ɗin, musamman da naga up to now baya hawan motar. amma mutumin da yake kwana yana sallah har sai gari ya waye sannan ya rumtsa, mutumin da yake driving yana sauraron karatun alƙur'ani yana bi, mutumin da baya rabo da ambaton Allah a bakinsa, mutumin da common magana ɗaya yayi sai ya ambaci Allah, to ki faɗa min ta ya ba zai kuɓuta daga haɗarinmu ba?, taya ba zai kuɓuta daga sharrinmu ba?, ai muma wasa muke, iyakar kuɗin da muka ɓarnatar ya kamata zuwa yanzu ace mun haƙura kawai, mu fahimci cewar Turaki yafi ƙarfinmu dan yana tare da kulawar ubangijinsa".
Samha tace,"idan kai ka haƙura ni dai ba zan haƙura ba, dole ne ma sai na ƙwaci soyayyar mahaifiyata, dole ne ma sai na ƙwatarma kaina hakki. ka duba kaga banda mota guda ɗaya da kuma fili guda ɗaya me Baffa ya taɓa mallaka mana?. amma Zaytuna motarta biyu, bayan fili har gida tana da shi, Turaki kuwa an handame duk wata kadara an basa, komai Baffa yay yunƙurin yi mana sai Maama tace shi ya kamata a bawa saboda shine Babba, ko kuma tace ai su basu da uwa sai kace mune muka sa uwar tasu ta gudu".
Shiru ya ratsa kafin Sameer yace,"to yanzu what next kike ganin zamu yi?".
tace,"akwai wani dodo anan ƙasar, na faɗa masa zan basa kwangilar kisan mutum biyu, yace min zan ba shi 20ML, nace masa 10ML zan ba shi, da ƙyar dai muka ƙarƙare a 15ML, dan haka zan sayar da motata ɗaya da kuma sabon filin da Maama ta bani, sai muga abin yi".
Sameer yace,"hakan yayi".
daga haka ta wuce ciki ta barshi anan parlo.
*Gombe.*
a cikin parlon na Kaka, tana zaune ta zabga tagumi tana jan carbi, sai Yami ma a gefe ta zabga nata uban tagumin, sai Maijidda dake kwance akan ledar ɗakin, ba bacci take yi ba idonta ne kawai a rufe.
dukkansu kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka shaida bala'in tashin hankalin da suke ciki, duk sun rame sosai. tun a daren jiya Amir ya ƙara kai kuɗin da kidnappers suka nema amma shiru har safiyar yau babu wani labari na dawowar Fillo, tun kiran da suka yi na cewar sun ɗauki kuɗin zasu yi abinda ya dace to basu ƙara kira ba, haka su Kaka suka yi kwanan zaune kamar yanda Amir yay daga can gidansu, amma shiru-shiru babu wani bayani.
to haka yau ɗinma tun 11 na rana Hajiya Madina tayo musu aiken abinci amma sun kasa ci. dan a inda Ɗausiyya ta ajiye flask ɗin tun ɗazu yana nan a inda yake babu wanda ya taɓa shi.
Yami ce tace,"Ƙawata ki ɗanci abincin nan ko loma biyu ce dan Allah".
Kaka ma tace,"ke ya kamata kici tunda kina da matsalar ulcer".
Kaka ta dubi Maijidda tace,"tashi ki zuba abincin nan kici".
bata buɗe idonta ba hawayen daya taru aciki ya sauko tace,"ba zan iya ci ba Kaka".
dai-dai nan suka ga an ɗaga laben ɗakin, da sauri suka waiga kusan a tare suna kallon ƙofar, da fatansu ace Fillo zasu gani, but sai saɓanin hakan suka gani, sai suka tsaya suna kallonsa sun kasa ɗauke idonsu akansa. kamar yadda shima ɗin bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya.
kallon su yake yana so ya hango maganar da Khalil ya faɗa masa a fuskokinsu, babu wanda yasan da dawowarsa hatta kuwa Maama, dan ko driver bai kira yaje ɗaukansa ba, daga airpot napep kawai ya nema ya hau ya taho.
ta gate ɗin ma'aikatan gidan aka sauke shi, kuma yana shigowa straight ɗakin Kaka yayo bai ko bi ta kan ma'aikatan dake gaishe shi ba, dan wata magana ma da yaji suna yi ta Allah ya sanya alkhairi duk bai fahimta ba.
Kaka ta ɗauke idonta akansa tana cewa,"bismillah me Babban suna". baya jin zai iya ɗaga ƙafafunsa daga wurin da yake ya shigar da ita cikin ɗakin, dan ya riga ya gama samun amsar tambayarsa a fuskarsu, ta tabbata matarsa ta ɓata, har tsayin lokaci ba'a ganta ba.
kuma sai ka lura sosai zaka hango uban hakin da yake yi tamkar wanda ya taho a guje tun daga El-Salvador.
Yami ta yunƙura ta miƙe ta ɗauko darduman sallah ta shimfiɗa tana cewa,"bismillah ga wuri". Turaki ya ziro daguwar ƙafarsa ciki yana takawa tamkar wanda bai da jini a jikinsa.
ya zauna hoton Fillo na haska masa acikin idonsa, tunaninsa ya katse sanda Kaka tace,"ina yini, an sauka lafiya?".
Yami ma ta gaishe shi sannan ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya maganar ba yace,"lafiya lau". sai kuma duk sauran maganar tasa ta katse ya kasa faɗin komai.
sai da Yami tace,"muna godiya da kulawarku, Allah ya bada lada". shirunta ya haɗe da fashewar kukan Kaka. Turaki ya juyar da idonsa kanta yana ta kallonta kamar yaune ya fara ganinta. kuka sosai Kaka take kamin tace,"ni da gawarta ne ma na gani hankalina zai fi kwanciya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
furucin nata na ƙarshe ya haɗe da rufewar idanun Turaki yana dukan ƙirjinsa, for few seconds yana jin kukan Kaka acikin kansa da kuma hasashen halin da take ciki.
ya buɗe idon ya sauke a ƙasa murya a sarƙe yace,"ki daina faɗar gawa Kaka, ganin gawarta ba yanzu ba insha'Allah, za'a ganta very soon aci gaba da adu'a Allah ya bayyanata". yanda yake yin maganar sai yaji kamar me koyon magana dan bai ma san ta yanda ya haɗa kalmomin ba ya faɗa.
Yami tace,"Allah ya amin