin shiru ta hango Nuratu da Mommi na nufo su, har da Inna Wuro dake goye da Farha. itace a gaba ta taho tana cewa da Umma,"Falmata ni dai Amadu ya rantse yace min ba aljanu ba ne mutanene shisa ma na iya shigowa asibitin nan amma da a waje zan tsaya gaskiya, dan ban iya saka kaina a masifa, Aliyun ma ni da wurin ƴan sanda aka kaishi tunda ance har yanzu yarinyar bata farka ba, ko kawai ayi kotu da ɗan banza kowa kuma sai yay ta kansa kar aja kuɗin Amadu ya ƙare". Umma ta miƙe tana cewa,"sannu da zuwa Inna". tana rufe baki Nuratu da Mommi suka iso wajen, dai-dai kuma da miƙewar Turaki. yana tashi idonsa ya kai kan Mommi, ta ke idanuwansa suka firfito waje yana binta da kallo me ban mamaki da al'ajabi, me yake gani?, dama da gaske akwai fuska biyu a duniya?, wannan matar ai photocopy ɗin Fillo ce. Mommi da ta iso gabansa ta ɗaga masa hannu alamar sannu. mamaki na bala'i ya ƙara kama shi, bai san lokacin da ya kamo hannunta ba ya jata zuwa room ɗin da Fillo ke ciki. ganin hakan yasa kowa miƙewa yabi bayansu da kallo harta kuwa da Mum da taji su Umma na cewa,"ikon Allah wannan yaron na da lafiya kuwa". Nuratu tace,"ah wannan sai dai mahaukaci". ta faɗa tana bin bayansu da sauri. Inna Wuro tace,"ah tou haka duk zaku yi ta gamuwa da gamonku, ance aljanu ku ka kwaso kun dage mutanene, ni dai da naga ba zan iya ba ai ta kaina zanyi, wa zai zo ya wahala, haka kawai a shanye ƙafa ko wuy
🏠