ole ya haƙura ya maida hankalinsa kan aikin da Baffa yasa su, sai dai zuciyarsa ta kasa natsuwa, rabin tunaninsa na kan Fillo, so yake yaji ko da muryarta ne, amma babu hali, tunda har Zaytuna yasa ta tambayi Yami ko suna gaisawa da su kaka ta waya, Zaytuna tace masa Yamin tace itama wallahi duk ta rasa ta inda zata same su.
kuma randa Fillo ta cika kwana 21 cif, ranar kidnappers ɗin suka kira wayar Yami suka shaida musu suna buƙatar naira miliyan 5 cas,idan kuma babu to su yanka musu ƴarsu su turo musu da namanta a kwali, suka kuma bada gargaɗin cewa in har suka sanar da wani batun hakan to ko da sun kawo kuɗi lallai sai sun yake ƙafafun yarinyar, aka kuma saka musu muryar Fillo dake ta kuka tana roƙon Kaka akan azo aceceta zata mutu.
wannan batun yasa Kaka da Yami suka yi ɗiff ko Maijidda basu bari ta sani balle su Hajiya Madina da sun tsab zasu iya sanar da police.
Kaka ta kira Amir a waya yazo, ita da Yami suka bincike ɗaki tsab suka kwaso takardun filayen Fillo da Abdulhamid, filaye guda huɗu da kuma takardar wata gona, ta bawa Amor tace dan girman Allah yay shiru aje a siyar duka ayau azo aje akai kuɗin nan.
cikin sa'a kuwa Amir na zuwa gaba ɗaya abinda aka saya filayen da gonar miliyan ɗari huɗu da hamsin. dan haka ko da ya kawowa Kaka kuɗin sai aka ƙara ɗauka shanu guda uku akaje aka siyar har kuɗin yayi making yanda aka nema.
kuma Amir shi ya ɗau kuɗin yaje ya kai inda Kidnappers ɗin suka buƙata, bai dawo gida ba sai wajen biyu na dare cike da tsoron dajin da yaje ya ajiye kuɗin, har ya kasa bacci saboda firgici.
su Kaka kuwa ana can anata zabga adu'a, Kidnappers ɗin sunce da an kai kuɗin zasu saketa ta dawo gida a lokacin, amma har sallar asuba har wayewar gari babu ko da inuwar Fillo.
hakan ya ƙara ɗaga hankalin su Kaka, suka kasa tsaye suka zaune ita da Yami, sai zagayen ɗaki suke yi, ana hakan wayar Yami dake ƙugu a soke tayi ƙara, da sauri jiki na rawa ta ɗauko ta kara a kunne, abinda ya doki kunnenta a lokacin shine Kukan Fillo.
tace,"Fillo kina ina?".
tace,"Yami sunce ba zasu sake ni ba, wai kuɗin yayi musu kaɗan sai an ƙaro. Yami karku ƙara musu ko biyar, ni na saddaƙar mutuwa zanyi, ki faɗawa Amir kar ya ƙara zuwa dan sun ce zasu karɓi kuɗin kuma su kashe shi, He has done so much for me that I can not repay him, bana son rasa shi Yami, kar ya ƙara zuwa dan Allah, gwara ya rayu ni na mutu, Yami ki kula min da Kaka bata da kowa sai ni sai Allah". ta faɗa tana kuka sosai, kuma me taɓa zuciya.
ƙit kamin Yami tace wani abu an kashe wayar.
Amir yazo gidan jikinsa duk a sanyaye don tuni Kaka ta kira ta shaida masa, ko da ya shigo ɗakin zubewa yayi daga bakin ƙofa, har tsawon minti biyar ya kasa cewa komai, sai da ƙyar ya iya buɗe bakinsa yace,"Kaka ko dai mu sanarwa da su Hajiya?, tunda sunce a a shirye suke suyi duk abinda ya kamata".
Kaka tai saurin girgiza kanta tace,"a'a Amir, ana faɗa musu zasu kai lamarin ga hukuma, su kuma mutane nan kaji abinda suka ce muddin hukuma ta sani sai sun kasheta".
Amir ya haɗiye wani abu a maƙogoronsa da ƙyar sannan yace,"shikenan Kaka, zanje yanzu akwai wani filina acan ƙauyenmu zan siyar da shi, shima kuma gidan da zamu zauna zan siyar da shi. gaba ɗaya in Allah ya yarda za'a iya samun ko miliyan biyu ce, sai a haɗa a ƙara basu". daga yanayin yanda yake maganar in ka kalle shi sai kayi masa kuka, bakinsa duk ya bushe, gaba ɗayansa ya wani firgice ya zaftare saboda rama.
Yami da Kaka suka haɗa baki wajen ce masa,"a'a karka sayar da komai Amir".
ya miƙe kamar zai faɗi yace,"Kaka bamu da wata mafita da ta wuce wannan. gobe zan dawo in Allah ya yarda, kuma a gobe zasu saki Fillo da izinin Allah, fatana ku kwantar da hankalinku kuyi ta adua".
Kaka tace,"to Amir a haɗa da sauran shanun can guda 5 da suka yi saura, akwai awaki ma guda 10 duk ka siyar sai a haɗa".
da kansa kawai ya iya amsa mata sannan ya fice jiki duk a saɓule, yana tafe yana layi kamar wanda yasha ƙwaya, bacci ne fal a idonsa da wata azababbiyar yunwa da yake ji, amma baya jin cikin biyun ɗa zai iya samuwa, shi da cin abinci da bacci kuma sai Fillo ta dawo.
kuma a safiyar ranar ne Turaki ya kira Khalil yake tambayarsa ga me da jikin Maama. dan shi har yanzu bai yarda da lafiyar da take ta faɗa dan bai ji a voice ɗinta ba, kuma taƙi yarda suyi vedio call.
Khalil mutum ne shi da baida wani ɓoye-ɓoye, ko saƙon mutuwa ne kai tsaye yake sanar da shi, dan haka kai tsaye Khalil yace masa,"Hammah ai yau kusan 3weeks kenan ana cikin tashin hankali, zancen da nake maka yanzu haka Maama bata cikin hayyacinta, ta fita ita da ƴar aikin nan Fillo an sace ƴar, har yanzu shiru babu labarin yarinyar, shisa ka kasa jin Maama a yanda kake so".
Turaki ya ɗauke wuta, ya daskare daga zaunen da yake, wayar ta silale daga hannunsa ta faɗo ƙasa, maganar Khalil ta shiga tariya acikin kansa. yarinyar ta ɓata, an saceta, 3weeks ba'a ganta ba, babu labarinta, ba'a san ina take ba.
hannunsa ya dunƙule ya