NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 323

aje wannan a ɓangaren tunaninka...idan ba haka ba wallah ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, ba ruwanka da sabgar ƴaƴana ka fita a harkarsu". Ya ɗago ido ya kalleta ta ɗauke nata daga kallonsa, muryarsa a ƙasa yace,"ita Yusran me tace miki dama?, babu wanda ya duketa balle zagi, kayan da zata fita da su ne basu dace ba akace ta sauya shikenan sai ta ɓare baki...". Ammi ta wurga masa wani kallo tare da cewan,"ni rufe min baki, ina ruwanku da shigar da tayi, ina ce ai ba tsirara zata fita ba ko?...da ƴaƴan waccan Matar ne da kake kallonta da gashin ido ai ba zaka ce da su ƙala ba, sai nawa ƴaƴan da aka raina shine za'a bi a takura musu...to da gatansu tunda ban mutu ba saboda haka a bar takura musu, na faɗa maka. itama kuma Kakar taka ka faɗa mata...shima Aliyun zai shigo ya same ni". Ya girgiza kansa kawai, kamin yace,"kiyi haƙuri". Tana ƙoƙarin fita maganarsa ta tsaida ita,"Ammi dan Allah ki kwana ɗaya kawai". Tace,"tunda takarda aurena a hannunka ta ke me zai hana". "dan Allah Ammi, wallah idan ki kai nisa da yawa gidan baya daɗi". Tai murmushin takaici,"har yaushe asirin da ke kanka ya kunce daka fara sanin muhimmancina acikin gidan nan?...kaima ka zama mace ka iya makirci kenan, to ni ba zaka yaudaren ba, ko ɗazu baka san ina kallonka ka shigo ka fita ba ne saboda kana tsoron kada uwarka ta tsine maka...". Yusuf yay saurin katseta da cewan,"Ammi don Allah ki daina irin wannan maganar...". Itama bai ƙarasa ba ta katse shi da faɗin,"an riga an shanyeka ai duk gaskiyar da zan faɗa a iska zaka dinga jinta". Yay shiru bai ce komai ba, ta ƙara cewa,"ka tashi ka kaini airpot". Yay saurin miƙewa yana karɓan jakar hannunta suka fita tare. Tunda suka shigo motan babu wanda yay magana, har ga Allah Yusuf naso yay hira da mahaifiyar tasa amma yana tsoron ta balbale shi da faɗa, dan yanzu da abunda yake na faɗa da wanda ba na faɗa ba duka na faɗa yake zamar mata indai tsakaninta da shi ne. Tunda yazo ma yake son mata albishir da cikin Nuratu amma yana tsoron abunda hakan zai haifar, dan bata ƙi ma tai muguwar adu'a ba tunda ba son auren nasu ta ke ba, ita duk abunda ya shafi Falmata to shikenan ta ɗaura gaba da shi, yasan da ace Nuratu ba jinin Falmata bace Ammi zata ɗan rangwanta masa akan ƙin zaɓinta da yay. Maganarta ta kutsa cikin tunaninsa. "yarinyar da na so na haɗaku ce za'ai bikinta. Da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai ya haɗata da wanda ya fika. Ɗan governor ɗin Jigawa ne, yaron ance a ƙalla ya mallaki sama da miliyan 200. Shi ɗaya ne a wurin mahaifinsa, babarsa ita ɗaya ce for morethan 35years da suke tare da mijinta...ba irin Babanka ba da shekara 15 muka ɗauka tare yaje ya ɗauko min annoba". Yusuf yace,"Allah sanya albarka a auren nasu". Aciki ta amsa masa, yana kallon yanda ta ke hararsa ta cikin window, tunda yake da ita basu taɓa fita tare ba ta shiga back seat ba sai yau, tunma bayan auren nasu dama bata yarda ta shiga motarsa, hanya ma bata so su haɗa da shi. "Ammi Nuratu ta kwan biyu bata da lafiya". Ya faɗa cikin kwantar da murya. Ammi ta dakata daga danna wayar da ta ke yi ta ɗago ta dube shi, kamar ba zata ce komai sai can kuma a hankali tace,"bata da ƴan'uwa ne?". Ya rumtse idonsa sosai kamin yace,"tana da su mana Ammi". "ohh tou kuma kazo kana faɗa min bata da lafiya, ai su zaka je ka sama bani ba da ban haɗa dangi da ita ba". Bai ƙara cewa komai ba yay shiru, Sani Abacha International Airport ya ajiyeta, bai baro wajen ba sai da jirginsu ya tashi tukunna. Yana kan hanya abokinsa Dr Huzaifa ya kira shi, saboda haka ya yanke hanya ya biyo ta shongo estate. Slowly yake driving ɗin, Idonsa na kallon left side yana kallon wani gini da ake ƙarasawa, idonsa ya sauka akan yashin da tifa ta juye yanzu ta bar wajen. Kamar wanda ya tuna wani abu sai ya waiga yana daɗa kallon wajen daya bari, hoton wannan yarinyar ya haska acikin idonsa a wancan lokacin daya taɓa wucewa ta wajen. Tana zaune a gefen yashi ta ƙudundune tana rera kuka a hankali, ta riƙe siririyar doguwar ƙafarta tana kallon wajen da taji ciwo cike da tashin hankali. Gaba ɗaya ciwon ba wani babba bane, amma kace wadda akace ƙafartata ce ta ruɓe za'a yanke saboda kawai jinin daya fito a wajen ɗan kaɗan. sai yaga kamar yanzu ne abun ya faru, dan bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba tunawa da yay da irin dramar da suka sha da ita akan kawai ta bari ya saka mata bandage akan ciwon da taji. _"jinina zai ƙare"._ Haka ta faɗa masa a lokacin daya tsuguna gabanta yana tambayarta me ya faru, cikin muryar kuka, kuma duk da cewar muryar tata ɗauke ta ke da kukan da tasha, hakan bai hana daɗin muryarta fitowa ba. Ta runtse ido ma ta kasa kallon ciwon, ya koma mota ya ɗauko first aid amma ko da ya dawo sai ya tarar bata wurin, abun yay matuƙar bashi mamaki a sannan, dan zatonsa ma ko aljana ya gani ko kuma aljanu suka buɗe masa ido yau, saboda kyan yarinyar ma yafi kama dana aljanu. Kuma sai can z
🏠