NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 323

cewa,"you mean ita ɗaya zata tafi?". "kamar dai hakan. Amma ƙila Nabla ta bita kasan ita amara ƙirjin biki ce". Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihu. Yana cikin saka takalminsa Inna Wuro ta dawo parlon, tayi kasaƙe tana kallon Yusra dake yafa ɗan yalolon mayafinta a kafaɗa. "kuma fita zaki yi a haka?". Inna Wuro ta tambayeta tana kuma ƙarewa shigar jikinta kallo. Yusra ta jefa cingom bakinta ta amsa mata."yesss mun koma school yau...na manta ma ban faɗa miki ba, ko da yake jiyan na shigo ai na tarar kinyi bacci, an kafe mana result and i don't have any problem". Inna Wuro tayi mata wani kallo, kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta juya ta dakatar da Yusuf dake shirin fita tana ce masa. "wai kuwa kana kallon a yanda yarinyar nan zata fita shine ba zaka tsawatar mata ba, kana babba amma kai sam baka san abinda ya kamata ba, da kai da hoto duka ɗaya. Kalla fa gantalallan ɗinkin dake jikinta, wuya duk a buɗe kusan rabin nono a waje, amma a haka ta ke ikirarin zata fita har makaranta salon ta jawa Amadu zagi". Sam Yusuf bai lura ma da kayan dake jikin Yusra ba balle ɗinkin, sai bayan daya gama saka takalmin ya kalleta, sai aikin zumɓura baki gaba ta ke yi tana ƙunƙuni, da gaskiyar Inna Wuro dole tace gantalallan ɗinki, shi a wurinsa ma wannan ɗinkin asarar kaya ne. "ke karki kuskura ki fita a haka". Ta ƙara kumbura kamar zatai kuka ta ke nuna kayan jikin nata. "fisabilillahi me wannan ɗinkin yay, ni gaskiya babu abunda zan sauya tunda ko Ammi ta ganni da su kuma bata ce komai ba". Inna Wuro tace,"yo wannan Uwar taki sanin ya kamata tayi da zata hanaki fita tsirara". Yusuf ya wurga ma ta wani mugun kallo. "yaushe na fara wasa da ke? Ki wuce ki sauya su babu inda zaki fita a haka". Yana rufe baki Aliyu ya miƙe daga kwancen da yake, shima yana mata wani banzan kallo irin na baya son raini yace,"Uban waye sa'anki anan da ana yi miki magana kina ke ba haka ba. Kin wuce kinyi abunda akace ko sai na saka miki ƙafa". Yusra ta fashe da kuka tana bige-bigen ƙafa a ƙasa, ta wuce Inna Wuro tana faɗin ba zata ƙara zuwa site ɗinta ba sai dai idan sauya mata suna akayi. Inna Wuro ta bita da cewa,"ai dama bani ke gayyato ki ba, ke kike kawo kanki". Ta dubi Yusuf tace,"yau zaka koma kano ɗin?". Yace,"may be". Ta taɓe baki tai ciki abinta. "kai kasan abunda kace, ni dai nafi ƙarfin zagi da yaren bature. Na ɗauka yau ɗin zaka tafi na baka saƙo ka kaiwa Nuratu". Jin ta ambaci abar ƙaunarsa yay saurin cewa,"ki bada yau zan koma". Tace,"na fasa ai". Sannan ta dubi Aliyu tace,"kai kuma ɗan zaman kashe wando idan zaka tafi karka bar min tv a kunne ka kashe min". Yusuf na fitowa yay part ɗin Ammi mahaifiyarsa, har ya shiga parlon sai ya fito sakamakon murɗawa da cikinsa yay, ya koma part ɗin Hajiya Falmata da suke kira da Umma. Step sisters ɗinsa ya tarar a parlon su biyu, Salma da Kursum. Ya ƙarasa shiga ciki ya zauna kan kujera suka gaishe shi, Salma ta miƙe tana faɗin,"bari na kira Umman". Tare suka dawo da ita, Salma na gaba ita tana baya da waya kare a kunnenta tana bada sallahun da za'a taho mata da shi daga kano. "yanzu ka shigo?". Ya kalli Umman da tai masa magana yace,"na ɗan jima ina wajen Inna Wuro". Tace da shi,"aiko ga breakfast ɗinka can ina ga ma yay sanyi". Ta kalli Kursum tace,"je kiyi warming abincin Yayanku". Within 3mints Kursum ta dawo ta janyo center table ta ɗora plate ɗin abincin a kai. Yana ci suna magana da Umma, tana sanar masa tafiyar Nameer da yay a ɗazu, ya samu aiki a wani company dake can taraba state. Bayan ya sauke spoon daga bakinsa yace,"Nameer ɗin yace min Daddy bai yarda da zuwansa can ba". tace,"da ƙyar Alhaji Saleh yay conviecing ɗinsa ai, shine Nameer ɗin ya wuce yau da wuri". "to Allah ya taimaka ya bada sa'a". Umma ta amsa da amin. Sauri sauri Yusuf ke yi wajen cin abincin dan gaba ɗaya hankalinsa na can wurin Ammi, fatansa ma Allah sa Yusrah bata faɗa mata ya shigo ba. Yana gamawa ya miƙe yana yiwa Umma Sallama. Ta tambaye shi,"when zaka koma?". Yace,"may be da yamma ko kuma gobe". Umma tace,"Nuratu tai min complain jiya da mukai waya...". Tun Umma bata ƙarasa maganar ba yay murmushi tare da cewan,"tare zamu tafi insha'Allahu". Itama tai murmushin tana cewa,"sai ka dinga haƙuri da rigimar Nuratu, musamman yanzu da ba ita kaɗai bace". Fitowarsa daga part ɗin Umma na Ammi ya wuce, a parlo ya tarar da ita suna magana ita da yaranta, ya ƙaraso ciki kansa a ƙasa gabansa sai faɗuwa yake. Ammi kam ko iskar da ta ɗebo shi ta kawo shi bata kalla ba, maid ɗin dake riƙe da trolley ɗin Ammi ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa. Sai da ya bari Ammi ta gama magana da yaranta sannan ya gaisheta, tai banza da shi tamkar bata ji shi ba. ta zo fita ne ma ta tuna da ƙararsa da Yusrah ta kawo mata sannan ta dakata daga fitan, ta dawo tai tsaye akansa. "idan ka wulaƙanta ni nayi maka shiru ba zan yarda ka dinga saka min yara kuka ba ka
🏠