NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 160 of 323

a lafiyarta ba wannan alƙawari ne, ta ya zaku karɓi kuɗin?, or throught bank za'a tura maku". mutumin yay dariya sosai yace,"zaka kawo mana kuɗin da hannunka". nan ya shiga korawa Turaki bayanin inda zai je ya kai kuɗin ya ajiye. Turaki ya tabbatar masa da cewar zai zo ɗin in the next few minutes amma su tabbatar ba su yiwa Fillo komai ba. mutumin na bushewa da wani dariyar yace,"ga yaronku kuyi magana dan ka tabbatar yana lafiya, idan kunji jishi yana kuka ba komai bane akayi masa, soro ne kawai da yake ciki". daga can inda mutumin ke zaune kan kujera ya ɗorawa Fillo wayar a kunnenta a tsawa ce yace,"yi magana da father naki". cikin matsanancin kuka tace,"Kaka". Turaki ya ƙara matse hannun Maama da har yanzu ke hannunsa, muryarsa a hankali yace,"Fulaniii". sai kuma ya fesar da iskar bakinsa me zafi yace,"kina jina?". a wahalce tace,"Turakii, dan Allah kazo ka cece ni, kashe ni zasu yi sun ce, wai zasu yi amfani da ni, ka faɗa musu Kaka bata da kuɗin da suke nema". ta faɗa cikin kukan da duk wanda yaji sai ya zubar mata da hawaye. Turaki ya tattaro jarumtarsa da yake jin tana neman barinsa yace,"kiyi shiru ki daina kukan kinji, zan zo in ɗauke ki yanzun nan. babu abinda suka isa suyi miki in har bakinki bai gushe da ambaton Allah ba, amma na faɗa miki ki daina kukan kinji Fulani". wannan jarumtar tasa ta maza yaji ta ƙwace, bai san sanda ya zube a gefen gadon Kaka ba, idonsa na cika da tarin hawaye, ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya magana ba, acikin zubar hawayen da babu wanda ya lura da shi a fuskarsa yace,"karki bari suyi miki komai kinji Fulani, i know who you are, i know you can protect your dignity, dan Allah karki bari suyi miki komai, dan Allah". yanda take sauke numfashi a wahalce kawai yake jiyowa, ya matse idonsa sosai yana jin zuciyarsa na wani mugun matsewa, yaci ta sassauta kukan tace,"to zaka zo yanzu". yace,"yes, i will come right now, just some minutes kinji". ƙit yaji wayar ta katse, ba tare da yabi ta kan kowa dake jiran cewarsa ba ya ratsa ta tsakiyar Maama da Yami ya fice daga room ɗin cikin sauri. yana shiga mota yay dialling number D.P.O yace masa,"ranka ya daɗe kun fara tracing numbern?". yace masa,"yes, before wayan naku ya katse har mun gano a inda suke, yanzu haka yara sun ɗau hanya. ka tsaya ka ɗauke ni a hanya". Turaki nasa hannu ya sha re zufar goshinsa yace,"please ka faɗa musu suyi a hankali kar suja su cutar min da ita". da haka ya katse wayar sannan ya kira wayar Khalil yace,"Bro i need five hundred million naira in cash right away, kaje Zenith Bank wurin Faisal, on my way to meet you there in the next 10minutes". acikin motar Turaki da yake sharara mahaukacin gudu akan hanyar zuwa ƙauyen pindiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na dare har tayi, waya ce maƙale a kunnensa yana tabbatarwa da kidnappers ɗin cewa shi ɗaya ne ba tare da kowa ba kamar yanda babu wanda ya shaidawa maganar.. sai dai a dai-dai wannan lokacin da yake wayar da su, a dai-dai wannan lokacin Fillo ta samu damar zare igiyoyin jikinta ta miƙe tana bin hanya saɗaf saɗaf ta yanda babu me jin motsinta, kuma ta tabbata har ta fice babu wanda zai ganta kamar yanda mutumin nan ya faɗa mata. sai dai kuma me?, sanda ta ke zuwa gab da ƙofar zata fita, dai-dai jikin windown wani ɗaki, bala'in tsoron dake tare da ita sai ya koma zuwa tsantsar mamakin abinda kunnuwanta ke jiyo mata, muryar wanda ta ke ji da kuma sautin dariyarsa da abinda yake faɗa na saka jijiyoyin jikinta tsinkewa. ta ja ƙafarta a hankali ta isa jikin window tana leƙawa ta yanda ba za'a ganta ba, tana tsaye a wurin kunnuwanta na ci gaba da jiye mata abubuwan da yake faɗa, maganganun nasa da take jinsu tamkar ɗigar dalma ajikinta, in one time sai taji jikinta gaba ɗaya ya zama kamar na statue, ko hannunta ta kasa motsawa, ko idonta ta kasa ƙiftawa, zata iya rantsewa cewa zuciyarta kanta ta tsaya da aikin buga jini zuwa sassan jikinta. a sanda ƙyar idonta tayi tozali da shi ta siririyar ɓular, zaune tsakiyar mutanen wanda ya tabbatar mata shine Babban Oga da taji suna ta ambata, kuma yana ɗaya daga cikin mutanen da suka shigo ɗazu har tabi su da kallo. sai ta koma da baya ta lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar ta zama ƙanƙara tana narkewa ruwan yana taruwa acikin idanunta, taji duk wani tsoro nata yana bin iskar wajen dake kaɗawa, taji kamar duk wani abu da yake cikin kanta yana farfashewa a ƙasan wajen da ta ke, taji duniya gaba ɗaya tayi mata zafi. sai ta ƙara matsawa da baya tana saka hannu ta goge hawayen da ya taru cikin idonta amma sai taji ƙamas babu komai, idonta a bushe yake kamar famfon da ya shekara guda babu ruwa, haka ma fuskarta. "Amir!". taji zuciyarta ta furta da wani irin amo kamar ba nata ba. "Amir ta ke gani anan, Amir ta ke ji yana faɗar shi zai fara keta haddinta kamin kowa, shi ta ke ji yana faɗar ya cika burinsa na shekara da shekaru ya gama handame musu komai, har yana faɗin bai zama lallai ma su barta da rai ba". gaba ɗay
🏠