NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 153 of 323

sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri. bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki sai jin hawaye yayi ya sauko masa ba tare da sani ba, daga ƙarshe Inna Falmata ma tayi nata. bayannan kuma aka rarrabawa ƙur'ani da littafan adu'oi. daga nan kuma aka ɗauki amarya akayi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki. Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haɗu da Baffa ba, iyakar kyau dai yayi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango amma sam babu wannan annurin na farin ciki a fuskarsa. Gimbiya Ilham kam tun sanda tai ƙoƙarin kama hannun Turaki taji yanda ya make hannunta taji jikinta yyi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, kace bai taɓa dariya ba a duniyarsa. Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side ɗinta dan bata ma so wasu ƴan bani ka iya ɗin suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo yace zai shigo. hakan ko sai data faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faɗa musu abinda Hajiya Madina tace masa na cewar basa nan, a same su acan masarautar. to haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura yayi dole, dan ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast dan shima irin Turaki ne bai iya cin abincin restaurant ba. kuma a ranar da daddare Boɗejo tazo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinyesu saboda masifa akan Turaki sai yaje Dinner, har da cewa,"aini Madina ban san ke fitinanniya bace sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haɗari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata aniyarki ta koma miki". Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, har ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta. Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba tace,"wuce motar Nasiruddeen na waje suyi maka rakiya, in an hana ƙawayenka zuwa ai kana da ƴan'uwa". sannan ta juya kan su Zaytuna tace,"ku kuma ku wuce muje, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum ba ta da ƙashi. to kuyi gaba muje ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure dan naji ana ƙishin ɗin haka, in ban ba'asa naje na bankawa ƴar mutane wuta ba". haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, MC ma da yay batun liƙi sai Khalil ne ya fito ya wakilce shi ya watsa bandir ɗin ƴan 500 har guda biyu. kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Gimbiya Ilham kam da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba ita kanta ba sonta yake ba. bata tabbatr da hakan ba sai after an tashi daga dinner sunzo shigo mota yace,"ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke akayi. idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren to kinyi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki ba shirmen so irin naki ba. and again ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki dan already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin". wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan Gimbiya Aisha. washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole taje, shima kuma taga abinda yafi na jiya a wurin Turaki, don opalli ya nuna kowa ba auren so suka yi ba. ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiɗe haka taji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate ɗin su Turaki, daga gidansa zuwa nasu babu nisa, gidan ya gaji da haɗuwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba. shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar ɗanta za'a kai babu abinda zaisa taje. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira tai banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faɗa masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame. acan gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita Fulanin ba so take ba. haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da adu'a sannan suka baro su. kamar yanda sunnah ta koyar Turaki suka yi nafila tare da matarsa, bayan sun idar ya kama kanta yayi adu'a, sannan ya gabatar mata da abinci. ita taci dan shi bai iya cin komai ba, sai bayan da ta kammala ya tashi ya bar ɗakin ya wuce parlo ya zauna, tunda ya fito kuma yake ta tunanin Fillo, Allah kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa. ya jima zaune anan daga baya ya tuna fa
🏠