NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 156 of 323

in. kan uba ke kiga wuri kamar dama can a haka aka ƙera shi, na rantse da Allah wanda bai sani ba yazo wajen nan sai yace gidan sarauta ya shiga". sai tayi saurin zaro waya a jaka tana miƙawa ɗaya daga cikin ma'aikatan tana cewa,"ungo maza lafta min lambarku a wayata, ina zanyi saken wannan azababben decoration ɗin da bikin ƴata, habawaa ai dole jama'a suzo suyi kallo na kece raini ma, ta yanda gobe ba zasu ƙara ɗaukan gajigarin masu decoration na musu aikin wofi suna asarar kuɗi ba". ma'aikacin na murmushi yace,"Hajajju bari na karanto miki kawai". Hajja Balkisu tace,"yi da sauri, ai ni duk a tsume nake. yanda kasan in ɗauke wajen nan in tafi da shi". Ma'aikacin still da murmushi fuskarsa ya shiga karanto mata lambar yana rubutawa,"08067261323". tace,"me zan saka a sunan?". yace,"kawai rubuta Arewa Culture Decoration". daga cikin gida kuwa Gimbiya Ilham na zauna tana ta bin Hadiman dake kaiwa da komowa wajen kimtsa kayayyankin da suka shigo da shi. sai taji suna tafiya da zaman kaɗaicin da ta ke ciki, dan Turaki tuni ya fice daga gidan ko sallama ɓata haɗa su ba. can kuma sai taji parlon ya karaɗe da wata uwar guɗa kamar gidan zai tsage, ta rumtse idonta for the first time da hawayen farin ciki ya sakko mata tun kawota, ko ba komai tasan duk wannan abin da akeyi na murnar ta kai budurcinta gidan miji ne. Boɗejo ta fito daga bedroom ɗin da suka kwana riƙe da farin bedsheet ana haskawa mutane ɓacin da yay dan su shaida, ta bawa Jakadiya Hanne tana barin wajen da rawa. ta isa wurin Ilham ta rugumeta tana ƙara sakin wata uwar guɗa ta musamman, sai kuma kowa yayo kanta ana cewa,"barka Gimbiya, sannu Gimbiya, sannu sannu, Allah ya huce gajiya, ubangiji ya kawo albarkar ɗaki, sannu. Fulani Azima na cewa agaisheki, a gaisheki, ayi miki gaisuwa irin gaisuwar da babu mahaluƙin da ya taɓa samunta". daga nan Boɗejo da Inna Falmata suka kamata sukai cikin ɗaki da ita. bayan an yiwa Gimbiya Ilham gashin ruwan ɗumi mai kyau, sannan aka haɗa ruwan lalle da turare Boɗejo tayi mata wanka da shi, aka fito da ita sai zuba masifaffan ƙamshi take yi. duk wannan hidima dai da akeyi Boɗejo ƙwafa kawai take jerawa tana tunanin irin rashin mutumcin da zata yiwa Turaki tunda yasa ƙafa ya bar ɗanyan amarya ita ɗaya kamar mayya. kwalliya aka yiwa Ilham ta gani ta faɗa, tayi azaban kyau, aka fito da ita a lulluɓe da alkyabba fara tas me adon red ajiki, babu ta inda ake ganinta harta ƙafarta kuwa dake sanye cikin wani half conver na sarauta, akan cushion na babban parlon gidan aka zaunar da ita tayi zama irin na masu mulki, Mutum uku daga dangin mahaifiyarta suka zo suka ɗaga hular alkyabbar nata ana fasheta da turare me bala'in ƙamshin gaske, suna yi ana tafi ana busa shantu ana rera mata waƙa na son barka da kawo budurcinta lafiya lafiya, after sun gama bajakolin fesa turaren sai wasu bayi guda biyu suka zauna kusa da ita gefe da gefe suna mammatsa mata ƙafafunta. acan ɗaya ɓangaren kuwa Turaki na fita gida ya wuce, kaitsaye part ɗin Baffa ya nufa don zatonsa ko suna can suna breakfast, sai dai ko da yaje duk basa can Baffan ma bai tashi ba, dan haka ya taho side ɗin Maama, time duk sun zauna zasu yi break fast, kallo ɗaya Maama tayi masa tasan baici abinci ba, hakan yasa ta miƙe ta shiga kitchen ta dama masa kunun gyaɗa shap shap ta soya irish, duk da cewan akwai soyayyan irish ɗin amma tasan ba zai ci ba. sai after break fast ɗin ne Maama ta zaunar da Turaki a ɗaki tai masa nasiha sosai akan yanda zai zauna da matar da ba sonta yake ba, ta nusar da shi in har yay haƙuri ya kyautata mata to tabbas zai ga ribar hakan, tunda har yayi biyayya Allah ba zai barsa haka ba. tace,"Me Babban suna ko ni zan iya zaɓa maka Ilham matsayin wacce zaka aura, saboda yarinya ce me hankali da tarbiyya, ita kaɗai ta fita zakka acikin yaran Mai Martaba, to nasan dan ka aureta ba faɗuwa kayi ba ka sami uwar ƴaƴa ta gari. but ni ta yanda akazo da lamarin aurenne ya ɓata min rai, shiyasa duk naji na tsani auren wallahi, to amma ya zamu yi tunda ubangiji ya shirya faruwan hakan tuni. adu'ata Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina tsakaninku, ya kuma baku ikon fahimtar junanku ta yanda ɗaya ba zai cuci ɗaya ba". sannan ta ƙara cewa,"ka dai ji me nace maka ko?". ya ɗaga kansa kawai tabbacin yaji, dan bai jin zai iya magana. suna zaune da ita suna ta hira kiran Boɗejo ya shigo wayarsa, yana kallo yay banza da kiran, da ya ƙara shigowa ya kashe wayan gaba ɗaya yana jan tsaki tare da kwanciya kan gadon Maama. ita dai tana kallonsa amma ko kusa bata yi magana ba, saboda tasan irin ɗacin da yake ji a zuciyarsa, and beside ta lura kamar yana da wata damuwa acan ƙasan ransa, sai dai bai faɗa mata amma tasan duk runtsi zata sa ni. miƙewar Maama kenan zata shiga toilet taji an banko ƙofar ɗakin, kallon wajen da zatai taga Boɗejo a fusace ta shigo, ta bi Turaki dake gadon idonsa a rufe ta ƙarasa wajensa tana ta zazzaga masifa kamar zata bankawa ɗakin wuta. H
🏠