NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 149 of 323

ce". Turaki yasa hannu ya shafa fuskarsa tukunna ya yunƙura zai miƙe sai yaji Yami da Kaka na maimaita kusan magana mai shigen wacca yaji ɗazu da yana shigowa. "ashe kuma lokaci yazo to ubangiji Allah ya sanya alkhairi". ana cikin wannan halin suke faɗar kalmar Allah ya sanya alkhairi!, to ko dai duk tsananin tashin hankali ne yasa kowa ya fita a hayyacinsa har yake faɗar abinda bai kamata ba. sai da ya isa bakin ƙofa sannan ya juyo yana kallon Kaka yace,"kuma babu gidan wasu ƴan'uwa da zata iya zuwa can?". Kaka tace,"babu, duk inda ya kamaci ace an bincika duk an duba. dan shi wanda ma zai aureta da kansa yaje can dangin mahaifinta ya duba, kwanansa ma biyu acan ɗin, amma ko da ya dawo yace wallahi bata can". Kaka ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Turaki ya dinga kallonta kafin ya fice daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. ya wuce yana maimaiata kalmar wanda zata aura cikin ransa. daga nan kai tsaye ɗakin Maama ya wuce, lokacin da ya shiga zaune ya sameta a gefen gado ta zuba uban tagumi. har ya cire takalmansa ya shigo ya zauna kusa da ita bata sani ba, sai da ya janye hannun da tayi tagumi tukunna tai firgigit ta ɗago tana kallonsa. tana ɗago ido ta gansa sai ta fashe da kuka tare da kifa kanta a kafaɗarsa. ya rumtse idonsa sosai yana jin kukan nata na taɓa zuciyarsa tana ƙara matsewa da damuwar da take ciki, yasa hannu a kanta yana cewa,"innalillahi wa'inna ialihi raji'un, Maama whats wrong?, kukan me kike Maama?". ya faɗa dan yana so ya ƙara tabbatar da komai daga bakinta, amma da mamakinsa sai gani yay ta ɗago tana yi masa zancen da ya ɗaure masa kai matuƙa ya kuma rasa ina ta nufa. "Me Babban suna ka taɓa ce musu kana sonta ne?, ko kuma ita tace maka tana sonka ne da har ka amince musu?, yanzu shikenan ni ban isa ba, ban isa ai magana da ni akan abinda ya shafi rayuwar ɗana ba?, kuma a rasa a lokacin da zaa shirya bikinka sai lokacin da akaga ina cikin tashin hankali, me Fulani Azima ta shirya?". sai kukanta ya ƙaru sosai hakan yasa tayi shiru tana ƙara kwantar da kanta a kafaɗarsa. "Maama ban fahimci abinda kike son cewa ba, me ya faru?". sai ta ɗago da kanta ta kalle shi sosai, a ƙwayar idonsa ta gasgata cewa bai san duk abinda ke faruwa ba. saboda haka sai ta miƙe tsaye ta kamo hannunsa tace,"ka muje ka faɗawa Baffa da gatanka, kai ba maraya ba ne, dan haka ba irin wannan shirin kayi ba, ba irin wannan tanadin ka yiwa aurenka ba". bai iya cewa komai ba har suka fita daga ɗakinta suka bar part dinta suka nufa na Baffa still tana riƙe da hannunsa. suna shiga suka tarar da Baffa zaune a parlo yana kallon news ya ɗora hannunsa akan tumtum ɗin dake kusa da shi. Hajiya Madina ta nemi kujera ta zauna tana rufe fuskarta da duka hannunta biyu, Allah ɗaya yasan abinda take ji a zuciyarta, kuma ta lura in bata yi da gaske ba zuciyartata na gab da bugawa. Turaki ya kalleta ya kalli Baffa wanda ko juyowa bai yi ba ya kalli inda Maama take, dan haka abin sai ya ɗaure masa kai ya dinƙa kallon su 1 by 1, abinda zai iya rantsewa bai taɓa gani ba a tsakaninsu ba kenan tsawon rayuwarsa, fushi da junansu dai, shi ko irin wannan saɓanin da ake cewa ana samu tsakanin Mata da Miji ma bai taɓa gani ba ko da a fuskokinsu. to me yake faruwa ayau ɗin?, duk akan ɓatan yarinyar ne ko ya?, me Maama take son faɗa masa ne ɗazu da bai fahimta ba?. sai ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya zauna daga gefen kujerar da Maama take, ya kai hannunsa ya ɗora akan yatsun ƙafarta yana jin wani abu na tsarga masa. tunaninsa ɗaya ne me ya saka masa Maama zubar da hawaye irin haka?. bai san lokacin da ya haɗe yatsunsa ba ya dunƙule, banda akan ƙafar Maama yake babu abinda zai hana shi nausar koma menene. sai da ya rufe idonsa ya buɗe tukunna ya buɗe baki yace,"Barka da Rana Baffa". a sannan ne Baffa ya gyara zamansa yana kallonsa yace,"yaushe ka sauka?". yana kallon mahaifin nasa da son gano abinda ke faruwa yace,"ban jima ba. na baro Bellon acan zai ƙarasa projects na jiya da kayi magana". tun ajiya da suka yi waya da Khalil yaso ya taho amma sai Baffa ya kirasa yace zai yi representing nasa a wani program da yake da shi da safe, dalilin da yasa ya zauna ɗin kenan, kuma ayau ɗin ko Bello bai san ya taho ba saboda daga can airpot yayi. Baffa yace,"an dawo lafiya?". yace,"lafiya lau". shi dai jikinsa duk a sanyaye yake, musamman da har yanzu yaji Maama na kuka kuma Baffa ko kallon inda take zaunen bai yi ba. baya so yayi saurin interfering shi yasa yay shiru, amma sai yaji ba zai iya jurar jin kukan Maama ba, hakan yasa idonsa a ƙasa yace. "Baffa da akwai wata matsala ne?". Baffan yace,"ita Babar taka bata faɗa maka ba ne?". Turaki ya ɗago ido ya kalli Hajiya Madina sannan ya kwantar da kansa gefen gwiwarta yace,"a'a, bamu zauna da ita ba tukunna". Baffa yace,"to gobe bayan an idar da sallar juma'a insha'Allahu za'a ɗaura maka aure, kai da ƴar uwarka Ilham, dan haka sai ka zama alert". da wani bala'in shock Turaki ke kallon Baffa, maga
🏠