NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 157 of 323

ajiya Madina kam dama tana ganin itace ta shige toilet ta rufe ƙofa, haushin duk wanda ke da sanya hannu akan lamarin aurenan take. bata fito a toilet ɗin ba sai da taji Boɗejon ta fita, ta fito a ranta tana jin haushin irin zagin da Boɗejo ta dinƙa mata ita da Turaki, cikin ranta tana jin ina ma ace akwai ƙasar da babu wanda ya sa ni sai ita, da ba abinda zai hanata ɗauke Turaki a gobe ta kaishi can yaje ya huta na kwana biyu ko zuciyarsa tayi sanyi. acan gidan Turaki dai sabon biki ne ya tashi, dan yana zuwa ya tarar da danginsu da dangin Fulani Azima an cika gidan sai tashin busar algaita ta ko'ina, ta dole Boɗejo ta shirya shi har da cewa wallahi idan baiyi wasa ba sai tayi masa wankan da kanta. ya fito cikin dakakkiyar shadda fara da ta saje da alkyabbar Gimbiya Ilham, yayi azababben kyau har yafi na ranar ɗaurin aurensa. kamar dai wancan kwanakin haka yau fuskarsa duk babu walwala har akai taron aka gama, sai da Boɗejo ta tabbatar sun gama cika al'adarsu sannan hankalinta ya kwanta. jama'a sunci sun sha an bar arziƙin abinci a inda yake, bayan kammalawa Inna Falmata ita tayi jawabin godiya ga duk waɗanda suka zo da kuma tarin adu'oi wa ma'auratan, daga nan kuma sai aka shiga ɗaukar hutuna kamar hauka, kowa burinsa bai wuci yay short vedio yana hasko gidan ba ta yanda duniya zata gani ta shaida gidan arziƙi. ƙarfe biyar na yamma Turaki ya wuce police station kan sabon report da ya shigar tun a ranar da ya dawo, suka kuma tabbatar masa da cewar suna kan yin bincikensu, bai dawo gida ba sai 6 kuma ba gidansa ya wuce ba wurin Maama ya wuce, inda yaje ta tarar ta wuce wajen Kaka anzo ance tana can ta suma. *Kidnappers.* ga duk wanda ya san Fillo a yanzu zai iya rantsewa ba ita bace, saboda yanda ta fita a hayyacinta, abinka da mara ƙiba, kallo ɗaya zaka yi mata ka zubar mata da hawaye saboda yanda ta fige, idanuwan nan sun ƙara ɓurmawa ciki. zaune take akan ƙasan simitin wajen an ɗaure ƙafafunta da igiya, haka ma hannayenta an ɗaure su ta baya, yanda fuskarta tayi jawur da yanda jini ke fita daga bakinta kaɗai zasu shaida maka irin azababben dukan da ta sha a iyakar yau. ƙaton mutumin dake gabanta ya ƙara buga mata bindigar hannunsa a fuskarta, take bakinta ya ƙara fashewa kanta ya lanƙwashe. cikin burkitacciyar hausarsa yace,"muddin baka daina yi mana gardama ba, to wuya yanzu ka fara shanta. in bakayi wasa ba sai mun kaseka ayau ɗin nan". da ƙyar Fillo ta miƙar da wuyanta ta ɗago tana kallonsa da idanonta guda ɗaya da bata iya gani sosai da shi. kallonsa take yi tana hango ranar da suka tsareta suka ce ta bayar da lambar wanda za'a kira, lambar Amir kaɗai ta haddace a duniyarta kuma bata tunanin zata iya bayar da shi, saboda tsoronta kar ya cutu da jin halin da take ciki. sai da tayi da gaske tukunna ta iya haɗa lambar Yami ta bayar dan ba wani haddaceta tayi sosai ba, kuma sai da aka gwada lambar kusan sau uku duk ba correct ba sai ana huɗun Allah ya taimaketa kiran na shiga taji muryar Yami a sanda aka ɗaga, da wannan ta samu ta kuɓuta daga wahalar da suke bata. kuma tun a ranar da aka kawo kuɗin suka ƙirga suka ga harda ƙarin dubu ɗari biyar akai amma hakan bai yi musu ba suka ce fiye da wannan suke so, idan bata manta ba tana jin shi ƙaton na cewa,"wato iyaye naka suna sonka sose, tunda har gashi suna ƙara mana kuɗi akan wanda muka nema. wannan ya nuna mana sewan sun tara kudi da yawa, don haka ba zamu sake ka ba sai an cika mana kudi ya zama miliion goma". tunda taji ance ƙarin dubu ɗari biyar tasan Amir ne kaɗai zai yi hakan duk da bata san ta yanda akayi su Kaka ma suka sami wannan kuɗin ba. dan a ranar da suka kira waya aka sawa su Kaka muryarta tana cewa azo a ceceta, the first abinda Kaka ta faɗa mata shine,"ki daina kuka Fillo, kiyi ta adu'a kinji za ki kuɓuta, banda ƙarfin da zan kawo musu amma Amir zai zo ya tafi dake kinji". ta sa ni a irin son da Amir yake mata zai ƙara fiye da haka ma in har ace yana da shi, kuma tun a ranar ta ƙara jin Amir ya sami wani waje na daban a tare da ita, in ace da sonsa ya ragu da 85%, to a yanzu wannan son nasa zata ce ya ƙaru da morethan 1000%, saboda shi ɗin mai sonta ne kuma me ƙaunarta, dan haka a duniya bata da wani wanda ya fishi. dukan cikinta da akayi da ƙafa shi ya dawo da ita daga duniyar tunani. ta saki kukan da bata jin zata iya riƙe shi, ta shiga ambaton Allah a fili da kuma zuciyarta. ta buɗe bakinta wanda leɓenta suka riga suka zama ganda tace,"ku kasheni kawai, dan Allah ku kasheni ko na samu na huta. kunce sai an ƙara muku kuɗi an ƙara still kuna faɗin bai isheku ba, na faɗa muku bamu da wani gata sai Allah, dan Allah dan Annabi ku kasheni kawai". ƙaton ya jawo jakar kuɗi na biyun da Amir ya kuma kawowa naira miliyan biyu, sai dai basa tunanin da naira miliyan bakwai da rabi kacal zasu iya sakin yarinyar, sun jima suna kidnapping su yanke kuɗaɗe masu uban kauri, amma basu san me yasa akan wannan yarinyar ba suka buƙaci kuɗi kaɗan.
🏠