ar tasa tana ɗorawa da faɗin,"ban kiraka da lambata ba saboda nasan ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burgeni, duk uban miskilancinka ka san manyanka".
yaji kamar ya kashe wayar dan mugun haushinta yake ji, amma sai bai yi hakan ba.
a daƙile yace,"ina kwana". tace,"lafiya lau, kun wayi gari lafiya?". yace,"lafiya lau". tace,"yauwa dama zan tambayeka ne ya ka sami Ilham ɗin?".
ta faɗa tana yin ƙasa da murya. yace,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". tace,"ya salam, baka gane nufina ba ne?, ita yarinyar a ya ka sameta nake nufi?". ya ƙara cewa,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?".
Boɗejo taji kamar ta kai masa duka ta cikin wayar, dan in kusa gareta yake ma ba abinda zai hana faruwar hakan. cike da takaici ta ƙara yin ƙasa da murya tana faɗar,"ya zanyi tunda kai farin shiga ne, sai nayi opalli-opalli tukunna zaka gane. dama haka zancen ya zancen budurcinta?, ya ka same shi?, fatan dai ta kawo shi lafiya?".
da ƙosawa yace,"gata ki tambayeta". ya faɗa yana direwa Ilham wayar akan cinyarta.
ta buɗe idonta da ke rufe bacci na so ya ɗauketa, ta kalla wayar da call ke tafiya, da sauri ta ɗau wayar ta saka a kunne tana cewa,"Inna ina yini". Boɗejo tace,"Ilham ni ce, lafiya naji muryarka haka, kuka kika yi?, ko ba kya jin daɗi?, mene matsalar faɗa min, Turaki ne ya gaya miki magana babu daɗi?".
Ilham tace,"a'a". ta faɗa tana sakin sabon kukan shagwaɓa. hankalin Boɗejo a tashe tace,"ni bana son kuka, ki buɗe baki ki min bayani, ko sai na zo?". cikin muryar kuka Ilham tace,"Boɗejo jikina duk ciwo yake min, zazzaɓi ne ajikina. kaina kamar zai cire, kizo dan Allah".
Boɗejo tace,"bawa mara mutuncin wayar". Ilham ta kai hannu ta ɗora masa wayar a kunne, da masifa Boɗejo tace,"daga mugu sai kai Turaki, yanzu yarinyar babu lafiya shine dan tsabar zalunci baka wuce ka kaita asibiti ba?, haka kaga ubanka na yiwa Madina?. gaskiya ban yafe ba sai Allah yay mana sakayya tsakanina da kai. kuma dan uwarka Madina ka amsa min tambayar da nayi maka tun ɗazu, in kuma sai nazo har gidan kaga tsayina inji".
Turaki yay guntun tsaki yace,"ni dai karki ƙara zagar min uwa. amsar tambayarki kuma ta kawo shikenan, karki ƙara kirana ki kira wayarta idan kina son magana da ita, ni ban haɗa komai da damuwa ba so ki barni inji da abinda ya damen".
bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana miƙewa ya bar wajen, Ilham tabi bayansa da kallo tana jin hawaye na sakko mata.
yanzu shikenan irin wannan zaman zasu dinƙa yi da shi?, ana aure dan farin ciki amma tun ba'aje ko ina ba ta fara fuskantar ƙalubale, tana ji ana faɗar tun daga daren farko mace ke fara samun kula da tarairaya daga wajen mijinta amma ita nothing like that, ya sameta a virgin ɗinta amma kamar wadda ta zo masa a fafe, sai faman haɗe rai da kumbura yake ba, duk uban kukan da ta sha daren jiya sannu wannan bata samu ba, balle taimako daga garesa.
and cikin ƙarfin hali ta gyara kanta duk da zafi da raɗaɗin da take ji amma hakan bai sa yaji tausayinta ba a sanda ta tabbatar da yaji uban zafin dake jikinta sanda take kwantar da kanta jikinsa, yanzu shikenan ita wannan soyayyar da take ta kwaɗayi a gidan aure ba zata samu ba kenan?, dama haka illar auren wanda baya sonka yake?.
sai kawai ta kifa kanta a hannun kujerar ta fashe da kuka mai ban tausayi.
daga can masarauta kuwa tuni ko'ina ya ɗauka da batun Gimbiya Ilham ta kai budurcinta gidan miji, kowa kuma sai ya shiga saka kyautukansa acikin wata ƙatuwar kwalla da ke dire a ƙofar turakar Fulani Azima, guɗa kawai kake ji na tashi da tafi ana son barka ana yabon Fulani Azima da tarbiyar da ta bayar.
ƙarfe goma sai ga manyan motoci ƴan ubansu na jiniya a ƙofar gidan Turaki, mota guda biyu ɗauke da hadimai mata, suka fito suka isa inda wata baƙar mota ta ke cike da sassarfa. acikin motar ne aka shiga fito da manya manya coolers na abinci, wasu coolers ɗin abinci ne cikinsu irin na gidan saurata, sai wasu coolers ɗin kuma uban kayan gara ne kamar hauka. dan Gimbiya Ilham tsab zata shekara da su indai ba cin abinci aka dinƙa musu ba.
haka suka dinƙa shiga da coolers ɗin suna fitowa suna kuma ɗibar wasu, sai da suka gama shigar da su tas sannan kuma sai ga ma'aikatan kamfanin Arewa culture Decoration suna shigowa ɗauke da kayan aiki a hannunsu suna nufar can baya inda ƙaton haraba yake wajen filoti guda, a wajen harda swimming pool irin tafkeken nan. suka baje kayan aikinsu kuma cikin ƙanƙanen lokaci suka shiga gyara wajen da decoration irin na gidan sarauta bango zuwa bango, haka ƙasan wajen ma duk an malale shi da uban carpet me taushi an baza uban tumtum sai ka rantse ko fadar mai martaba ake haɗawa.
wata ƙawar Fulani Azima na zuwa taga irin yacca decoration ɗin ya haɗu sai tayi tsaye ta kasa motsi ta saki laɓɓa tana bin wajen da kallo cike da burgewa.
"wow, la'ila ha'illahu, dan Allah aina aka samo waɗan nan masu iya aik