NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 165 of 323

ai cikin rashin sa'a suna buɗewar suga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan. "raise your hands up". su shidan da suka rage ba'a harba ba suka ɗaga hannayensu sama time ɗin da Dsp yay arresting ɗinsu. Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fillo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba acikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido ko zai ganta anan duk da perlon ya fara dubawa. jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera dake wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wacca ƙwayar ta kaɗa tayi jawurr ya sauke kallonsa akan Dsp yace,"yallaɓai banfa ganta ba, bata cikin gidan nan yallaɓai". muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka. Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu ƴan sanda guda uku zo, waɗanda sune aka saka su nemo Fillo a sanda suka shigo gidan. "yallaɓai babu wurin da bamu duba ba acikin gidan nan kaf babu yarinyar". Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa yace,"ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?". da farko duk shiru suka yi sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko tukunna ɗaya acikinsu yana karkarwa yace,"mu ma bamu san inda ta ke ba". yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙe a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"wallahi bamu san inda tayi ba ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo". furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"what!, ta gudu?, baku san ina tayi ba?". ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga. Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"dan Allah kayi haƙuri". Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu". Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo da son tabbatar da abinda ƙwayar idonsa ke gani. cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fillo har yana riƙe ma ta hannu har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen. "You!". Turaki ya faɗa in shock. sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci. yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki. "waye kai?". Turaki ya tambaya . tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo. Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir yayi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki. Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannu da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle. a taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukaci wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"who are you?". sai da fuskar Amir ta kumbura tayi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa, tukunna Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can ya doko shi ta can, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yayta ball da shi kamar wanda ya samu ball ɗin gaske. tun Amir na iya ihu har yazo ya daina, tun yana buɗe baki yana uban nishi da son yin magana har ya kasa, shi kansa so yake yace da Turaki who is he, dan wannan dukan da yake masa ko uwarsa ya kashe sai haka. da Dsp yaga dai Turaki na ƙoƙarin yin kisan kai yace da ƴan sanda dake tsaye,"ku dakatar da shi". amma me ƴan sanda uku akansa sun kasa ƙwace shi daga kan Amir, suma ɗin duk sai da ya watsa su gefe yana miƙewa cikin huci da cewar duk wanda ya ƙara zuwa kusa da shi sai ya haɗa da shi. bai ma san sanda yasa bayan hannu ya kwaɗe police ɗin dak
🏠