NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 152 of 323

Baffa ya kira wayata Allah ba zan ɗaga ba. dan dana hau whatsapp naga Marfu'a(Yayar Ilham wadda itace ta farko a ƴaƴansa mata), ta ɗora invitation card na dinner da cocktail ranar saturday da sunday". Hajiya Madina da har yanzu ta ke a fusace tace,"sa ji uwar kunya kuwa, dan gobe ma zamu bar ƙasar ni da shi, sai su nemi uban da zai yi replacing angon, ai insha'Allahu duniya sai ta gane auren cusa kaine, ango ba so yake ba". tana kallon Zaytuna tace,"kema uwar rawar ladabi da biyayya, Allah sa inga kin shiga lamarin bikinsu kiga asalin ɓacin raina". ta faɗa tana maida hannunta kan goshin Turaki da take jin zafin kan na ratsa fatar hannunta, a lokacin Turaki ya buɗe idonsa yana kallonta muryarsa a raunane yace,"Maama da gaske ne kun fito da yarinyar nan ta ɓata?". ta ke Hajiya Madina ta fashe da kuka tace,"ko dan wannnan dalilin tashin hankalin da nake ji ai yaci ace a tsayar da maganar auren ɗana?. banda ma dai Baffan Baffa ne ai sai ya miƙe tsaye yace ko za'ai a bari aga yarinyar mutane dana fita ta ɓatar tukunna, amma har shine yana min tsawa yana cewa babu ruwan auren ɗansa da ɓatan yarinya. yanzu fisabillah me Kakar yarinyar nan zata ɗauke ni?, ba sai su koma min kallon matar banza ba azzaluma na ɓatar musu da ƴarsu nazo ina shagalin bikin ɗa, wallahi ni dai sanyin Baffanku ba komai bane fa ce cutarwa". ya rumtse idonsa ya buɗe tukunna ya ƙara cewa,"garin ya akayi ta ɓata?". nan ta kwashe labarin komai ta ba shi. "to su police ɗin suna cewa wai sun fi tunanin kidnappers, ka faɗa min Hammah idan kidnappers ne tuni basu kira waya ba, amma fa shiru shiru har zuwa yau babu wanda ya kira waya, ko'ina an duba babu ita kamar ɓacewar aljani, har yanzu dana sanin fita nake da yarinyar nan, dan Kakarta da wanda zata aura zasu ga kamar da gangan hakan ya faru, kasan zuciya bata da ƙashi". ta faɗa tana kuka sosai. Idonsa a lumshe yace,"ki daina kuka Maama, insha'Allah an kusa a ganta". dukansu suka amsa da amin. sannan ya miƙe yace,"zanje in kwanta, kaina yana ciwo sosai". tace,"tafi ɗakina, kuma ka cire damuwar komai a ranka. yanda kake da gatanka zakai auren gata nan da wani lokaci insha'Allah. Dikko ne yay sirika ba Madina ba". Turaki ya wuce ya hau upstairs yana jinsa kamar ba shi ba, yana jin komai kamar a mafarki. kuma kafin ya kwanta sai da ya kira Bello ya sanar masa, tsaban shock Bello ashar ya ɗura a lokacin, har bai san sanda yay formating document da yake haɗawa ba. kuma Turaki bai jira cewarsa ba ya kashe wayarsa. *Washe gari, Juma'a, Masarautar Kaltungo, Ƙarfe Ɗaya da rabi na rana.* ana idar da sallar juma'a a masallacin aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki dubu ɗari uku. ɗaurin auren daya samu halarta manya manyan ƙusoshin ƙasar nan, dan duk wanda yake da faɗa aji a ƙasar nigeria da wajenta sai da Mai Martaba ya gayyace shi ɗaurin auren, kuma cikinsu babu wanda ya turo wakilinsa duk da kansu suka zo. duk girman masallacin fada sai da mutane suka cika shi taf, ciki da wajensa babu masaka tsinke, ango dai yana tare da mahaifinsa dan babu abokinsa ko ɗaya, Bello ma da yace zai biyo jirgin safe Maama ce tayi sai taci ubansa matsawar yazo. ango dai kamar ba ango ba dan fuskarsa babu walwala, ga shi dai acikin mutane kuma inda ake ɗaura aurensa, amma hankalinsa gaba ɗaya na can kan Fillo, ina take? da kuma halin da take ciki. bayan gama ɗaurin aure aka tafi reception, inda ɗumbin jama'a suka ci sukai hani'an, dan babu wanda zai ce bai goge haƙori da naman kaza ba. ana dawowa daga reception kuma aka koma can gidan mai martaba, cikin masarauta kenan, duk ta yanda Turaki yaso ya zame ya zille ya tafi gida abin yaci tura, dan Baffa na riƙe da hannunsa sai nunawa jama'arsa shi yake cike da tsantsar farin cikin da ba zai misaltu ba, shi kansa Turakin sai da yaji tausayin mahaifinsa, bakin Baffa sam yaƙi rufuwa, da zarar sun gaisa da mutum zai nuna masa Turaki yace,"shine babban ɗan nawa, asa masa albarka". haka ya dinƙa yawo da shi yana nunawa jama'arsa da jama'ar mai martaba. Turaki kam ya koma kamar yaro, bai sami salama ba sai da suka dawo fada, dan iyakar wanda suka dawo fadan duk ƴan'uwa ne, yana jin wayarsa na ta buga ringing daga Maama sai dai babu ta yanda za'ai ya ɗauka. acikin fadar Mai Martaba ne zaune daga tsakiya akan royal chair, sai Hakimi a kusa da shi ta hannun dama, sai Baffa a kusa da shi ta hannun hagu, sannan Falmata a kusa da shi sai Boɗejo daga kusa da hakimi ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba me ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufe haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje. Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, tayi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma
🏠