zata tashi".
daga nan kowannensu sai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran lambar da ya nema a contact list, daga ɓangaren Dr Yusuf matarsa Nuratu ta ɗaga kiran tana sallama acikin muryar bacci.
ya kalla agogon hannunsa yaga ƙarfe biyu da rabi na dare a lokacin, a sanyaye yace da ita,"Farha har tayi bacci ne?". tace,"ban sa ni ba wallahi, na barta tare da Mommi na shigo ɗaki saboda kaina da ke ciwo, your Excellency ni dai gobe zuwa zanyi na nemo mata maganin kuka gaskiya".
yay guntun murmushi yace,"ba wani magani da za'a bata, kowanne jariri ai yana kuka dama". Nuratu na noticing yanayin voice ɗin nasa tace,"ehh amma nata kukan yayi yawa". sannan ta daɗa cewa,"your excellency lafiya kuwa naji muryanka so sad?".
yace,"lafiya lau". ba don ta yarda da cewarsa ba tace,"as early morning zaka dawo ko?".
yace,"ehhh may be". tace,"Inna Wuro ma fa ta dawo, daga saukarta ta biyo ta nan wai anan zata kwana can gidan aljanu sun shiga, sai surutai ta-ke wai Aliyu ya kaɗe aljanu sun tafi da shi zasu ɗauki fansa, fatan ta Allah yasa kar su kashe shi tunda ya kashe ƴar sarkin aljanu, da gaske ne yay accident ɗin?".
yace,"Allah ya gyara Inna Wuro, yanzu kina jina?, zan aiko driver ya ɗauke ku, sai ku shirya ku taho tare da Mommi".
tace,"ni dama from your voice na gane babu lafiya, meke faruwa Dr?, kar dai da gaske Inna Wuro ta ke yi".
jin duk tabi ta rikice yace,"relax, yarinyar bata mutu ba ai. akan maganar da nayi miki kwanaki ne".
tace,"wai Dr nah kana ganin hakanne kuwa?".
yace,"i pray so hakan ta faru, na gwada jinin yarinyar ɗaya yake dana Mommi, Swty sai dai kinzo xaki ga abinda nake faɗa miki, dan Allah kuyi da sauri ina so ku ƙaraso before yarinyar ta farka. kuma karku taho da Inna Wuro tazo ta ishi patients da zance, ki bar mata Farha itama kar taita kuka".
daga haka ya katse wayar yana kallon Turaki dake yiwa Maama bayani.
"ban san ya akai ba Maama, asibiti sun kira ni kawai, yanzu haka har an sanya mata jini likitan kuma yace zata farka nan da 30minutes".
daga ɓangaren Hajiya Madina tayi magana sannan ya ƙara cewa,"ehh naga Dsp nata kirana amma ban ɗaga ba". tace,"tom gamu nan Me Babban suna, plss take care". yace,"Maama kizo da sauri dan Allah".
ya kashe wayar ya saka a aljihu tare da miƙewa ya fita daga office ɗin ba tare da yace da Dr Yusuf komai ba.
Fitar tasa babu jimawa Dr Yusuf ma ya biyo bayansa. inda ya same shi tsaye a bakin ƙofar room ɗin da Fillo ke ciki yana leƙenta ta cikin wani glass.
daidai da ƙarasowar Daddy da Ammi wajen, Yusuf ya isa wajensu yana kallon Aliyu da ce masa,"Malami ka kwantar da hankalinka, kayi adu'a kawai Allah yasa ta farka". Aliyu ya sauke numfashi yana komawa da baya ya zauna kan kujera.
Yusuf yace da su Daddy,"na fito ai tun ɗazu ban ganku ba".
Ammi tace,"gida muka koma, da dukkan alama mutanen acikin tashin hankali suke, dan sai bayan zuwanmu da muka shigo cikin haske naga alamar hakan a tare da mahaifiyar yarinyar, ashe ko ɗankwali ma babu a jikinta, haka ma sarƙa ce ɗaure da hannunta. shine naga babu dacewar mu tsaya da ita a haka tunda mutane kowa na wucewa, dalilin da yasa muka koma gida kenan".
Yusuf yace,"Ammi wannan matar fa ba mahaifiyar yarinyar bace, ni har na fara ɗaukar maganar Inna Wuro fa, saboda ita wannan yarinyar ta taɓa kwanciya a asibitin nan, tana da matsalar aljanu da suke yawan ɗaukarta su kaita wani wajen, shi yasa nafi tunanin nima ko aljanar tata ce ta fito a siffar mutane".
Daddy yace,"a'a wannan matar mutum ce, kun riga kun san baiwar da Allah yay min, da naga aljani na san shine. ta bakin nata dai tace wasu mutanene suka sace su shine suka samu suka gudu".
Yusuf ya sauke nunfashi yace,"ofcourse an kidnapping yarinyar in ban manta ba 1month kenan".
Ammi ta nemi wuri kusa da Aliyu ta zauna, bayan ta dube shi da tausayawa ta kalli Yusuf tace,"ya jikin yarinyar?". yace"da sauƙi, nan da mintuna kaɗan ma zata farka".
Daddy yace,"mun biya ta station sun kwance sarƙar hannun matar, da ƙyar suka yarda da mu akan hakan dan tunanin su ma wai ko me laifi ce ta gudu, to amma duk da haka sun haɗo mu da police ɗaya sannan sun shigar da report wai should incase. yanzu please kasa nurse ko kuma kai da kanka kayi ƙoƙarin mata treating hannunta, tsintsiyar hannun duk ya farfashe yay caɓa-caɓa da jini wallahi, abin tausayi".
ya juya yana kallon Ammi yace,"tana ina?".
tace,"gata can wajen corrido ɗin can tana sallah, naga hankalinta duk yaƙi kwanciya, ni tausayi ma ta-ke ban wallahi".
Dr Yusuf ya kira wata nurse, yayi mata nuni da inda Mum ke zauna yace ta ɗau kayan aiki taje wajenta. ba ɓata lokaci Nurse ɗin kuwa tai treatment duk inda wani ciwo yake ajikin Mum, dauriya irin ta babba shi kaɗai ya hanata yin kuka, dan sosai take jin zafi da raɗaɗi, har aka gama ƙwayar idonta na kallon gefe ɗaya, sai bayan an gama tukunna ta ɗago tana kallon duka hannayen da aka ɗaure wajen bandage kaɗan ba mai yawa ba.
a lokacin Turaki ya bar jikin ƙofar ya shiga kaiwa da komowa a wajen