in nan lafiya".
Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Fillo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum.
Fillo tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? sai mu kira su azo a tafi damu".
Mum tace,"su waye hakan?".
Fillo ta ɗago ido ta kalleta sannan tace,"lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina".
Mum ta girgiza kanta tace,"ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba". sai kuma ta haɗe hannayenta tace,"idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su, sunce zasu yi tsafi da ni ne, kuma babu abinda nayi musu".
Fillo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta tayi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba ayanzu ƙila sai ta gani da idonta.
a lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fillo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu".
Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda basu san ina zasu ɓulle ba suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan suci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke.
*A dai-dai wannan lokacin.*
Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne acikin ruwan ƙwaryar dake gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki.
"to ban san dai abinda hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki".
maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta tace,"wacece wannan?, wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?".
sai kuma tayi ƙasa da murya tana kallon Boka tace,"ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, nayi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne".
Boka yay dariya yace,"haba Azima, yanda muke da ke ai kin fi ƙarfin haka a wajena. abinda nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta".
sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"leƙo ki gani". ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye doguwa siririya, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu.
yace,"to kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu".
fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa tace,"to saboda me boka?".
sai yasa hannunsa acikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fillo yake yace,"ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin adu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba haka kuma bata min ɗaya bata ambaci adu'ar neman tsari ba. saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki babu abinda asirinmu ya isa yayi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi".
kan Fulani Azima yay matuƙar ɗaurewa, ta dinƙa hasaso tsayin yarinyar tana so ta kwatanta shi da na Ilham amma sam babu haɗi, tsayin Ilham bai ko kusan nata ba. to wacece wannan ɗin?, tabbas ya zamar mata dole taje gidan Alƙali Dikko da ƙafafunta, idan aljanu sun kasa ita ba zata gaza ba domin ba ta taɓa barin wani ya shiga gaban al'amarinta, dole sai taga bayansa ko waye.
ta numfasa tace,"shikenan me girma boka, yanzu ya batun mu na janyo hankalin Alƙali Dikko kaina?".
Bokan ya bushe da dariya yace,"kin haƙura kenan, ai nayi zaton har yanzu kina kan bakanki na cewar son gaskiya kike so Dikko yayi miki ba sai anyi amfani da asiri ba gudun lalacewa wataran".
tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai tace,"mu bar tuna baya. yanzu dai a san abinyi akan Mai martaba, a kashe shi kawai na huta da aurensa da ke kaina. shi kuma Alƙali ayi aikin da za'a gama da rayuwarsa kawai, ina nufin ya saki kowa ya kamani ni ɗaya hatta kuwa da mahaifiyarsa. tashin farko abinda nake so shine Alƙali ya fita daga hayyacinsa yaywa Madina saki uku sannan duk ya kori ƴaƴansa, daga baya kuma sai ya dawo kaina ya mallaken ta yanda zamu yi rayuwa da shi har a bada. da wannan buƙatar ta biya sai a raba auren Ilham da Turaki, kuma ta yanda nake so mutuwar auren ta kasance Dikko yaje gidan da kansa ya umarci Turaki da ya saki Ilham".
Boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana ɗaga hannu sama yace,"buƙata taki ta biya Azima, duk yanda kika nema haka za'ai, kuma komai da kika nema zai faru tabbas, angama da wannan buƙata taki ki jira kwanaki biyu kacal".
Fulani Azima ta saki wani murmushi na jin daɗi da kuma nasara, sannan ta miƙawa Jakadiya hannu. cikin rawar jiki Jakadiya tasa hannu cikin jaka ta ɗauko yari da sarƙa da zobe ta saka a tafin hannun Fulani Azima.
har yanzu murmushi bai ɗauke a fuskar Fulani Azima ba ta