NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 164 of 323

yake suka fita daga wajen tana ta uban kuka. suna fitowa tayi wani kukan kura ta shaƙi wuyan Jakadiya tana girgizata tana faɗin,"wallahi ba ki isa kin tona min asiri ba, ba zan kwanta cuta ba kibi ta bayan fage kije ki fallasa ni, zan kasheki sannan zan je in kashe Ramlar ma". haka ta dinƙa sambatun magana bata saki wuyan jakadiya ba har sai da ta tabbatar ta mutu tukunna ta jefar da ita a wayen, ta bar wajen kamar ana tankaɗata har ta fito daga cikin jejin, tana zuwa ta buɗe mota ta shiga Driver yaja su, sai da suka shigo cikin gari sannan tasa ɗankwalinta ta shaƙo wuyan driver shima tana faɗar,"ba zan barka a raye ba kaima ka tona min asiri, ba zan barka kaga ciwona baka tona min asiri". bata sake shi ba sai da ta tabbatar ya mutu, kuma kamin Fulani Azima tayi wani ƙoƙari na karɓar kan motar, motar ta gangara ta faɗa gefe, nan ta-ke glass ɗin motar ya tarwatse da yawa suka soki cikin kanta, ta kurma ihu tana neman ɗauki tana ƙoƙarin fitowa a motar, bata ankara ba ta kai fuskarta saitin wani glass da yay kamar kibiya ƙwayar idonta ɗaya ta soki glass nan take ruwan idon ya shiga tsiyayewa. *A dai-dai wannan lokacin.* *Yanda Abin ya kasance da kuma yanda abin ke faruwa.* sanda Turaki ya ƙaraso wurin da kidnappers suka buƙaci da ya ajiye kuɗin, yay parking motarsa ya fito ɗauke da dumin jakar kuɗin. ya tsallako side ɗin da suka ce yay tafiya me nisa sannan ya ajiye jakar a wajen, ya ɗauko wayar Maama dake aljihunsa ya ɗaga calling ɗinsu dake shigowa. daga can ɓangaren yaji ance,"kai ne kasa coffee yadi?". yace,"ehh ni ne". ya faɗa yana duddubawa ko zai ga ta inda mutumin yake. sai yaji mutumin na dariya yace,"ai ba zaka taɓa ganinmu ba ka bar wahalar da kanka da waige-waige, ka juya ka bar wajen ka koma bakin motarka ka jira yaronka zai zo ya sameka". jin haka yasa Turaki saurin juyawa ya bar wajen, for the next 5minutes sai ga mutumin yazo ya ɗauki jakar shi kaɗai, cikin sauri yake tafiya don barin wajen, a lokacin Turaki ya fito daga jikin wata rila da ya laɓe. yasa hannu a bayan wandonsa ya zaro bindigar da bai taɓa riƙeta ba sai a yau, ya saita ƙafafun mutumin ƙwayar idonsa na hasko masa yacca ake harbi acikin film, bai taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai a yau da ya shiga office ɗin DSP ya ɗauko ba tare da sanin kowa ba, kazalika bai taɓa riƙe bindiga ba balle har yay attempt na harbi, but today bindiga tazo hannunsa, and zai gwada amfani da ita ko da ace wannan itace dama ta ƙarshe da yake da ita a duniya. ya saita ƙafar mutumin ba don yana tunanin dai-dai ya saita ba, kuma babu ɓata lokaci kai tsaye ya saki bullet, kuma cikin sa'a bulle ɗin ya shige ƙafar mutumin, hakan kuma bai sa Turaki ya haƙura ba ƙara sakin bullet ɗin wanda a yanzu kai tsaye ya wuce zuwa kaɗar mutumin daidai sanda ƙafafunsa ke durƙushewa a ƙasa yana sakin jakar kuɗin ya riƙe kafarsa dake zubar da jini. abinka da wanda bai san kan lamarin ba kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin dake fuskarsa. yana faman huci kamar mayunwaci za ki yace,"ina yarinyar ta ke?". ya faɗa cikin ɗaga murya sosai. sai kuma ya sassauta muryarsa yace,"zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuɗin ka tafi safely, but first tell me ina yarinyar ta ke?". shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa atake ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yacca yaji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu. Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin ƴan sanda suka mara masa baya, yayinda wasu mutum biyu suka ɗauke wannan wanda Turaki ya harba sukai mota da shi. harbin farko da Turaki yayi su Amir sunji a lokacin suna laluben Fillo acikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri ɗaya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta suka koma ta yanda zasu tsira. Amir yace,"duk yanda akayi shegun mutanen nan da police suka zo". wani me kama da shi yace,"tabbas kuwa, but har ta ya mu kayi sakacin hakan ya faru?". sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fillo yace,"hau katanga ka duba mana". yana hawa katangar ya ƴan sanda daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi yace musu,"police ne mota har guda uku". yana faɗar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi. su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fillo ta bi, sai d
🏠