NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 150 of 323

nar na maimaituwa acikin kansa. bai san sanda ya furta,"aure kuma Baffa?, dama ana irin wannan auren?, Baffa aure ban shirya ba kuma bada yarinyar da nake so ba?". kamin Baffa yay magana Maama ta buɗe fuskarta da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye tace,"kaji ai zancen da nake maka ba. yanzu tsakani da Allah idan har aka yi masa hakan an masa adalci kenan?, ina aka taɓa yiwa mutum aure ma bai san da zancen ba sai kace wani gantalalle, and beside ita kanta matar da aka lalaƙa masa bai ce yana sonta ba, haba Baffa ka dawo cikin hayyacinka mana, ɗanmu fa da gatansa taya za'a ce za'a masa irin wannan auren da ko mara gatan ma ba'a yiwa irinsa, abar ta batun ma ni a sanar da ni tunda dama ni ba kowa bace, amma dai at first ai ya kamata shi a sanar da shi in ya amince sannan, idan ma kuma dolen ake so ayi masa sai a sanar da shi tunda wuri ba wai sai a ƙurewar lokaci irin haka ba, kawai tsakani da Allah dan anga yaro yana da biyayya sai ake zaluntarsa duk ta inda aka so, wannan ba daidai bane wallahi, kuma Allah ko kotu muka je sai an ƙwatarwa ɗana hakkinsa". Baffa ya ɗago ido ya kalleta da kyau yace,"you are free to go there Madina, ki shigar da ƙara gaba da kotu kinji. abu ɗaya kawai nake so in sanar miki shine babu mahaluƙin da ya isa ya hana wannan auren. duk fitinar da zaki tayar wallahi sai dai ta ƙare miki ke ɗaya, wannan batu na aure magana ce ta mahaifiyata, saboda haka babu uban da ya isa ya hana, ɗa nawa ne ba na wani ba, kuma tun a jiya na faɗa miki muddin kika nemi ki ɗaga min hankalin ki tada fitina akan wannan batun, to tabbas zai yanke tsatstsauran hukunci akanki". Hajiya Madina ta ƙara fashewa da kuka sosai. Turaki dai na zaune kamar gunki sai kallon Baffa yake kamar yana kallon sabon mutum. sai da Hajiya Madina taci kukanta sosai tukunna ta ɗago tace,"muddin ina raye, muddin da lafiyata babu wanda ya isa yaywa ɗana auren dole, sai kace wata mace. abunda ko ada can ba'a yi ba, idan ma auren dolen ake so ayi masa a fara faɗa masa mana, ba wai aje a ɗauko ɗiyar matar da ba ƙaunarsa ta ke ba a haɗasa da ita". sai tai ta ɗauke idonta daga kan Baffa ta maida kan Turaki, tasa hannu ta ɗago fuskarsa daga saman cinyarta da ya kwantar, ta kalla cikin idonsa tana ganin yacca ƙwayar ta sauya kamar bata shi ba, taji wani bala'in tausayinsa ya kama shi, yana da mugun haƙuri kuma yana da tsananin biyayya ga iyaye ko da ace zai cutu, tana kallonsa tace,"kana da ni Hammah, ni mahaifiyarka ce da ba zan iya zuba ido naga ana cutarka ba, saboda haka ka faɗa min zaka iya auren Ilham ko ba zaka iya ba?, ka shiryawa wannan auren ko baka shirya masa ba?". Turaki ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana jin wani abu na taso masa daga ƙasan zuciyarsa, dama har yanzu shi under 20years ne shi bai sani ba?, dan a ganinsa yaron ma da yake 20years ba za'ace zaa masa irin wannan auren ba, me yasa Baffa?, me yasa zai biyewa rikicin tsufan Boɗejo?, ofcourse baya san wannan auren, kuma ko da ace zai iya so ɗin kukan Maama kaɗai na iya sa shi ya ƙetare umarnin Baffa da bai taɓa ƙetarewa ba tunda aka haife shi, to amma sai dai Baffan ya karya shi da furucisa guda ɗaya, ya sagar da shi daga duk abinda yay niyyar yi. dan shi tanadin da yake Baffa na gama zancensa daga nan sai ya miƙe yaje ya sami Ilham ɗin yay mata cin zarafin da ko da gawarsa ba zata yarda a ɗaura mata aure ba, to sai dai a yanzu Baffa ya gama da shi tunda har yake batun zai ɗauki tsatstsauran mataki kan Maama, bijirewar tasa ba zata haifar da komai ba sai ɗa mara ido. dan haka zai amince ya auri yarinyar, amma ya tabbata da kanta zata bar gidan, dan ba zata taɓa samun fuskar zama da shi ba, ya sa ni ita ta amince tana sonsa tunda har aka yarda da auren, but she will regret. yanzu baida lokacin yi mata komai saboda ba abinda ke gabansa ba kenan, neman Fillo ne a gabansa yanzu. yasa hannu ya dafe kansa yana jin zafin dake kansa na ratsawa a jikinsa. ya buɗe ido ya kalli Hajiya Madina da har yanzu hannunta ke kan goshinsa tana kallonsa kamar ba zata ƙifta ba. ta ƙara ce masa,"karka cuci kanka, sai in har ka yarda za'ai auren nan, idan baka yarda ba yanzu ka miƙe in kai ƙara gaban Babban Alƙali, dan yau daga uban har ƴaƴan sai na maka su a kotu dan ba zan ci gaba da zuba ido ina kallo ana zaluntar min kai ba wallahi, ko zaka yi aure ba'a cikin shiri ba na yarda amma sai in wadda kake so". bata ma san sanda tai furucin daga uban har ƴaƴan ba. Turaki ya kalla mahaifinsa yace,"Baffa ni fa ba yaro ba ne". Baffa yay saurin ɗaga masa hannu yace,"sanin hakan yasa muka haɗa aurenka da ƴar'uwarka, ka shirya gobe after salatul juma'a za'a ɗaura aurenka. haka muka zauna muka yanke ni da mahaifiyata da ƴan'uwana, and that is our final decision, idan har kuma ka bijire min to tabbas zan sallamaka a cikin ƴaƴana sannan in sallami itama Babar taka dake ɗaure maka gindi". Hajiya Madina tayi hanzarin miƙewa daga kan kujera tace,"in har zan cika alƙawarin dana ɗauka na riƙe yaron nan bisa amana, to A
🏠