ajiye sarƙar a gefen boka tace,"wannan kyauta ce na baka. kuɗinta kimanin miliyan goma ne, kyauta ce kawai ba kuɗin aikinka ba".
Boka na murmushi yace,"godiya nake".
tace,"sai muje ga lissafin abinda zan bayar akan aikin".
ya ɗaga kansa sama yana kallon reshen bishiyoyi na tsawon daƙiƙa kafin ya sauke yace,"da farko za ki bayar da miliyan goma, sannan za ki kawowa jikokin Aljanu baƙin jaki guda biyar, sannan za ki haƙa kabari ki yanko mana zuciyar jariri fari wanda ana haihuwarsa ya mutu, sannan kuma muna buƙatar yatsa ɗaya na ita mahaifiyar Dikko".
rufe bakinsa kenan sai suka ga jan ƙyalle ya faɗo gabansu ɗaure da wani dunƙulen abu.
da tsananin mamaki yake kallon abin na tsawon daƙiƙa biyu kafin ya kai hannu ya ɗauko ƙyallen, ya ɗauko shi zaren da aka ƙulle shi na warwarewa.
mamakin dake tare da shi bai gama sakinsa ba yaga baƙar kurciya ta faɗo kan hannunsa a ma ce, sabon mamaki tsantsa ya kama shi.
ya ɗau kurciyar ya haɗe da wannan ƙyallan sannan ya juyo yana kallon Fulani Azima wadda idanuwanta ke a warwaje tana binsa da kallo.
taji yace,"ya akai haka?".
tace,"me ya faru?".
yace,"me na faɗa miki shekaru ashirin da biyar da suka wuce kafin nayi miki aikin Ramla?".
cikin saurin baki da rawar murya tace,"kace kar na kuskura inyi sakacin da asirin nan zai karye, domin duk ranar da ya karye ba zanji da daɗi ba".
tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan yace,"ban labarin yanda aka yi bayan barinta gida".
jikinta na rawa tace,"lokacin da ta bar gida can ƙasar china ta nufa kamar yanda ka faɗa, bayan wata uku na bi sahunta zuwa dajin da kace anan aka jefa kurciyar domin na tabbatar da taje can ɗin. kuma ko da naje na ganta ɗin a gefen wata bishiya tana cin ganye, itama kuma ta ganni dan har ta dinƙa roƙona akan in taimaka mata bata san ta yanda akayi tazo wurin ba, ta bar Muhammad da Zaytun acikin ɗaki wuta tana ci bata san ba ko Madina ta kula kar yaran su cutu. sai nayi mata dariya nake faɗa mata cewar ni ce silar zuwanta wurin kuma ita da ƙara komawa wajen ƴaƴanta har abada. to muna cikin haka da ita ne sai ga wasu turawa sun zo, suna zuwa suke tambayata cewar nasan wannan mahaukaciyar ne?, da farko har zance musu a'a sai kuma nace ehh, sai ɗaya daga cikinsu yace min to suna da buƙatar siyanta idan zan siyar musu zasu yi tsafi da jininta, ni kuma jin hakan yasa ba tare da wani tunani ba na amince musu dan har inda suke da zama ma muka je tare suka min bayanin cewar zasu ajiyeta aɗakin tsafi tsawon shekara ashirin da shida cif kafin nan sai su zuƙe jinin jikinta suyi tsafin da zasu yi da shi, kuma tare da ni suka sakata a wani ƙaton ɗaki ko taga babu suka kulle suka ce za'a ke bata abinci ne kawai tana ci, don har sarƙoƙi suka saka suka ɗaureta saboda kar ɓacin rana yasa ta gudu, kaji abinda ya faru Boka, ko ɗaya ban saɓa ƙa'idar aikinka ba wallahi".
Boka ya ƙara murmushi sannan yace,"Azima aikinki ya lalace, domin kuwa maganar da nake miki yanzu asirin da yake kan Ramla ya barta kuma ba da jimawa ba za ki karɓi sakamakonki saboda aljanin da yay wannan aikin ba me yafiya ba ne".
Fulani Azima ta dafe ƙirji cikin bayyanuwar tashin hankali a tare da ita tace,"kamar ya Boka ban gane ba, me kake so kace min?, ta ya hakan zata faru?".
yana ɗago matacciyar kurciyar da jan ƙyallen yace,"waɗannan sune asirin da ke kan Ramla, wannan kurciyar da kike ganinta tun ranar da ta ɗauki Ramla bata ƙara zuwa nan ba sai yanzu, wanda ke tabbatar da cewa Ramla ta baro inda ta ke ta dawo cikin garin nan, kuma mutuwar kurciyar nan shine zahirin cewa babu wani abu da ya sami Ramla".
sai ya jefar da kurciyar sannan ya ɗauko ƙyallen yaci gaba da cewa,"wannan kuma shine ƙyallen da muka ƙulle ƙwaƙwalwar kifaye acikinsa saboda Ramla ta manta komai, dan haka faɗowar wannan da kuma warwarewarsa ya shaida mana Ramla ta dawo cikin tunaninta".
ya jefar da ƙyallen ma sannan ya juya bayansa yana kallon akuyar dake tahowa tana kuka yace,"idan za ki iya tunawa wannan itace akuyar da kika kawo muka ɗaurewa baki saboda rufe bakin Ramla, tsawon wannan shekarun tana nan tare da ni bata taɓa kuka ba sai yau kuma ayanzu, hakan ke tabbatar da cewa bakin Ramla ya buɗe duk inda ta ke yanzu tana can tana magana".
Fulani Azima ta ɗora hannu akanta tare da kurma ihu tace,"na shiga ukuna".
Boka yace,"ba ki shiga uku ba tukunna sai kinga yanda reshe zai juye da mujiya".
ya faɗa yana sa hannu ya daki ƙasar dake gabansa sannan yace,"kar hankalinki ya tashi sosai, ke ko garin da kike ba za ki bari ba, amma sai dai za ki kwanta baƙar jinyar da za ki ji gwara ace haukacewa kika yi ko kuma ɓatan kika yi da wannan ciwon da zai kamaki. domin za'a zo har kan gaɓar da hatta ƴarki ba zata iya zuwa kusa da ke ba".
Fulani Azima ta fashe da kuka sosai tana cewa da boka yay mata rai. cikin wata razananniyar tsawa yace da ita,"Azima ta shi ki bar mana wuri". ya faɗa yana nuna mata hanya.
suka miƙe tare ita da Jakadiya jikinsu sai rawa