NOVEL SHARES -
a sai taji jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata electric shock, haka ma zuciyarta na harbawa fat fat kamar zata faso ƙirjinta ta fito, numfashinta na fita da ƙyar tana jin kamar ana zare ranta.
ta jingina kanta da bango tana kasa rufe idonta, komai da ta ke ji ta ke gani kamar mafarki ba gaske ba. ta ƙara dafe bangon wurin tana rumtse idonta tana girgiza kanta da ɗan saurin kuzarin da take jin tana da shi, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ta buɗe ido taga ba Amir ta gani ba, Allah yasa idan ta buɗe idon taga mafarki ne ta ke yi ba muryarsa ta ke ji ba acikin azzaluman mutanen da tasan babu makawa sai wutar Allah ta ci su. Ta shiga buɗe idonta a hankali tana mai tsoron buɗewa bugun zuciyarta na ƙara tsananta.
a lokacin ta ƙara jinsa yace,"ba zata san ni na tsara komai ba kuma na shirya ba har sai bayan na gama da rayuwarta. zanje yanzu dan ana kan hanyar kawo kuɗin fansarta...in ance ma nasan mutanen nan a shirye suka da yin komai akanta da tun farko ba'a ɗauki tsayin wannan lokacin ba, da ban tsaya na jira na gama haifar da tashin hankalin da bai da misaltuwa ba a wurin Kakarta, da a yanzu kuma bamu ambaci miliyan ɗari biyu ba, da 2billion naira zan ambata musu".
Fillo ta buɗe baki tana ƙoƙarin furta kalmar innalillahi a fili amma sai taji ta kasa sarrafa harshenta, sai bakinta da ke rawa kawai, cikin fitar hayyaci ta juya da gudu ta buɗe ƙofar ta fice tana jin kamar numfashinta zai ɗauke.
gudu take sosai acikin duhun daren, cikin jejin da take gani kamar ba'a duniya ba, ko gabanta bata iya gani sosai, sai da ta tabbatar tayi nisa sosai sannan ta duƙa tana haki a wajen da ta ke, wucewar daƙiƙa biyu ta ɗago ta ɗora daga inda ta tsaya, tun ƙafafunta na ɗaukarta har taji suna dab da dainawa, kuma a lokacin da ƙarfinta ya ƙare lokacin taji tayi karo da abu, karo da abu kamar mutum.
tsoron da ya barta tun a ɗazu sai ya dawo sabo a sanda ta ɗago ido tana kallon halittar dake gabanta, da sauri taja da baya tana dafe kanta cikin ranta tana jin anya kuwa yau itace?, anya bata yi gamo ba?, anya zamanta a wajen can bai sa aljanu sun shiga jikinta sun rikita mata tunani ba?.
sai ta juya tana kallon bayanta kan ta juyo ta ƙara kallon matar da ke gabanta wadda ta ke duk a firgice, firgicin da zata ce ya ninka nata, kuma mafaka take nema, inda zata tsira da ranta ta ke nema.
sai taga matar ta ɗaga hannunta biyu tana haɗe tafun hannunta alamar roƙo, ruwan hawaye na bin idanunta, jini ya taru a ƙwayar idonta, a cikin rawar murya irin wadda ta sa ni taji tace mata,"dan Allah ki taimaka min zasu kashe ni, amma dan Allah kema karki cuce ni".
ta faɗa acikin yaren fulatanci muryarta na shaida tsananin tsoro da kuma tashin hankali.
hasken farin watan da ya hasko su ya haskawa Fillo sarƙar da aka ɗaure hannun matar da ita, ya kuma haska mata abayar dake jikinta wadda taci ubanta da mugun dauɗa sai wani kalar wari ke fita a jikinta, yalwataccen gashin kanta a barbaje ɗauke da tsirarrun furfura duk ya tuttuje.
Fillo ta tsayar da ƙwayar idonta akan dogwayen yatsun matar tana jin wani kalar hawaye me zafi da bata taɓa zubar da irinsa ba na bin kumatunta, kallon yatsun nata ta ke amma a yatsun wani hannun na daban, furucin da matar tayi na maimaituwa acikin kanta da irin sautin muryar da ta sani, ta rumtse idonta sosai tana jin ruwan hawayen dake ciki na ƙarasa sauka.
bata san lokacin da ta faɗa jikin matar ba ta rungumeta tana fashewa da kuwa, kuma ƙarar harbin bindigar da suka jiyo ya cika dokar dajin yasa ta fizgi hannun matar sukai gefen wata bishi suka ɓuya, ba nata ƙirjin kaɗai ba, har na matar tana jin yanda yake bugawa kamar zai faso.
a bakin bishiyar wajen suka duƙe Fillo na kamo kan matar ta kwantar akan ƙirjinta tace,"Alhamdulillah, welcome back to the family".
*please vote, comment and share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Avoid any mistake._
*35*
Fillo na rungume da matar har bayan wucewar wasu daƙiƙu sannan ta zare jikinta anata, ta ƙara saka idonta akan fuskar matar don tabbatar da abinda ta gani ɗin kar taje ko idonta ke mata gizo.
ai ko da ace bata taɓa ganin hotonta ba, tsananin kamannin da take da yaranta kaɗai ya shaida mata wannan itace matar da suka ɗauki shekaru ashirin da biyar basu ganta ba.
ita ayanzu ma sai ta iya rantsewa hoton fuskar Turaki kawai ta-ke gani a fuskarta, ta kamo hannayenta tana daɗa kallo da suke sak da na Zaytuna tun daga kan tsayin yatsun har farcen, haka ma a sautin muryarta sai ka rantse kace Zaytuna ce tai magana, daga nan sai kuma ta sauke idonta akan sarƙar dake ɗaure da hannuwan nata.
taji hawaye ya kusa sakko mata tsaboda tsananin tausayi, tayi attempting kunce sarƙar sai taga ba zata iya ba.
ji tayi matar ta ƙara ce mata,"dan Allah karki cutar da ni kema".
Fillo tai murmushin ƙarfin hali, taji tausayin kanta na bin iska yana tafiya, yayinda na matar ke biyo iska na lulluɓeta.
tace,"ba zan cutar da ke ba Mum, adu'a nake so kiyi mu fita daga wur