NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 159 of 323

owa ya fita daga gidan nan, ni kaɗai ne amma zuwa nan da minti goma zuwa sha biyar Babban Oga zai iya zuwa saboda haka ba zan ce miki ki fita nan da wuri ba. kawai dai kiyi hankalin da ba zasu gane cewar wannan igiyar a kwance ta-ke ba, idan kika ta shi akwai ƙofa ta nan baya kusa da parlo da aka cire ki jiya, kibi ta nan ki fita. kina fita za ki hango wata ƙofa a wurin sai kiyi saurin buɗewa ki fita, za ki ganki cikin daji karki tsaya a kusa-kusa sai kin tabbatar kinyi nisa sosai da babu me iya riskar ki". yasa hannu a aljihu ya ɗauko ƙaramar waya yace,"ga wannan kina iya kira gida ki faɗi inda kike ko da za ki kasa gane hanya". tabi ƙaramar wayar hannun nasa da kallo kafin ta ɗago ido ta kallesa tana nazarinsa. yay mata murmushi yace,"ni dai har ga Allah iyakar abin zan miki kenan, ya rage naki kuma ki kuɓutar da kanki ko kuma ki zauna su cuceki tun kina ƙaramarki. dan wallahi ina mai tabbatar miki sai sun mayar dake yarinyarsu after sun gama talauta danginki, ƙarƙari ki kasa juriyar ɗaukarsu ki mutu su jefar da ke, dan Babban Oga bai da imani wallahi". yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fitar ya barta, tabi bayansa da kallo kafin ta dawo da idonta kan wayar da ya bar mata. jin kamar motsi tayi saurin ɗaukar wayar ta tura acikin rigarta, Allah ya taimaketa kuwa tana sawa ana turo ƙofa a shigo. jere ta gansu duk kusan kansu ɗaya, zata iya cewa bata taɓa ganinsu ba duk da cewar fuskokinsu a rufe yake da mask irin wanda take gani a film, suka wuceta suka shiga ciki, in ta lura da kyau kamar harda mace, na ƙarshen ya duƙa gabanta ya mammari fuskarta yana wani makirin murmushi yace,"zamu huta sosai da kai". da faɗin hakan ya miƙe yabi bayan sauran. taji sabon hawaye ya taho mata, ta rumtse ido sosai tana rasa ma me take ji a ranta. dai-dai nan taji mutumin ɗazu ya dawo can ƙasa da muryarsa yana cewa,"you got the chance, zasu yi zaman meeting yanzu and atleast they will take up to 30minutes kamin su gama, babu wanda zai ji motsinki har ki fice, karki yi wasa da wannan chance ina daɗa jadadda maki if not wallahi a yau ko ba'a ɗau gawarki ba sai kin mugun raina kanki, dan kaf wannan mutane da kike gani sai sunyi amfani da ke". yay saurin ficewa gudun kar wani ya fito ya gansa tare da ita. *A dai-dai wannan lokacin.* wayar Hajiya Madina da ke riƙe a hannun Nihal tayi ringing, tai saurin miƙa mata sanda ta ke tambayarta,"waye?". tace,"ba suna a jiki". Hajiya Madina da jikinta yake a sanyaye ta karɓi wayar, dai-dai kuma da katsewar kiran, ta sauke numfashi jikinta duk a mace saboda halin da Kaka ke ciki, tun ɗazu suka zo asibiti amma har yanzu bata dawo hayyacinta ba, a sannan likita ya shigo ɗakin yana cewa,"Hajiya meet me in my office". da hanzari Hajiya Madina tabi bayansa, nan kiran lambar ɗazu ya ƙara shigowa, ta ɗaga tana yin sallama tana ci gaba da bin bayan likitan. daga can ɓangaren taji wata gwandareriyar murya na faɗin,"Hajiya mune kidnapper na ƴarku". tsabagen rikicewa sai wayar ta suɓuce daga hannunta tana tsaya daga bakin ƙofar tana haki kamar wadda tayi tsare, saura ƙiris wayar ta kai ƙasa Allah ya shigo da Turaki yay saurin riƙo wayar yana dubanta. "lafiya Maama?". da shi da kowa na ɗakin suka tambayeta a tare suna yowa kanta. tsabar gigita tama kasa cewa komai sai nunawa Turaki wayar ta ke da hannu. ya kalla screen ɗin wayar yana kallon yacca call ke tafiya, ya kara wayar a kunnensa yana cewa,"Salamu Alaikum". cikin ɗaga murya aka ce masa,"karku ƙara yi mana sallama ba ita muke buƙata ba". mamaki ya bayyana akan fuskar Turaki yace,"wake magana?". aka ce,"wanda suka yi garkuwa da yaro naku ne, kuna san yaron naku a raye ko kuma mu kashe shi mu aiko muku da namansa?". Turaki bai san lokacin da yaywa hannu Maama wata muguwar damƙa ba da yasata yin ƴar ƙara tana faɗin,"Me Babban suna zaka karya min hannu". bai ma san tana yi ba becouse he is totally getting out of control, ƙwaƙwalwarsa ta shiga faɗa masa anger ɗinka ba zai yi amfani yanzu ba, just relax and control your self. ya buɗe idonsa da ya rufe in just 10seconds, yaja leɓensa ciki ya cije da ƙarfi sannan a hankali ya sauke dogon numfashi, ƙwayar idonsa da ta sauya kala ta dawo yanda ta ke. ya ɗauko wayarsa a aljihu yay ɗauki lambar tasu, sannan ya bi bayan kiran nasu da suka katse. bugun farko suka ɗaga, cikin kwantar da murya Turaki yace,"muna jinku, me ku ke da buƙata?". mutumin yay dariya sosai yace,"kun tabbata za ku bayar da komai muka ce?, idan kun san baku shirya karɓan ƴarku ba karku sa mu ɓata bakinmu wajen yi muku bayani". Turaki ya ƙara rumtse ido yace,"duk abinda kuke so na tabbatar da zaku sa me shi". mutumin ya kuma dariya yace,"good. ga yaronku nan yana ta kuka kullum yana so yazo ya ganku, amma munce ba zamu sake shi ba sai an bayar da miliyan ɗari biyu tukunna mu barsa ya dawo gida da ƙafafunsa". zuciyar Turaki na bugawa fat-fat yace,"you got additional of 300million, zan baku miliyan ɗari biyar muddin baku taɓ
🏠