NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 151 of 323

lƙali Dikko dan ka sakeni ba zanji wani ɗar acikin raina ba. so barazanar sakinka ba ita zata sa in sauka akan bakana ba, aure in kaga anyi tabbas to da amincewar yarona". tana gama faɗar haka tace da Turaki,"Hammah ta shi muje, inga wanda ya isa yayi maka auren dole, ko da kai yaro ne ba'a isa ba balle kuma da hankalinka". cikin ɗaga murya Baffa yace,"Madina wai me yasa baki da mutumci ne, auren nan na faɗa miki mahaifiyata ce ta shirya shi, shine har kike so in ta ke umarninta?". Maama ta taɓe baki tace,"cikin ku huɗu da Allah ya bata kaf ɗinku wa aka yiwa auren dole?, kuma jikoki nawa gareta?, sauran ƴaƴan nata rasa ƴaƴa suka yi da ba zata yiwa ƴaƴansu ba sai nawa ɗan da aka sawa ido dan an gansa yafi kowa haƙuri, yafi kowa biyayya. to daɗin abinda ƙasa bata cika bakina ba balle a cuce shi...Me Babban suna ta shi ka ji, aure sai in bana numfashi, kaf ƴaƴana ba wanda aka isa aiwa auren dole". Turaki ya riƙe kansa da ke neman barazanar fashewa ya riƙo hannun Maama yace,"zan aureta Maama, zanyi auren na amince. adu'a kawai zaki yi min". ƙyam idonta ya tsaya akansa tana hango tsananin ƙarfin halin dake tare da shi wajen ganin ya furta hakan. ta maida kallonta kan Baffa tana kallonsa, ko a jikinsa, bai damu da halin da ɗansa zai shiga ba ma?. ta ɗauke kanta tace,"babu komai akwai Allah, idan ma saboda wata manufa aka haɗa auren nan Allah ya saka maka ya kareka daga sharrin mugun mutum...and ko banza ƴarsu ce zata wahala wallahi tunda babu sonta a zuciyar mijinta. kuma sai in dai bai ga wadda yake so ba, abu da Allah ya halasta masa auren mace huɗu, yana ganin wadda yake so zan ɗaura masa aure da ita wallahi kuma banga wanda ya isa ya hana faruwar hakan ba, in masa auren gatan da ko ƴaƴan masu mulkin ma ba'a yi musu". taja hannunsa,"tashi muje Allah yayi maka albarka ya baka ladan biyayya, idan ba me tarbiya ba waye ma zai yarda da wannan kalar cutarwar". ta mayar da kallonta kan Baffa tana cewa,"Allah ya bawa mutum ƴaƴa amma baida burin da ya wuci ya ƙuntata musu, duk wai ace mutum shi yana bin maganar manyansa, Allah na tuba yayye ba iyaye ba har sunsa na baƙantawa ɗan cikina, ita kanta yarinyar nasan ba kai tsaye akai komai ba sai da ubanta yaji ta bakinta, amma kai wai me biyayyar yayye ka yanke hukunci kanka tsaye, sai anyi magana ka dafe ƙirji kana nishi hawan jininka zai tashi, inga me zaman jinyarka yau". tana gama faɗar hakan ta kama hannun Turaki, kamar wani ƙaramin yaro haka ta ja shi suka fita daga parlon Baffa na bin bayanta da kallo, ko kaɗan bai mamakinta ba dan dama yasan za'a rina, in ace dai Turakin yana son yarinyar yasan babu abinda zata ce balle har ta tada jijiyar wuya haka, amma akan hakan yau ɗaya har tana faɗar wai yana ƙuntatawa ƴaƴansa, when akai haka?. acan parlonta ta tarar da duka yaranta zaune sunyi jungum-jungum, Khalil da Nihal da Zaytuna, Samha da Sameer basa nan dan basu dawo daga ƙasar da suka tafi ƙulla mugun nufinsu ba. ta shigo tana ta masifa, Khalil ma yay tsaki yace,"gaskiya, gaskiya abinda Boɗejo tayi bata kyautaba sam. wannan wane irin aure ne tsakani da Allah?". Nihal ma na turo baki tace,"yanzu dan Allah duk burin da muka ci akan auren Hammah sai azo mana da shi a irin haka?, shirin me muka yi tsakani da Allah, ni wallahi wannan tsohuwar dama ta mutu". Zaytuna dai ba tace komai ba illa kallon Turaki da take tayi ƙwayar idonsa kamar ba nasa ba. Nihal ta miƙe ta isa kusa da shi tana ɗora hannunta akan nasa tace,"Hammah kai kace kana son auren da har tai mana wannan shirmen?". bai ce komai ba, lokacin Hajiya Madina ta ƙaraso wajen riƙe da cup a hannunta da ruwan sanyi aciki, ta zauna tana tallafo kan Turaki ta bashi ruwan ya sha. bayan ya sha ta ajiye cup ɗin tana faɗin,"suje can suyi bikinsu su kaɗai, ni da ƴaƴana dai babu mai zuwa, wanda ya fasa cewa ina baƙinciki ba ɗan halak ba ne. kuma kaima ana ɗaura auren kayo kwana ka dawo gida". Nihal na matsar ƙwalla tace,"yanzu Maama sai kace bamu da gata sai ayi bikin Hamman'mu a haka babu shagalin komai?, duk fa ina ta cewa friends ina idan Hammanmu zai yi aure kowa zan gayyace shi. shi Baffan dan tana babarsa kawai kuma sai ya wani kama biyewa rikicin tsufanta, ni taja ma wallahi har Ilham ɗin na tsaneta, ƙilan ma harda wannan munafukar Babar tata aka haɗa baki". Hajiya Madina tace,"kwantar da hankalinki Nihal, shi da yake da ikon auran mata har huɗu, Allah ya kaimu nan da ranar da zai hango zaɓin ransa. anan za'aga inda ake aure, lokacin zamu yi namu shagalin bikin akan matar so, kuma ko a yanzu ina da arziƙin da zan iya yin bikin da zaici uwar nasu acikin kwana biyu cal, sai dai ba zan ɓarnatar da dukiyata ba akan auren matar shige". ta kalli Khalil tace,"kaima uban ƴan ladabi da biyayya, ka sake nai kiciɓis da kai zaka je wurin ɗaurin aure gobe babu abinda zai hanani sa maka kafa na fyaɗeka a ƙasa, in taka ƙafar in karya banza". Nihal tace,"dama ni wallahi babu inda zanje dan ɓuya ma zanyi ko
🏠